Hibbah ce take waya da Ummi tace "yanzu saboda selfishness irin nasu yasa suka turata saboda 'yar tasu bata kai Dua dinba" ummi tace "Hmm kedai bari kawai I try my possible best naga anfasa amma nunawa suke ai 'yar suce" hibbah tace "suna shiga hakkinta wollah" tace "gashi ni duk damuwata kartayi missing zuwa musabaqa dinta gakuma scholarship" hibbah tace "zasu sa taga kamar karatunta is of no used tunda batada supporter" tace "I'm telling you" hibbah tace "yanzu hajiya Abidah bazaki hakura idan na'iso saiku tafi ba?" Tace "hibbah ba haka bane but anyway I will wait!" Tace "toh sai munzo din?" Tace "safe flight" sannan sukayi sallama.
Dua nashiga daki bacci ne mai nawi ya dauke ta ga stress, ga rashin bacci da batayi ba, ga kuma uwa uba kukan da taringayi duk su suka sa mata zazzabi, akan dadduman da tayi sallan la'asar bacci ya dauke ta, hajiya hira suke tayi da Amrah da magrib yayi suka tashi sukayi sallah tare sannan suka wuce dinning domin yin dinner Alhaji ma yazo ya same su suka fara cin abincin tare dan Jim kadan yayi gyaran murya sannan yace "Ina yarinyar nan take ita bazaci abincin bane?" Hajiya tace "kasan kanta na ciwo so Dua takai mata ai tun dazu" yace "yauwa ko kufa" suka gama cin abincin su Alhaji yayi part dinsa, har time din Dua baccin zazzabi takeyi Hajiya tace "Amrah nikam ina yarinyar ne?" Tace "granny ai har yanzun ma bacci takeyi bata tashi ba" hajiya tace "Lalle ma toh ai ba hutu aka turota tayi ba, mikomin kofin ruwannan kigani" Amrah ta mika mata sannan suka wuce dakin da Dua take suna zuwa ta banka kofar da karfi sannan tashiga without any second thought ta kwarawa Dua ruwan Dua ta farka a firgice sannan ta zauna sakamakon ruwan da yashiga har hanci tane yasa tari ya sarketa kamar zata fito da kayan cikinta granny tace "You're not here for break da zaki wani samu daman kwanciya kina bacci maza tashi ki wuce waje kije kiyi wanke wanken nan sannan kishiga ki gyara kitchen kinsan uwarki ma a kaskance a gidan marayu aka dauko ta kuma dole tayi biyayya balle ke, zaki wuce ne kosai na Kara miki?"
Dakyar tarin Dua ya tsaya ciwon kanta maimakon ya ragu sai abunda ya karu ita har mamakin kanta ma takeyi datayi bacci me nauyi bata tashi tayi sallah ba dan ita komin baccin da takeyi lokacin sallah nayi ajikinta zai bata sannan zata farka, ta dafe kanta da taji yana neman tsagewa takama hanyar backyard tafita hawaye nabin kuncinta tarasa me tayiwa mutanan nan da suka extreme hate her, lantana da take ta observing dinsu amma bata da say ta karaso gunta sannan ta riketa ta zaunar da ita tafara bata hakuri kasa kasa take mata maga bata kaunar hajiya taji balle tace a bakin aikinta tace "amma kinyi sallah?" Dua tace "no I just wakeup" suna jin muryan hajiya na dososu da sauri Dua ta mike tayi wajan wanke wanken lantana kuma ta gudu ta buya hajiya ta bude kofar tace "kee!" Ta wurga mata goran morning fresh sannan tace "in kinso kiyi da sauri ki gama in kinso kuma kiyi tayi da sebin jiki har asuba tamiki kina wajan dan wannan ke yashafa sannan tayi wucewar ta".
Lantana ta fito tazo tasa Dua tace "barinje in mata sallama sai muga ko yanzu zata shiga dakin ta nan lantana taje tahada mata tea dinta na dare sannan tashiga parlourn tace ""Barka da warhaka hajiya" tace "yauwa" tace "naga kamar yanzu da wuri kike shiga ciki shiyasa nace barin hado miki tea din tunda yanzu sanyin ya sauko Nima ina son komawa daki" tace "kamar kinsani toh ajemin akan mirror yanzu zan shigo" tashiga ta ajiye mata sannan ta fito tace da hajiya "Kodai na kawo miki ne karyayi sanyi"tace "A'a fa barshi ma ganinan zuwa ma" sukayi sallama sannan tafita tasamu Dua tace yanzu tashiga ciki so tashi kiyi Alwala ga dakina sai kishiga kiyi sallah" tace "toh nagode Anty" Dua ta hada harda isha'i tayi tunda already time din yashige kafin ta fito har lantana ta gama tace "thank you Anty" tace bakomai jekiyi arranging dinsu a kitchen kar inshiga hajiya ta kamani" tace "hakanma ai nagode" tace Allah sauwake" tace "Amin" ta kwashe kayan tabi ta cikin gidan.
Sai dare irfan ya'iso gidan time din har hajiya ta shige ta kwanta Alhaji ya kira ta sai kukuni takeyi da masifa kasa kasa tafito parlourn ta hade rai ta zauna akan kujera kafa daya akan daya tana girgizawa Alhaji yace "toh irfan ni zanshige ciki idan kaci abincin sai ka wuce dakin dakake sauka" yace "toh Alhaji nagode" sannan ya juyo ya gaishe da hajiya ko amsa masa batayi ba yace "hajiya dama wannan tsaraban kine" ya fada yana mika mata tajuyo ta kalla tilin kayan da yace natane ta amsa tana mai godiya aranshi yana Mamakin son abun duniya irin na hajiya yanzu yanzu harta chanza masa yace "bakomai hajiya sai da safe" tace "tsaya mana" ta kwalawa Amrah kira zo ki daukowa yayanki lemu da snacks ki hada da abinci ki aje masa a dinning tace "toh" tunda tafito yake ta kallonta yasan face din but where har tazo gabansa ta saya tace "everything is ready there" tayi wucewar ta.
Ya tashi ya wuce dinning din yana Mamakin rashin kunyar yarinyar ko gaisuwa bata iya bane yaji karan an bude kofar backyard anshigo sannan yaji footsteps ta corridor ana doso dinning din kawai yafarajin bukun zuciyan shi yana karuwa trying so had to control but yakasa yatashi zai bar gun kawae tashigo har zata wuce taga da alaman mutun batama tsaya kallon fuskan wanda ke gunba kawai tadan rusuna da kayan hannunta tace "ina wuni" yakasa cewa komai sai kallonta da yakeyi ita kuma ta wuce kitchen din tafaran arranging plates din, after some seconds kamar wadda aka sikara kawai yayi kitchen din ji kawae tayi yace "who washed all those plate?" Tadan juyo ta kallesa sannan ta dauke kanta tace "nice" yace "baga sink ba a cikin kitchen din so why are you suffering your self doing outside + weather in zazzabi ya kamaki fa" tace "acan hajiya tace ayi".
Har ya koma daki tunani kawai yakeyi waya kawosu kaduna dama sunsan Baba Alhaji ne ko kuma side din hajiya ne, meyasa aka tara mata wannan tulin wanke wanken ita kadai while gidan da akwae masu aiki plus sistern ta why not suyi tare but if he could remember that day Amrah ba sonta take yiba are they not sister kawai ya kwanta da niyar samun amsoshin shi gobe da safe,
Dua nashiga daki time din Amrah na waya tace da wanda take wayan "excuse me" ta kase kiran sannan ta kwashe da dariya tace "kina tunanin kinzo hutu ko?, toh you're wrong, sai ayi maza a kwanta a kasan tiles dan yau ba gado sannan ta cigaba da dariyar muguntan ta, har tagama cewa komai Dua bata ce mata uffan ba tadau wani zani da towel din wankanta ta shinfuda ta kwanta sannan ta rufu da hijab dinta kawai maganar ammin ta 8years back taji a kunanta "ohh my darling bana hanaki kwanciya a tiles ba bakisan sanyi zai kamaki ba oya tashi" tace "O'o so nake ki dagani sai inga karfinki" "funny baby as usual barin goyaki toh" tashare hawan idonta tace "Ammi I missed you , Allah jikanki" kuka take tayi tana bitar rayuwarta da gakuma wahal halun da takesha gakuma wadda nan gaba batasan wanne zata hadu dasu ba.Su Ayesha yaune ta kama zasu tafi German dukkansu sun hallara a school harda iyayen su Ayesha tacewa haidar "Allah sarki da yau harda Dua ko yanzu wani hali take ciki oho?" Yace "I always think so shiyasa nake Kara tsanar that doll girl Amrah" suna cikin magana kuwa sai gashi ana sanarwa su shiga mota za'a wuce dasu airport daganan kuma duk suka shiga jirgi aka sanar kowa yasa seatbelt sannan jirki yatashii Ayesha tace "I would miss you Dua"
vote pls
Share pls
Comment pls
JazakAllah khayr❤