KAI NE JARUMI PAGE 4

31 3 2
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼


WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH





*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*



  Page 4:


Da sauri ta girgiza Kan ta, tare da tashi ta zauna da kyau a fili ta ke fad'in,

" kaiii inaa da kunya na je ina cewa  Mama ta nema min magani na haihu, kaii ba zan iya ba ma, to ya zata kalle ni ma? Ai se ta ce bani da kunya ma"

Tana nan zune har qarfe hudu na rana ta buga ga kiraye kirayen sallar la'asar nan dik ya karad'e ko Ina, gani ta yi zaman ba zai yi mata maganin komai ba ga lokacin sallah ya yi kawai  se ta fad'a bathroom ta dauro alwala  ta fito ta zira doguwar riga da hijabi ta tada sallah, ta dade tana addu'ar neman gafarar Allah, da yiwa mijin ta da iyayen ta addu'a sannan taiwa dikkan musulmi addu'a kafin ta yi wa kan ta ta neman haihuwa me albarka ta dad'e sosai cikin sujjadar ta ta na maimaita addu'ar ta, sannan ta d'ago tai tahiya ta yi sallama, tana idarwa ta faɗa kitchen ta haɗa masu abinci dan qarfe shida Adnan ke dawowa, tana girki tana qara gyara gidan, ta je toilet din shi ta qara wankewa, ta fidda masa kayan da zai saka in ya dawo, sannan ta fito,bayan ta kammala girkin ne da gyare gyaren ta koma d'akin ta ta cire kayan ta ta d'aura towel ta shige bathroom dan yin wanka, had'a ruwan wankan ta yi cikin kwamin wanka ta zuba dik wasu abubuwa da take amfani da su wajen wanka, ta d'aga qafarta kenan zata shiga ta ji motsi alamar Adnan ya dawo kenan,Murmushi ta yi na farin cikin dawowar mijin nata ta qarasa shiga, kafin ta zauna ya bud'e qofar ya shiga, da sauri ta zauna ta na dariya, dan Sakeenah mace ce Mai kunya,har yanzu bata Iya bari Adnan ya gan ta ba kaya, se dai ta na saka qananan kayan da za a ce da su da babu dik d'aya ne, to ta fi son haka akan ta zauna ya gan ta ba komai a jikin ta, Murmushi ya yi Shima ya qarasa shiga bathroom din ya hau cire riga, se ni Kuma Hamidatuwa na jaaawo musu gambu na koma Ina jiran su a parlour.

Ina zaune na ji dariyar su tare da maganar Sakeenah ta na fad'in,

" Zaka fara ko? ko wanne kyau na yi a hakan, bayan ka dawo da wuri, ni da na so se na tsara kwalliya irin ta 'yan gayu se ka dawo"

"Tabb ashe kin shirya sumar da bawan Allah marayan Allah se Kuma Allah ya dube ni ya dawo da ni akan Kari, Sakeenah ni Adnan zan iya rantsuwa da Allah ban tab'a ganin macen da ta min kyau Kuma take min kyau a kowanne yanayi take ba sama da ke, ko kin yi wanka, ko baki wanka ba ke Mai kyau ce, ki dinga godewa Allah domin kuwa se a tara mata dubu kafin a samu irin ki goma"

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now