💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 25:
Duka ya sake kai mata ta goce, Atiyyaerh ce ya yi sauri ta shiga tsakiyar su, ta kwab'e baki kamar na me Shirin yin kuka, dan kuwa ji take kamar ta Saka kukan Sam bata ji dad'in abinda ya faru ba a tsakanin su,se take ganin kamar za a ga laifin ta, tinda sa'insa bata tab'a had'a su ba balle ya ce zai Kai wa matar Yayan nashi duka irin haka.
"Dan Allah Bappan Umar ka yi hakuri ka rabu da ita, matar Yayah ce fa? In ka dake ta kamar ka d'au hannu ka daki Yaya ne fa, na san ba zaka iya dukan Yayah ba ai ko? To ka rabu da ita ta min qazafi ita da Allah,Allah baya zaluntar bayin shi sai dai su su zalunci Kan su"
Kallo ya bita da shi Yana masifar son salon da take magana da shi a yanzun, ba qaramin burge shi ta yi ba, sai kace irin qananan yarannan masu shegen kyau haka ta koma,tsaki ya ja mai qarfi zai wuce sashen su dan in ya ci gaba da zama a wajen ba zai kyale ta ba,ya na juyawa ze fita ya ga Yayan shi a tsaye da Baba Garba, dafa kafad'ar shi Yayah ya yi yace masa su je ciki ya na son magana da shi,cikin rausaya kai na irin fushi fa nake dinnan ya bisu, Yaya kuwa kallon matar shi ya yi da Atiyyaerh yace su biyo shi, wani d'aki suka shiga, ba komai sai tabarmi, da ledar tsakar d'aki, sai littattafai, na Baba Garba , bayan sun zauna ne, Atiyyaerh ta miqe ta deb'o masu ruwa, suka sha suka yi mata godiya, sannan Baba Garba ya yi gyaran murya, ya yi sallama suka amsa,ya ci gaba da magana kamar haka,
"Zancen gaskiya ban ji dad'in yanda mun fita dan mu je nemo maku abinci amma mu dawo mu taddaku kuna fad'a ba, har da kai namiji a fad'an, kenan zaman ka a gidan bai da wani amfani in dai mata zasu na fad'a ka shiga? Ina son sanin abinda ya faru daga bakin ki Atiyyaerh kuma bana son ki boye laifin kowa, ki fad'an gaskiyar me ya faru,"
Sallama ta yi itama kamar yanda ta ga Baba Garba ya yi Kan ya fara magana,se suka amsa mata sallamar, sannan ta labartawa Baban komai, bata rage ba bata qara ba, wani kallo mijin Hajar ya bita da shi, Wanda yasa ta sunkuyar da kai,
"Wato ke lab'e kike masu kenan, tinda da alama a maganganun da Atiyyaerh ta fad'a ya nuna ba yau din ne kawai kk lab'e masu ba tin da aka kawo ta kk masu labe'n, " In ji Baba Garba da ya kafe ta da Ido ya na jiran jin me zata ce.
Cikin jin kunya Atiyyaerh ta dan matsa gefe ta takure, lura da hakan ne yasa Baba gaggauta maganar da yake son yi,
"Da ga yau zuwa har a bada bana son na sake ganin fad'a a gidannan, bana son a sake taruwa anan, ran kowa sai ya b'aci, matan su tashi su je a ci gaba da aiki, kuma bana son gaba ko qananun magana, ina fatan kun gane, ke kuma Hajar bata hakuri,"
kallon Atiyyaerh ta yi cike da tabbb wannan zan ba hakuri dinnan, amma mijin ta na daka mata tsawa se ta ba Atiyyaerhn hakuri, Atiyyaerh kuwa sanar da ita ta yi cewar ba komai Allah ya kyauta na gaba komai ya wuce,kowa ya amsa da ameen suka miqe suka fita, bayan fitar su ne Baba ya ma yaran shi nasiha, akan kar su kuskura mata su had'a su, su b'ata masu zumunci, komai zai faru kuma suna zurfafa tunanin su da binciken su kafin yanke hukunci, godiya suka yi sannan Yayah ya bama qanin shi hakuri for his wife behavior, nuna masa ya yi ai ba komai ya wuce, sannan suka fita.
Hajar ta rasa yanda zata yi dan ta dasawa mijin ta tsanar matar qanin nashi, dan haushin Atiyyaerh take ji matuqa,kowa na son ta a gidan, dan ita tin kan auren Ahmad ba son ta ake ba a gidan, balle yanzu an samu surukar so, tasan ita kam tata ta qare, duk wata hanya a 'yan kwanakin nan tabi amma shiru, dabara ce ta fad'o mata, tabbas tasan yaran ta basu da kunya da su zata yi amfani,dan in akwai abinda Muhammad ya tsana bai wuce wani ya tab'a masa yara ba......
*******************************
Afrah ce ke zaune a Parlour ta na kallo, Rasheedah ta fito ta ci uwar kwalliya,tinda ta aurar da Ablaerh hankalin ta ya kwanta, dan a zuciyar ta tana raya tana can tana fama da d'an wiwi, wataqilama ta sha duka yafi a qirga, ga faccala ga suruka, wahala goma da ashirin, murmushi ta yi da tai wannan mummunan tunanin, ta zauna a kujerar dake kallon ta Afrah da take daure fuska a duk sanda ta ga Mahaifiyar ta ta, dan tayi2 ta bar ta taje taga 'yar uwar ta amma ta hana ta, haushin hakan take sosai, ,
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....