💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Makaranta ku yi hakuri ku jira ku ji ya abun zai kasance har zuwa qarshe,sannan kar mu na manta cewar kowa fa da qaddarar shi a rayuwa, ba lallai ne a halicce ka ka ji daɗi all ur life ba, we ar not in this dunya to have fun, we ar here to worship Allah, kuma a cikin bautar shi ne ya ke jarabtar mu da abubuwa kala2, in ma ya jarabce mu da arziqi, ko talauci, ko ya haɗa mana dika, gaka mai arziqi amma ma talauci, ko gaka talaka amma mai arziqi, (mai wadatar zuci talaka,da mai kudi mara godiya) dan haka nake cewa ku qara hakuri, akan kome zaku karanta har mu Kai qarshen labari thank you.*
Page 24:
Ahmad a kwanakin nan ji yake duk duniya ba wanda ya fishi morewa da matar aure, ta bangaren Atiyyaerh kuwa ta sani bata yi irin auren da take so ba, Kuma har yanzu bata son Ahmad a ranta, amma ta na Jin dad'in yanda yake kula da ita, yake nuna mata soyayya, ta bangaren surukan ta ma bata da matsala da su, Inna Abu da Baba Garba basu da wata matsala, su suke ci da su ita da Ahmad d'in, dan haka ta kan fita ta ya Innar aiki bayan ta gama da na bangaren ta,Ahmad yana da Yayah da matar shi, wadda take da qananan yara biyu,Sadiq da Umar,yaran ba qaramayen marasa kunyan yara bane, yanda uwar su take ba kunya komai a tsattsaye haka suma yaran suke, Yayan Ahmad Muhammad sunan shi kowa na ce masa Yayah, bai da matsala, amma wani lokacin akan yaran shi sai a buga da shi a tsakar gida, nan ma yana samun pampo ne wajen matar shi,me suna Hajar, Hajar ko sunan surukar ta katsal take fadan shi ba sakayawa wato Abu, shiyasa yaran suma suka dauka, Abuu, Baba Garba ne kawai suke ce wa Baba, su abincin su daban suke yin shi a gidan, in ta ga dama ta zuba ta bawa surukan in bata yi niyya ba suci da yaran ta da mijin ta.
Atiyyaerh ta kasa ce ma surukar ta Abu, sai take ce mata Inna kamar yanda taji Ahmad da muhammad na kiran ta, ta kula da yanda surukan ta ke son ta, har Yayah, sannan kuma ta kula da yanda Hajar ta tsane ta, sai tana yada mata magana akan kyaun ta ai na d'an maciji ne a Jira lokaci kad'an mummunan halin Atiyyaerhn zai bayyana ne nan gaba, amma ba ta taba tanka ta, to yaushe ma tazo gidan? Kuma ma in ta dad'e me zai kaita biye mata? Ita fa a rayuwa bata son hayaniyar fad'a, rayuwar bala'i da masifa a ciki ta taso, to me zai dame ta kuma? Dan haka ganin halayen Hajar take nafila akan inda ta baro ba Wani damuwa bane a wajen ta.
Ta gama wanka kenan ta yi kwalliya daidai ita abin ta, dan rashin sabon da ta yi ne ma da Kwalliyar yasa wataran sai ta yi wanka sai ta manta bata yi Kwalliya ba se ta tina yanzu fa a gidan miji take sai ta dan yi kwalliyar kadan, to ranar Kuma an yi sa'a Ahmad a gida yace zai wuni, ita kuma kullum tana nuna masa fita neman na kai ya na dojewa dan be Saba ba, sai ya ce mata shi fa ba sana'ar da bai gwada ba basa kar bar shi ne, haka take hakura, ta biye mai ya yi ta jagwalgwala ta, bata so amma bata tab'a nuna masa ba,kuma bata taba kyamartar shi ba, dan daidai misali bai da qazanta yanzu, tana sashi gyara a inda taga bai mata ba, da dabara da Jan hankali zata nuna masa me take so ya gyara, misali wata rana suna zaune yana ta bata labarin yan ganyen abokan shi, ,
" kinga kafin na aure ki ,nida Baba Qarami sai mu sha ganye nadi shida a rana, ba abinda ya mana zafi, amma kinga nine yanzu har na d'au sati biyu ban sha koda sigari ba, sai sau d'aya,randa kk shiga yiwa Inna tuwo na sha da kk dawo na buga qasa nace ban sha ba🤣 , kika yi kika yi na kafe na ce miki ban sha ba, kin san me?"
Kada masa kai ta yi tana dariyar tina kafiyar da ya mata yana zaro ido kamar mage ta sha wanka,
"A ranar sai na ji wani haushin kaina dan me zan sha abinda ba ki so, bayan ke tinda na aure ki ba ki da burin da ya wuce na ki faranta min? Shiyasa na yi ta qoqari na daina, dana ji ina son shan Wani abun maye gwanda na zauna a gida na yi ta Koda kallon ki ne Ina Jin nishad'in da bana Jin irin shi a cikin kayan Mayen, shine zakiga na dame ki na maqale maki, ke kuma nasan kin gaji amma a haka ki ke hakuri dani,na gode Atiyyaerh 'yar aljannah ki ta taya ni da addu'a kin ji? Watarana inshaa Allahu zan dena ne"
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....