💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 22:
komawar Yousuf makaranta da kwana biyu kenan, su Atiyyaerh na zaune a Parlour su uku, Rasheedah, Atiyyaerh, da Afrah, yaran na ta hirar makaranta da Kuma qawayen su, Rasheedah na zaune ta na danna waya ta na kallon su lokaci zuwa lokaci, a dik sanda zata had'a Ido da Atiyyaerh sai ta zabga mata harara, ita kuwa ta d'auke Kan ta ta ci gaba da hirar ta, in ana sabawa da mugun abu to Atiyyaerh ta saba da na Rasheedah,buga gate da akai ne yasa su dika ukun da suka saurara da hirar da suke suka nutsu dan su ji waye, kallon Atiyyaerh Rasheeda ta yi, in an buga gida irin haka mazan basa nan dama ita take zuwa duba waye, miqewa ta yi ta dauki hijab din ta ta saka tai waje, tana budewa ta yi arba da qatuwar motar Hassan a waje, cike da murmushi yake kallon ta,
"Ashe lallai bugun zuciyata bai kasala ba wajen sanar dake zuwana,"
kad'a ido ta yi sama sannan ta isa gare shi, bayan ta yi masa sallama ta gaida shi tace,
"A gaskiya ni ban da abin fada maka kuma daya rage wa bakina Hassan, soyayya tsakanin mu ba mai yuwa bace, ka taimaka ka rabu dani, wai wa ma ya fada maka nan ne gidan mu?"
"Atiyyaerh ba zan iya rabuwa dake ba gaskiya,ina son ki sosai, duk da ni d'in ina fuskantar qalubale a gidan mu wajen neman auren ki da nake son shigowa, amma hakan ba zai hana ni na gwada sa'a ta ba,kuma dangane da tambayar ki na waya nuna min gidan ku, na biyo ki shekaran jiya da kuka raka yayan ku,"
Ajiyar zuciya Atiyyaerh ta sauke sannan ta bud'e baki za ta yi magana suka ji budewar gate da qarfi , tana juyawa ta yi Ido hud'u da Umman su, nan da nan ta rab'e gefe da niyyar ta shige gida, cikin fushi Rasheedah ta janyo ta baya,sannan ta ce,
"Ki jira na fad'i duk abinda nake so na fad'a a gaban ki Kan ki tafi, malam kalle ni nan, ni ce uwar ta, ba zamu baka auren ta ba, domin mun mata miji tin tini, in ma baka sani ba ka sani, kalli can, ka ga wancan gidan na kusa da mu?....."
Ta yi nuni da hanyar gidan su Ahmad ta ci gaba da magana,
"To a can gidan yaron yake,sunan shi Ahmad,tun Suna Yara suke soyayya kuma an yi magana gemu da gemu, iyayen shi sun kawo komai na aure,dama ana Jira ta kammala secondary school ne, Kuma alhamdulillah,da alama daga gidan mutunci ka fito dan haka kasan dai ba kyau neman aure akan aure ko? To ka tafi in da rabo sai kaga Allah ya kawo maka wata ta gari,"
Cikin tsananin daci da qunar rai Hassan ya kalli gidan su Ahmad, a ranshi yana jin haushin tsayawa Sanya da Wani bibiyar ta da ya dinga yi ba tare da ya d'au matakin neman auren ta ba,yau gashi wancan talakan ya riga shi, ko sallama bai masu ba yaja motar shi ya tafi, duk da ba son shi Atiyyaerh ke yi ba abun ba qaramin sosa zuciyar ta ya yi ba, ya za a ce wai yayar Mummyn ta ce zata mata wannan aikin, cikin kuka ta shige gida, tana zuwa zata shige daki ta ji Umman nasu ta daka mata tsawa da cewar,
"To uwar son maza, uwar jaye jaye, ke kenan baki da aiki sai jaye jayen maza ga Afrah nan ta kame Kan ta har yau ba Wanda ya biyo ta sai ke kin ballagazar da kan ki maza na faman binki dik inda ki ka shiga,yanzu gashi daga je ki duba waye shine kk tsaya sakin zance ko, to ki kwantar da hankalin ki in namiji ne sai kin gaji da shi, yanzu2 zan leqa gidan su Ahmad na yi ma Babar shi magana in da gaske suke to fito,"
Cike da tashin hankali Atiyyaerh ta kwasa da gudu ta tsugunna a gaban Rasheeda ta kama qafar ta cikin gunjin kuka ta ce,
" Ummana dan Allah ki yi hakuri, kar ki gurbatan rayuwa ta, zan shiga halin qunci fiye da kullum in aka ce Ahmad ne mijina, Umma ni na yarda ku barni na zauna ba aure har abada akan a hada ni aure da wancan jahilin ko islamiyya fa bai zuwa,"
"Iyyyeee lallai ne bari ki gani na ga alamar kin zaci wasa nake ko?"
Sama ta nufa a guje ta Sako hijab d'in ta, zata fita, Afrah da Atiyyaerh suna kuka suka riqe ta Suna bata hakuri, juyo wa ta yi ta hau kai masu duka dukkanin su a haukace, Afrah ta yi baya amma Atiyyaerh sam ta qi matsawa, kuka kawai take ta rasa me ke mata dad'i, fizgewa Rasheedah ta yi daga riqon da tai mata ta yi gaba, da sallama ta shiga gidan ba b'ata lokaci ta shige d'akin mahaifiyar Ahmad d'in, ta na zama aka gaisa sama sama sannan ta sanar dasu cikin nan da sati biyu su yi komai na Shirin auren Ahmad da Atiyyaerh su turo ai auren in suna so in basu so zata ba wa wani Atiyyaerh, cike da murna su ka yi godiya ta kamo hanya ta koma gida abunta kamar ta je bada auren 'yar tsana.
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....