KAI NE JARUMI PAGE 23

21 2 1
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼



WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH




Page 23:




Hannu ta sa ta damqi damtsen Atiyyaerh ta janye ta daga jikin Yousuf ta kwad'a mata mari, cikin qanqance Ido da d'aga murya ta ce,

"Ai dama na San za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, tinda na ga gilmawar ka kayo nan jikina ya ban akwai Wani abu, a gidan nawa zaki nuna min karuwanci? To ki kwantar da hankalin ki kwana nawa neèe ?daga gobe ne fa za a yi bikin naku, jibi an daura aure an kai ki gidan mijin, kin je can ki ci uwar da zakici a can amma ba a nan ba,"

Ran Atiyyaerh da Yousuf ba qaramin b'aci ya yi ba, musamman kalmar karuwancin nan da ta ambata ta sosa zuqatan su, amma dake Atiyyaerh akwai hakuri, tin kallon farko da ta mata na b'acin rai bata sake ko da kallon ta ba,ta juya ta koma gado ta kwanta ta dora pillo a  kanta, sannan ta ja bargo ta rufa, Yousuf ne har yanzu ya ke tsaye ya kuma tsare Umman tashi da ido, yana son ya yi magana amma ya rasa mai zai furta da Allah ba zai fushi da shi ba, tabbas in zai magana ko ashar ya dura ba zai ji sauqin zuciyar shi ba, wannan matar me mummunan halin da be tab'a ji ko gani ba a rayuwar shi mahaifiyar shi ce, kalaman shi dole su zama masu taushi a gare ta in Yana son Rahamar Allah, a wannan gab'ar kuwa bai da kalamai masu wannan taushin, hadiye wani abu ya yi mai mugun d'aci ya sa kai zai fice,

"Ina zaka je kuma?"

"Makaranta zan koma,"

kafin ta furta wani abun ya fice, daidai zai bude qofa Abban su shima ya kama zai shigo, murmushi Abban ya masa amma ya kasa maida masa da martanin Murmushin, dan haushin Abban ma yake ji sosai ai ba kowacce wasiyya ake cikawa ba, wannan akwai cutarwa a cikin ta, ace shi bai isa da gidan shi ba,saboda kawai wasiyya sai kowa ya rufe ido, fadar Allah nawa sike takewa duk da ba zai iya nunawa ba, amma tabbas yasan suna aikata Wani abun mara kyau ko da a b'oye ne, sai wata wasiyya ce zata hana su kyautata wa marainiya, wannan ko uwar ta na da rai ba zata so hakan ba, komai son ta yi mending abubuwa tsakanin ta da Umman su, kafad'ar shi Abban ya dafa ya d'an matsa kad'an,ai kuwa kamar ya matso da kuka, kuka ne ya kwacewa Yousuf, wanda Abban nasu ya ji dad'in zuwan kukan, dan ya kula tin ba yau ba d'an nashi yake son Atiyyaerh, sai dai a wancan zuwan da ya yi ya tabbatar da zargin shi ,se kuma ga wannan mummunan had'in aure da ake son a Yi wa yarinyar, rungume shi ya yi sosai a jikin shi dan ya yi kukan shi ba me hana shi, sun fi minti 5 a tsaye, sannan ya kamo hannun shi suka qarasa shigowa, zaunar da shi ya yi a kujera kusa da Sulaiman da idon shi har yanzu yake kamar gauta, duk da yayi kukan amma har yanzu zuciyar shi na nan da takaicin wannan had'in auren, ji yake kamar yaje ya batar da Ahmad din, in ba a ga ango ba wa zai aure ta d'in? Afrah ce ta je ta debowa Abban nasu ruwa da abinci, zama ya yi yaci tukunna, yaran na mai kallon lallai Abba har abinci kk iya ci? Bayan ya gama ya yi hamdala sannan ya fara magana kamar haka,

" kuyi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri, shine kalmar da zan iya had'a ku da ita, ku sani uwa ta wuce wasa, kar kuce zaku yi fushi da mahaifiyar ku, tabbas uwa ba abar wasa bace, ku yi hakuri da hukuncin da ta yanke, ni kaina zan so hana wa, amma a wannan karon ina son, itama ta ga irin abun da Sakeenaa take son ta gani, na fahimci inda komai yake dosa yanzu haka, ku qara hakuri, zuciyata tafi taku b'aci, badan komai ba sai dan ganin nine mai gidannan, ina da ikon sawa kuma na hana, amma qiriqiri gidana yafi qarfi na, dan haka dole na bamu hakuri dika, Yousuf kai hakuri a daura aure sai ka koma,"

Yana kaiwa nan ya miqe da jakar shi ya wuce ciki, wata qara yousuf ya saki ya koma da baya ya kwantar da jikin shi akan kujerar, sunan Allah kawai ya fara ambato, dan yasan shine kawai mafitar shi a halin da yake ciki cikin iKon Allah kuwa sai ya ji ya fara samun sauqin zuciyar shi, umarni ya ba Afrah akan taje wajen Atiyyaerh, ita kuma bata son zuwa kunyar ta take, wannan zalinci har ina, me zata ce mata? Da wanne idon zata kalle ta to? Amma haka ta miqe ta shiga dakin, tana zuwa ko taga Atiyyaerh na rawar sanyi, tab'a tan da zata yi se ta ji jikin ta rauuuu, kamar wuta, sai karkarwa take, miqewa tai a kid'ime zata fita, ita kuma ta tattare duk qarfin ta da ya rage ta cafko ta,

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now