💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*Page 9:
Da asuba bayan sun idar da sallah sun gabatar da duk wasu ibadun da suke yi bayan kowacce sallahr farillah, baccin su suka koma mai cike da nishadi, Adnan ji yake kamar ya dawwama a jikin Sakeenaah ya zamana dik inda za shi ko me zai yi ta na tare da shi, Sakeenah wata ni'ima ce da Allah ya bashi a rayuwar shi, ita alkhairi ce a gare shi ta kowacce fuska,yarinya ce ita da ta San qima da darajar Kan ta da ta mutane, ga uwa uba nutsuwa da sanin ya kamata, mace ce mai ibada da tsoron Allah, lallai shi kam ya yi dace, Allah ya dubi maraicin shi ya had'a shi da macen da ta tattara komai da yake buqata,akan ce mace ta auri mijin marainiya in ta yi dacen miji, to shi Kam ya auri matar maraya za a ce, qara qanqame ta ya y, ya kai bakin shi bayan ta ya na sumbata, cikin baccin ta take jin hakan, juyowa ta yi gaba daya itama ta rungume shi suka ci gaba da baccin su.
Basu farka ba sai wajen tara na safe, miqewa ta yi ta fara ayyukan da ta dora wa Kan ta tinda ta na da masu aiki amma ta gwammace ta yi hidimar mijin ta da kan ta, abincin karyawa ta musu sannan ta dora girkin da zata Kai wa iyayen ta, ta matsu lokacin tafiya gidan ya yi ta yi kewar su sosai,( ba lallai bane Dan Zaki gidan ku ki yi masu girki ya na dai Daga cikin kyautatawa, Dan ba kowanne miji bane Zaki dauki abincin shi ki Kai gidan ku be sa Ido akai ba, amma in gidan iyayen shi Zaki Kai se ki ga be damu ba,kaiwa naku gidan se ya zame maki abin magana Dan haka in Zaki Kai abinci gidan ku ki tabbata ba zai zama da zubewar mutuncin iyayen ki ba) qarfe 1:15pm ta gama komai, Adnan kuwa ya na gama karyawa ya zauna a dan qaramin parlourn su da laptop d'in shi yana ayyukan shi tare da duba emails din shi, shiga goma fita goma sai ta bi ta gefen shi, ta dan masa wassanni, in ko ta wuce bata kula shi ba ze shagwabe mata fuska kamar qaramin yaron da maman shi ke aiki ta manta da shi, a haka ta gama ta hada masu ruwan wanka ta fiddo masu kaya, inda ta dakko masu wata shadda ruwan toka da ta sha aiki me kyau, daka ganta ka san an kashe kudi wajen siyan ta da dinkata, anko ya masu shi da ita, zuwa ta yi ta zauna ta ja laptop din gaban ta ta yi saving masa ayyukan shi sannan ta yi hibernating laptop din, ta juya gare shi ta na kallo shi cikin wani salo na musamman shi ɗin ma qura mata ido ya yikamar ranar ya fara ganin ta, d'an hade fuska ta yi sannan ta ce,
"To a tashi haka nan muje wanka ko"
Adnan na ganin haka ya sake shigewa cikin kujera,ya na matuqar son yanda take tarairayar shi kamar Wani qaramin yaro, a gaban ta ne kawai ya ke Iya sakin jikin shi ya yi Duk abinda yake so,hamma ya yi tare da miqa shi a dole ya gaji kamar Wanda ya yi aikin qarfi, Sakeenah na ganin haka ta girgiza Kan ta ta na Murmushi, yau Adnan shagwab'a yake ji,ita kuwa zata Yi pampering din shi kamar jinjiri, tashi ta yi ta tsaya a gaban shi, ta bashi hannun ta guda d'aya dan ya kama, Cike da kasala ya miqa mata hannun shi d'aya, yunqurawa ya yi kamar zai tashi ya ja ta ta fad'a jikin shi, dariya ya Sanya mata,
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....