💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 17:
"Ina plate din Atiyyaerh?"
"Bata tashi ba in ta tashi na had'a mata nata,"
Tinawa ya yi jiya yarinyar bata samu bacci da wuri ba, ya tabbata bacci ne mai nauyi ya d'auke ta yanzun, se kawai ya ce,
"Ok,"
kafin su gama Atiyyaeh ta farka, ta fito, tana murza ido, gashin ta duk ya hargitse, ya sauka a saman kafad'un ta, direct wajen Rasheedah ta nufa,da sauri Rasheedahn ta hankada ta baya, yarinyar ta bige cup din tea da yousuf ya d'aga zai Kai bakin shi,zafin tea d'in da ya zuba a hannun ta ne ya Sanya idanun ta cika da hawaye, kallon Rasheedah Atiyyaerh ta yi sannan ta fashe da kuka,
"Shiiiii ki rufen baki,mai shegen kukan tsiya, uban wa zaki zauna wa a cinya? Ko Afrah ga ta nan a zaune tana karyawa da kan ta,ko kuwa se ke 'yar gwal zan d'auka? To maza samu waje zauna nan na hada maki abinci, kuma ki min shiru ko ki daku yanzunnan"
Miqewa ta yi rai a b'ace taje ta hado mata shayi tsalalo ba Wani wadataccen Madara da millo balle sugar, sannan ta soyo kwai guda d'aya, ta kawo ta dangwara mata ta yanko bread ta dora a saman K'wan ta ce,
"Ga shi nan ki cinye dan in kk tsaya min shegen kukan nan naki zane maki jiki zan kina ji na ko,"
kyab'e baki Atiyyaerh ta yi kamar zata yi kuka tana ci gaba da kallon Rasheedahn, cikin wata iriyar murya mai tsananin nuna gajiyawa da halayyar Rasheedah Auwal ya ce,
" Rasheedah ki ji tsoron Allah, wannann yarinyar da ko kyakkyawar magana mai ma'ana ba zata iya maki ba sai ta had'a da shirme kasancewar ba ta da cikakken wayo, ita ki ka zauna ki na wa wannan abubuwan na zalunci, dubi abinda kk bamu dubi wanda kk bata,ita da gidan ubanta, kayan abincin ubanta, kaiii amma baki da imani Rasheedah Sam sam" ya na kaiwa nan ya ja kujerar da yake Kai ya miqe da niyyar barin wajen.
"To a min gori tinda Ina gidan uban ta, na ga dai gidan qanwata ne Kuma Ina da gadon qanwata dole na zauna na ci azziqi na bar azziqi a mazaunin shi,sannan ba ni na roqi uban nata da ya ban wajen zama da abincin da zan ci ba, haqqin ka ne ciyar dani me kyau da ban wajen zama mai kyau,sutura mai kyau da kulawa, amma ka gaza wasu mazan sun tara kaima ka zauna cin azziqi, dan haka daga yau kar a sake min gorin azziqi da ka tara da ban ci na wasu ba, Kuma na ga ai zaka iya bata naka in kana so ba Wanda ya hana ka ai, da ta tashi da wuri ai da haka bata faru ba,"
komawa mazaunin ta ta yi ta ci gaba da cin abincin ta, gaba d'aya abun da Rasheedah ke yi a Kan idon Yousuf Kuma ya na gane halin muguntar da take wa Atiyyaerh da rashin azziqin da take wa mahaifin su,yaron yana da wayo sosai, shekarar shi bakwai, tashi ya yi da dan guntun tea din shi a hannu ya je ya had'e waje d'aya dana Atiyyaerh sannan ya sake raba masu, nata yafi yawa sosai, sannann ya miqa mata k'wan shi, ya d'au guda d'ayan da aka soya mata, ya na juya shi sai ya ga a qone ma yake ta baya, kawai sai ya hau cire qonannen Yana zubawa a gefen plate d'in shi ya na cin Wanda be qone ba, hakan da yaron ya yi yayi bala'in burge Auwal,komawa saman dinning d'in ya yi ya d'auki nashi Shima ya yi mixing da na Atiyyaerh ya sake raba musu Sulaiman ma ya aikata irin abinda ya ga Yayan shi da Abban shi sun yi,Afrar ce ta tashi dugui dugui zata yi itama Rasheedah ta daka mata tsawa,
"Meye haka? Meye wannan zaku dinga wa mutane qazanta wai ku masu tausayi,hana ta abincin aka yi da za ku dinga wa mutane qazanta? Ko dake wannan ma ai tausayin munafurci ne, ba za ku burge ni ba sai na ga kun fasa cin abincin kun bata naku dika,"
Buga tsaki Rasheedah ta yi sannan ta miqe zata wuce d'aki, Atiyyaerh na zaune ta na Shan tea ta dafe hannun ta a qasa,Cike da masifa Rasheedah ta wuce ko ganin gaban ta bata yi ta kuwa take hannun marainiyar Allah da ke zaune a qasa,wata iriyar razananniyar qara ta saka ta d'auke hannun ta ta na yarfewa tare da Kiran Mommyn ta, Auwal ba qaramin qoqarin danne zuciyar shi ya yi ba na barin ta be mata dukan tsiya ba, d'aukar Atiyyaerh ya yi ya lallashe ta ta yi shiru, sannan ya bata abincin, tare duk sika hade k'wai da dankalin turawan a plate d'aya suka qarasa karyawa, bayan sun gama ne ya shirya ya fita, fitowa ta yi ta kama kan yaran ta ta masu wanka, Atiyyaerh na ganin haka ta hau murna, tsakanin ta da wanka akwai amana, kayan ta ta hau cirewa a d'akin su Wanda a da na Sakeenah ne a yanzu Rasheedah ta maida shi na yaran, d'akin Kuma da yake mallakin Atiyyaerh sai ta maida shi na Afrah, kamar yanda Atiyyaerh ta ke Jin su Yousuf na ce mata Umma itama haka ta fito daga d'akin ba kaya, a bakin qofar toilet suka had'u da Rasheedah wadda ta dakko Afrah a hannu kamar wata jinjira, da kallo Rasheedahn ta bi yarinyar ,ita kuwa se dariyar farin cikin za a mata wanka take, cikin muryar ta mai dad'i ta ce,
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....