KAI NE JARUMI PAGE 29

26 4 1
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼


     

WRITTEN    BY HAERMEEBRAERH




Page 29:







Parlour ta bude mishi ta mai izinin shiga sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama, kafin ta d'ebi zobo mai sanyi da meatpie da suka yi ita da Afrah ta kai mishi, sai da ta koma ciki ta d'an bashi waje sannan ta dawo, ya d'an ci kad'an dan shi damuwar shi bai wuce tazo su yi magana ba, ita kuma ta rasa ta yanda zata b'ullo masa, zaman ta keda wuya Yousuf ya yi sallama ya shiga, ganin baqo kuma ga Dimond d'in shi a zaune ta sha kwalliya ya sa ya yi kicin2n da rai, fuskar nan kamar bai tab'a dariya ba, hankalin ta in ya yi goma ya miqe tsaye, a daburce ta furta,

" Sasssannu.. da zuwa Yayah,"

ko kallon ta bai ba ya amsa, idon shi na kan Hassan, yana jiran qarin bayani, daga tsayen ya harde hannayen shi a qirji yana kallon su,

"Ammm dama wannan shine Hassan.."

Se kuma tai shiru, Yusouf yace ,

" Ehemmm? Sai yazo yin me?"

Hassan ne ya miqe tsaye ya je ya ba ma Yousuf hannu dan su gaisa, kamar ba zai miqa masa nashi hannun ba, ya miqa mai  ya koma d'aya daga kujerun parlourn ya zauna ya hard'e qafa, qasa ta yi da kan ta, da a ce zasu kasa kunne da sun ji yanda zuciyar ta ke bugawa, Abbah ne ya yi sallama a tsakar gida, nan da nan ta yi wata ajiyar zuciya me qarfi, fit ta tashi da sauri ta fita waje, zuwa ta yi ta kama hannun Abba suka shige dakin su, tana shiga ta fara buga qafa irin na shagwab'ar da ta Saba yi wa Abban,

" Abba tin d'azu nake jiran ka, Hassan yazo ga Yayah can yana ta b'ata rai , yayi fushi, ni kuma bani na kawo Hassan ba, ganina ya yi a hanya muka gaisa, na zo da shi dan bana son mu tsaya a waje, ina son na masa bayani, akan ina da wanda nake so, amma Yayah kamar ba zai gane hakan ba gaba d'aya ya b'ata rai,"

Hawaye ne ya gangaro mata, Abba murmushi ya yi dan ya gane a rud'e take sosai,

" kwantar da hankalin ki ina shi Yousuf d'in yake? Muje na gan su"

Noqe kafad'a ta yi ta zauna gefen Mama da ta fara bacci,

," A'a Abba ni dai bana son na sake ganin Fuskar Yayah sai ya sakko, tsoro nake ji,"

Dariya ta ba Abban ya fita, ta kama hannun ta ta saka a baki tana cisgar farcen ta tare da qurawa qofa ido, ta kasa kunne sosai dan ta ji me za a ce, Abba ne ya musu sallama ya Samu waje ya zauna suka gaisa da Hassan ya bashi baki akan ga abinda ke akwai na auren Yousuf da Atiyyaerh,  hankalin shi ya yi matuqar tashi a karo na biyu, hawaye ne suka zubo ya yi saurin d'auke su, amma ya makara a kan idon Yousuf, jikin Yousuf ya yi sanyi, dan ya tabbatar ba qaramin so yake wa qanwar tashi ba, amma sawun giwa ya take na raqumi, shima in ba ita rayuwar shi zata shiga hatsari, hakuri ya ba Hassan cike da dakewa ya nuna masu ya gode zai wuce amma yana son a mai alfarmar ganin ta ko da sau d'aya ne, kishin Yousuf ne ya motsa ya dan had'e rai, ya ce,

" Minti 5 na baku danni sauri nake zan tafi nima,"

Murmushi Hassan ya yi dan ya gano Yousuf d'in kishi ke damun shi, se ya dafa kafad'ar shi yace ,

"Ni minti 2 ma ya ishen,"

Abbah ne ya yi murmushi ya miqe ya shiga ciki, tana ganin Abba ta miqe tana zaro ido da son Jin me ya faru, cikin tsokana Abbah ya ce,

"ki je yayan ki na can na fada akan kin kawo wani,"

Hawaye ta fara tana yarfa hannaye, Abba dariya ya saka yace,

"Matsoraciya waya fad'a maki ana tsoron miji? Ba tsoro tsakanin ma'aurata sai dai biyayya, da ladabi, in kina jin tsoron namiji sai ya ci kashi akan ki, amma in kina mai biyayya sai rayuwar ku ta zama abin burgewa, kin ji ko, share hawayen ki wasa nake maki,"

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now