💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 15:
Ko da na bi inda Rasheedah ke kallo sai na hango Mama d'auke da Atiyyaerh a cinyar ta, tana shafa bayan ta a hankali a haka har ta yi bacci, komai akan idon Rasheedah ke faruwa, d'auke idon ta ta yi ta zumbura baki gaba dan ganin ga ta ta yarinyar a gefe amma a qasa ko Maman ta d'an jingina ta da jikin ta, nan da nan abun na ta ya motsa, ta d'aure fuska, ta kira Afrah, maqe kafada yarinyar ta yi taqi zuwa, sai ta matsa kusa da Mama sosai, daidai wajen Atiyyaerh, itama ta kwantar da kanta, murmushi Mama ta yi ta shafa gashin ta, a qasan zuciyar ta tana nema wa Atiyyaerh sauqin zama a wajen Rasheedah Koda ta hanyar Afrah ne.
Bakwai na cika dangi na nesa da na kusa kowa ya tattara ya koma mahallin sa, Mama sai ta wuce da Atiyyaerh gidan ta, Rasheedah ba qaramin Jin dad'in hakan ta yi ba, dan a zaton ta sun manta da wasiyyar da Sakeenah ta bar musu, ko Kuma tinda sun San halin ta ba za su yarda yarinyar ta zauna a wajen ta ba, Dan haka gida ya rage Daga Masu aiki sai Adnan,Adnan d'in kuwa dama shi ko zaman makoki da ake a farfajiyar gidan shi ba zama yake a wajen ba, ko waye ya je masa gaisuwa sai dai ya tarar da su Abba ya musu gaisuwar ya juya, Koda yaushe ya na sama cikin d'akin shi, daga sallah sai tasbihi da roqar wa matar shi da iyayen shi Rahamar Allah, Jin shi yake kamar ba zai tab'a Iya ci gaba da rayuwa Mai dad'i ba a yanzu da ya rasa jigon rayuwar ta shi.
A qarshen satin Abba yace ma Adnan ya qoqarta had'awa Atiyyaerh kayan ta da dik Wani abu da ya dace dan damqa ta wajen sabuwar Uwar ta ita wasiyya ana so a gabatar da ita da gaggawa, hankalin Adnan ba qaramin tashi ya yi ba, yayi kuka ba iyaka, da kan shi ya lallashi kan shi, dan ya san cika umarnin Sakeenaahn shi zai yi ya riga ya mata alqawari, yana daga cikin wasiyyar ta da ta dinga jadaddawa kafin ta mutu, kuma ya kamata a cika mata ita, had'a kayan Atiyyaerh ya shiga yi idanun shi na zubar da hawaye, yana cikin hadawar ne ya ga wasu takardu guda biyu, daya duba sai yaga
*Zuwa Ga Ablaerh My Love*
Sai dayar kuma an rubuta,
*KAI NE JARUMI NA*Daukan ta Atiyyaerh ya yi ya ajiye a gefe ya bude tashi, gaba d'aya fuskar shi ba komai sai hawaye, tayi jawur da ita,
*Mijina*
*Kai ne jarumi na, kai ne hasken idaniya ta, kaa zauna dani cikin so da qauna, tare da amana, ka zama jigon rayuwa ta, kai ne Wanda in nayi kuka kk sharen hawaye na, in nayi dariya kk tsayawa ka kalli kyau na ka yaba min,in nayi girki kai santi ka yabi aiki na*
*Jarumi na, ina qara roqon ka akan ka daure akan abinda na yi wasici akai, ba dan ba ka da iko akan d'iyar ka ba, sai dan na san Jarumtar ka zata sa ka yi hakuri, dan cikar burina, fatana ka yi ta min addu'ar samun sa'a akan quduri na kar ya zama ba nasara*
*Allah ya had'a fuskokin mu a jannatul firdaus, mu d'ora rayuwar aure fiye da wadda muka yi a nan duniya Mai Cike da tsafta da jin dadi, INA SON KA MIJINA JARUMI NA*
*DAGA MATAR KA SAKEENAA*
Saka takardar ya yi a qirjin shi yana kuka, a qasan zuciyar shi kuma yana jin kwarin guiwar rabuwa da gudan jinin tashi, ci kaba ya yi da had'a kayan ta, bayan ya gama da kayan nata ne ya dauki wayar shi ya koma d'akin shi, (ban san me ya ke fada ba tinda ya rufe ta ciki☹) bayan zuwa kamar awa d'aya cur ya fito d'auke da wasu akwatuna da jaka a rataye a kafad'ar shi, qasa ya sauka ya kira driver din shi, bayan ya shiga ya gaishe da Adnan,sai Adnan ya bashi umarnin d'iban akwatunan daya d'akko daga d'akin shi zuwa qasa, sanan ya koma ya dakko kayan Atiyyaerh, ya zauna a kujera ya na kallon cikin gidan, daga baya ya miqe ya fita cikin hanzari yana share kwalla, zuciyar shi na tinano masa irin zaman so da qauna daya faru tsakanin shi da Sakeenaah a cikin gidan, d'aya motar ya bude ya zuba kayan Atiyyaerh a ciki,ya ja da kan shi, ya nufi gidan Mama, yana zuwa ya yi parking a farfajiyar gidan sannan ya shige ciki, Atiyyaerh na ganin shi ta daka tsalle ta d'ale shi tana masa surutai, wani ya gane wani Kuma bai ganewa, shi dai ba ya buqatar ganewar ma, kallon ta kawai yake kamar wanda ba zai sake ganin ta ba, Abba ne ya fito Mama na biye da shi,
"Aa Adnan kaine tafe, barka da zuwa, Bismillah zauna mana ka ke tsaye"
Isa gaban Abba ya yi ya bashi hannu kan shi a qasa kamar yanda suka Saba gaisawa, bayan sun gaisa ne ya gaida Mama ta amsa cikin sakin fuska da tausayawa, janyo kayan Atiyyaerh ya yi gaban su, sannan ya miqa wa Mama dan akwatin da ake saka mata kayan adon ta, musamman na gashi, share hawayen da ya gangaro masa ya yi sannan yace,
" Abba ina neman izinin ku akan tafiyar dana yanke hukuncin yi, zuwa Dubai, domin ci gaba da kasuwanci na, a yanzu banda sauran dalilin zama anan, sai dai inna tafi zan din ga zagayowa domin ganin ku,ku kad'ai nake kalla a matsayin iyaye, dan haka ba zan dad'e ba zan dinga zuwa ganin ku, sai dai duk abinda nake fad'a yanzu sai fa Kun bani izinin ku zan aikata shi,"
Kan shi a qasa, yana sauraran amsar su,ya na addu'ar Allah kar ya sa su dakatar da shi, dan baya Jin zai iya ci gaba da Zama a Nigeria kusa da 'yar shi ya na ji ya na gani ta na rayuwa a hannun Rasheedah,
"A gaskiya Adnan dole na jinjina Maka domin kuwa na yarda da sunan da Sakeenaah ke Kiran ka da shi na *KAI NE JARUMIN ta* domin kuwa a iya tsahon rayuwar ka ka ga abubuwa kala2, dan haka ina son wannan karon ma ka zama jarumin wajen sanyawa zuciyar ka hakuri, in dai tafiyar ka zata sama maka kwanciyar hankali ni dai na maka izinin tafiya, Allah ya sanya albarka, ya kare mana kai dik inda ka shiga, nasihata a gare ka ka zama mai tsoron Allah, kar ka zama mai sab'a masa ko ketare dokokin shi, in kai haka Allah zai kare ka ya kiyaye ka,sannan Kuma ka samu ka je wajen Baffanin ka da Kawunan ka ka musu sallama kar ka tafi ba tare da sanin su ba"
Kallon Mama suka yi da ta sha majina irin na masu kukan nan,
"Adnan Allah ya maka albarka, ya faranta maka, Allah ya jiqan mahaifan ka da Sakeenaah ya raya abinda kuka haifa Allah ya kare mana Kai a dik inda ka shiga, Allah ya habaka kasuwancin ka Ameen,"
Amsawa suka yi dikan su da "Ameen" sannan sika miqe don raka Adnan zuwa waje, wasiqar da ya ga an rubuta sunan Atiyyaerh ya zaro a aljihun shi ya damqa a hannun Mama sannan ya yi gaba zai fita,Atiyyaerh ce ta riqe shi tana kuka, tana kiran Mummyn ta, Adnan zuciyar shi ta cika fam da quncin rabuwa da mutanen da yafi so a rayuwar shi, bai san sanda ya yakice ta ba ya shige motar ya ja da gudu yana kuka, Mama da ta sunkuya ta d'aga Atiyyaerh dake birgima a qasa, kukan itama take, Abba share kwallar shi ya yi ya taimaka mata sika d'aga ta, dan ji ta yi ta yi mata nauyi, sai tirjewa take, tana kiran Daddy da Mummyn ta, a haka sika shiga,Mama ta goya ta,yar wayar shi Abba ya lalubo ya kira Auwal.
Ba su fi awa biyu a zaune ba Auwal da Rasheedah suka shigo, bayan gaishe2 ne, Abba ya sanar masu da dalilin kiran nasu dika, ya kira su ne dan damqa amanar da marigayiya Sakeenaah ta bar masu, Rasheedah ce ta bata rai sosai, sannan ta ce..........
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....