💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA? To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️*
*Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal*
Page 33:
Se da ya gama lallab'a ta sannan ya tambaye ta abinda take so ta karya da shi, nan ta shiga zayyano masa abubuwan da take so Cike da shagwab'a shi Kuma ya na haddacewa , da kyar ya samu ta yi bacci sannan ya rufe ta ya ja mata qofar a hankali ya fito.
Yanda suka barta a haka ya tadda ta, be damu ba ya hau bata umarnin ta dora abin karyawa saboda kar amarya ta tashi ba abinci, Kuma amarya ta na so a yi mata farfesun kayan ciki dan tana buqatar abu me d'an yaji yaji da ruwa ruwa,ta had'a da chips sannan ta soya qwai, sai ta mata kunun gyad'a, yanda yake fad'an saqon amaryar cike da umarni da izza abun ya gama gigita Rasheedah yau ita ake bawa Umarnin yi wa kishiya girki? Ga shi a yanda yake mata maganar ba wargi bata isa cewa dan me ba shiru ta yi dan tana gudun ya liqa mata duka ya qarasa zubar mata da d'an mutuncin da ya yi saura gaban 'yar cikin ta, ita yanzu gaba d'aya tsoro ma yake bata, ba qaramin canjawa ya yi ba, yana juyawa zai tafi ya yi Wani mugun murmushi, dan tabbas ya san amaryar shi mai Suna Khadeejah na da kirki sosai da sanin ya Kamata, ga ilimin addini da na zamani daidai misali, amma fa ya san tana da wani hali guda d'aya wato tsanar duk wani mai mummunan dabi'u wanda kuskuren da ya yi kenan wajen neman auren ta da ya yi ta hanyar zayyane mata halayen matar shi, a da yayi haka ne dan ita in tazo ta tausayawa Atiyyaerh ta bata kulawar da Rasheedah ta gaza bata,se ga shi ma bata ci gaba da zama da su ba ta koma wajen su Mama, amma yanzu ya gane kuskuren da ya yi na fad'a wa macen da zai aura halin matar shi ta gida,dan ya kula amarya so take ta ci qaniyar Rasheedah da kyau, zai bar su kuwa har zuwa lokacin da Rasheedah zata yi hankali Yana tafiya ya na magana shi kad'ai,
"Ai ko ba zan hana ba, yanzu ne zata san a ina ya kamata mace ta yi kishi sannan shi kishin ya ake yin shi,"
Ya sake yin wani murmushin mugunta ya fad'a d'aki, Khadeejah kuwa har ta tashi ta shiga wanka sai shima kawai ya fada suka yo wankan su fes bayan soyayyar su da suka sha, dik da ta na Jin kunyar shi a matsayin ta na mace Kuma budurwa, burin ta a gidan yanzu shine ta na so ta yi maganin Rasheedah dan haka in Auwal ya yi mata wani abu musamman wanda ya ke sata dariya topa zata ware murya ne tai ta dikar dariya,sedai ba irin dariyar nan mara dad'in sauraro take yi ba,ah ah ta na Yi ne cike da salo da yanga a ciki,Auwal d'in duk na kula da ita,ya kan sha dariya sosai shi d'aya ya jinjina kaidi irin na mata a ran shi.
Bayan sun kammala shiryawa ne ta ce Masa,
" Honey ni na gaji da zaman d'aki, muje Parlour, yunwa nake ji sosai, kaga tana gamawa kawai sai muci ko,"
Ta fad'a tana wani rausaya, aiko Auwal kamar raqumi da akala haka ya rungume ta a jikin shi suka nufi Parlour, Rasheedah kuwa da ta d'akko palates zata aje a dinning ce ta d'aga Kai ta hango su suna fitowa manne da juna, Khadeejahn ta Wani maqalqale shi sai shagwab'a take ta na Washhh ita jikin ta ciwo yake, suka samu kujera suka baje, suna maida nunfashi, cikin dariya Khadeejah tace,
" Honey kasan me?"
Ya girgiza kai dan ba qaramin kai shi duniyar wata take ba,
"Lips din ka wani zaqi suke da shi kamar zuma, bana gajiya da sumbatar su"
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....