💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 18:
A tsorace Atiyyaerh ta ja da baya,cab'al qafar ta ta shiga cikin kashin, yanda Rasheedah ke matsowa tana masifa haka Atiyyaerh ke ja da baya, tana tattaka waje da kashin, wata tsawa Rasheedah ta sakar mata akan ta tsaya ta daina yad'a mata kashi a ko ina, gigitaccen kuka yarinyar ta saki mai qarfi jikin ta babu inda ba ya rawa, Yousuf kanshi sai da ya firgita, ya durqusa gaban Ummar tasu ya na kuka ya ce,
" Umma dan Allah kar ki daki Ablaerh, ki yi hakuri, zan gyara maki wajen,"
Haushi ne ya qara kama Rasheedah ganin yanda d'anta ke kuka akan wannan sokuwar yarinyar, aiko sai ta ci uban ta yau, kallo ta watsa masa da ya sa shi miqewa ya yi gefe ba shiri, zuwa ta yi ta damqi Atiyyaerh da gashin kanta ta wanka mata mari biyu masu kyau, sannan ta kama kunnen ta ta yanka mata warning din daga yau kar ta sake ganin qafafun ta a parlor in dai ba ita ta kira ta ba, sannan ta tsaida ita gefe ta je d'akko abubuwan da zata gyara waje da shi, in banda a jiyar zuciya yanzu ba abinda Atiyyaerh keyi, dan ta kasa kukan ma, zuwa ta yi tana goge wajen tana zagin ta, bayan ta gama ta dauke ta a wulaqance tai bayi da ita, wanke mata ta fara yi da tsintsiya,a cewar ta bazata saka hannun ta ba bata son taba kashi, ko wa ya ke wanke wa Afrah Kashi oho? duk haka ta sossoke mata duwais da tsintsiyar yarinyar kuwa haka ta dinga kuka saboda azabar zafin da take ji, sai da ta rage kashin sosai sannan ta saka leda a hannun ta ta wanke mata, da ruwa mai sanyi, hankado ta ta yi waje tace taje ta kwanta ta yi bacci, cikin ajiyar zuciya irin ta wadda ta gaji da kuka Atiyyaerh ta tafi ta kwanta, jikin ta ba kaya sanyi duk ya dame ta, a fusace ta bar dakin, Yousuf ne ya shiga da gudu ya je ya rungume qanwar tashi suka yi ta kuka tare, tin daga nan ya dasa qiyayyar mahaifiyar shi a zuciyar shi, domin ganin mugun abun da take aikatawa qaramar yarinya, ruwan d'umi ya samo da taimakon Sulaiman a saman dinning na cikin flask dan basu Iya kunna ruwan zafin bathroom d'in ba da ruwan sanyi suka had'a daidai wanka suka mata wanka me kyau,Suna gamawa suka hau duba kayan da ya dace su Sanya mata a garin haka ne suka yi kaca kaca da wajen kayan sawar nata ba tare da sun Wani damu ba suka zab'ar mata wata riga da wando na sanyi suka sa mata,ba jimawa bacci Mai nauyi ya d'auke ta sai ajiyar zuciya take saki.
Cikin tashin hankali Sulaiman ya kalli Yousuf dan ganin b'arnar da suka tafka na fasa flask din ruwan zafin da suka yi wa Atiyyaerh amfani da shi, Rasheedah na jin qarar ko ta fito kamar wata mahaukaciya,
"kan uban can , a cikin ku waye ya fasan flask, ko uban ku ne ya siyo da za ku fasa min?"
" Umma ni ne na fasa ba da sane na ba, amma kuma ai kema ba ke kk siyo ba, Mummyn Ablaerh ce ta siyi abin ta," in ji Yousuf da ya kafe ta da Ido Shima cikin rashin kunya.
Mari ta daga hannu zata kai masa, Auwal da ya shigo da manyan ledoji niqi niqi a hannu ya ce,
"kina taban yaro yau na lahira sai ya fiki jin dad'i, dan se na maki dukan da ban taba maki irin shi ba jakar banza wadda bata da hankali, Rasheedah a kullum garin Allah ya waye se na zagi Kai na na Kuma yi wa kaina Allah ya qara dan son zuciyata ya kaini yi maki qarya na aure ki, ga sakamakon abinda na aikata nan Ina girba, ke din wata iriyar jarabawa ce mummuna a gare ni, a kullum Ina danasanin sanin ki a rayuwa ta, yanzu me ya faru? Me ya miki ki ke so ki dake shi? Ina Afrah da Atiyyaerh?"
Ido ya zuba mata Yana son Jin qarin bayani, Kalaman shi sun yi matuqar sukan zuciyar ta,ta ji zafin kalmar shi na ita d'in mummunar qaddara ce a gare shi, hawayen ta ta mayar ta na sauraron Yousuf da ke rattaba masa bayani akan abinda ya faru, kallon ta kawai ya yi da takaici ya ja hannun yaron suka wuce ciki, Yousuf Jin shi yayi kamar wani JARUMIn maza, da qananan shekarun shi ta dasa masa qiyayyar ta, da son kare Atiyyaerh ko da zata dake shi shima,ya qudurta ko kashe shi ma zata yi sai dai ta kashe shi amma ya dena shiru in tana zaluntar Atiyyaerh,shi yanzu ma ya dena son ta Mummyn Ablaerhn shi yake so, in ta dawo daga tafiyar da Abban su yace sunyi ita da Abban Ablaerh wajen su zai koma da zama.
*BAYAN SHEKARA UKU*
Yousuf ne ya fito da shirin zuwa makarantar *AL-ANSAR* da ke unguwar maqotaka da su, Atiyyaerh ce ke kallon shi Cike da sha'awa, Yousuf d'in ne ya Sanya ta zamo Mai tsananin son karatu, tinda yana koya mata karatu idan ya dawo ko sanda baya komai a gidan, Atiyyaerh na ganewa sosai kuma ta na da saurin daukan karatu,dafa Auwal ta yi da yake Saka takalmin shi a zaune a gefen kujerar da ke kusa da qofar fita daga parlourn,
" Abba nima ina son a sani a school din su yaya,"
Murmushi Auwal ya yi sannan ya d'aga ta sama yana mata wasa suna dariya, Afrah na gefe tana tsotsar hannun nata da ta saba, Rasheedah ce ta fito ta kalle su ta kalli d'iyar ta a gefe dake kallon su tana murmushi tana tsotsar hannu,
"Ikon Allah, wannan shine agola yafi dan gidan,"
Sannan ta wuce kitchen, sai da ta dawo ne Auwal ya bata amsa da,
"Tabbas wannan shine agola yafi d'an gida, domin ke da kk zo da gayyar ki gidan yarinya har da mijin ki, ke kk neman mallake wa yarinyar gidan ta, makaranta nake son saka ta, da kud'in ta, dan ubanta ya bada kud'in zuwan ta makaranta, har jami'a, sannan ya had'a da naki yaran, dama lokaci nake jira, dan haka gobe2n nan ba jibi ba zan d'auke su ita da Afrah na kai su makaranta suma,"
Tsallen murna Atiyyaerh ta saka, Yousuf na mata dariya, ya ja hancin ta, ita ko Afrah kuka ta saka, ita bata son makaranta, duka ake in ji Yah Sulaiman, da kyar Auwal ya rarrashe ta ya mata bayanin yanda lamuran makaranta yake in baka Jin magana baka karatu to fa zaka daku, amma in kana Jin magana Kuma ka na da qoqari se dai a baka kyauta amma ba duka ba, ta na Jin haka se ta yi shiru, had'e su ya yi dika ya fita dasu ta ci kanta dan tinda ya ce zai Saka Atiyyaerh a makaranta ta ke bala'in kashe kud'i za a yi a banza,se da ya qara saiwa yaran abun kwalama sannan ya aje su a makatanta, yawatawa ya yi ta yi da su Afrah,kafin su nufi hanyar gida Afrah ba wani ci take ba dan tafi ganewa tsotsar hannu, Atiyyaerh kam ta dage ta yi ta ci, dan ta san wataqila da sun je gidan shikenan ta gama ci kenan, ya maida su gida ya yi shirin fita aiki, ya qara jan kunnen Rasheedah akan amanar da aka bata, yana fita kuwa tace da wa Allah ya had'a ta bada Atiyyaerh ba, dukan ta ta hau yi tana zagi,
"Munafuka mai halayya irin na uwarta sak, ku dinga simi2 da kai, kamar na Allah, kuna cutar da wanda kuke tare da su, sarai kin san Afrah bata son makaranta kike wani tsalle, dan za a saka ku, dan kija ace ke mai hankali ko? Ita mara son makaranta ko? Kuma wane munafikin ne ya ce ki ce asaka ki ? Yau sai kinci ubanki, gobe in ya ce zai kai ku kice zaki kigani yanda zan kakkarya ki a gidan nan"
Sai da ta mata lilis sannan ta tura ta d'aki ita d'aya, Afrah ma miqewa tsaye ta yi zata bi bayan Atiyyaerh, Rasheedah ta daka mata tsawa akan ta koma ta zauna, aiko ta saka kuka sosai, taqi komawa ta zauna d'in, hannu ta miqa dan ta ja ta jikin ta ta hana ta, yarinya kuwa ta kwasa da gudu ta yi dakin, tana shiga ta kulle, kuka ta tadda Atiyyaerh nayi, bata ce mata komai ba ta zauna gefen ta ta saka hannun ta a baki tana tsotsa hawaye na zuba mata, a haka har su ka yi bacci suna ajiyar zuciya.
Bayan Yousuf sun dawo ne yake tambayar ina suke , Auwal ma tambayar ta ya yi inda yaran suke da ido ta yi nuni da d'akin su,kallon su ta yi ta ga yanda suka bi hanyar Suma da idanun su, se kawai ta yi murmushi, dan ta san qaryar da zata yanka masu, kwata2 bata son Atiyyaerh taje makaranta, bata son ta samu Wani abu na ci gaba a rayuwar ta sam........
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....