KAI NE JARUMI PAGE 12

28 2 0
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼

  

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 12:

Wata iriyar wahalalliyar naquda Sakeenaah ke yi,ta wani fannin ta sanya matsanancin tsoro da fargabar shin zata rayu da abinda take ta fata Allah ya bata shekara da shekaru ko Kuma mutuwa za ta yi? Wannan dalilin ne ya janyo jinin ta ya yi bala'in hawa, ba abinda take sai addu'o'i, wanda kusan rabin addu'ar tana nemar wa kanta rahamar Allah ne, sai kuma daidaito a tsakanin zumuncin ta ita da yayar ta, anyi inducing din ta kafin ta samu haihuwa, kukan jaririyar su ne ya karade ko ina, na dakin har da Wani sashe na asibitin ma.

Dik halin nan da Sakeenah ke ciki Adnan na gefen ta ya na riqe da hannun ta ko yatsina fuska ta yi sai ya mata sannu,in ko ya ga hawaye a idon ta na gangara haka Shima nashi idon zai ta zubar da ruwa addu'a kuwa bai San Iya adadin abinda ya roqar mata ba da abinda zata haifa, sai da naqudar ta taso gadan gadan ne aka tada shi d'aga wajen ta ya tsaya a gefe, ma'aikatan lafiyar suka duqufa dan taimaka mata ta haihu.

A lokacin da kukan jinjirar ta su  ya shiga kunnuwan shi kuwa rikicewa ya yi da murna da kuka, ba b'ata lokaci ya dora goshin shi a qasa dan godiya ga Allah, ya na d'agowa ya je jikin gadon ko gama gyara Sakeenaah ba a yi ba ya rungume ta ya hau sumbatar ta yace,

"Sannu my love dama na fad'a maki ke Jaruma ce, kin ga qoqarin da ki ka yi ko?Allah ya miki albarka, Masha Allah Atiyyah (Kyauta )ta iso Allah ka raya mana ita da imani,ka ba maihaifiyar ta lfy, ni kuma ka qaran arziqin kula da ita,"

Murmushi Sakeenaah ta yi mabayyani, bayan an dora mata yarinyar tasu a jikin ta ta kalle ta ta sake  murmusawa a karo na biyu sannan ta ce,

"Tabbas Ablah(cikakkiya daga kyaun halitta)  ta iso, Masha Allah ka ga yarinyar nan ba inda ta baro mu,"

Ta daga kai tana kallon mutane hud'u dake dakin, Doc. Midwifes biyu, da mijin ta Adnan, dan ta samu tabbacin maganar ta, gaba dayan su kad'a kai suka yi cikin yarda da maganar ta sosai,

"Tabbas wannan gaskiya ne madam, barakallah yarinyar nan ta na da kyau anya mun tab'a karbar kyakkyawar haihuwa irin wannan kuwa?" inji likitan,

"Gaskiya tinda muke bamu taba karbar haihuwar kyakkyawa irin wannan ba, kalar ta daban ne, Allah ya raya maku ita da imani," in ji d'aya d'aga cikin midwifes din,

" Ameen"

Suka amsa dika, nan take Adnan ya karbe ta ya mata addu'oin da suka zo  a sunnar Annabi Muhammad ana yi wa jarirai, sannan ya miqa ta ga Sakeenaah ta tauna dabino ta bata, nan danan ko ta tsotse shi tass, tana gamawa aka bata nono ta sha, sannan Doc. Yace su bada ta ai mata wanka a kawo masu ita, dai dai nan Mama da ta gaji da Jira a  bakin qofa ta shigo, itama ta na ganin yarinyar sai da ta yi sujjada dan godewa Allah, sannan tace a basu su dika su tafi ba maganar wani wankan asibiti tinda sun goge ta tas, haka kuwa aka  yi Sakeenah da baby na gama cika awannin da ake bayan an haihu a asibitin aka sallame su suka yi gida, gidan ta aka wuce da ita, dan basu shirya tafiya wankan gida ba, Adnan tuni ya sanar da ita baya so, shi a barshi komai a nuna masa zai mata Mama ta ce inaaa zaman biqi ba aikin namiji bane, ya dai bari a mata anan d'in tinda baya so ta je gidan ita ta zauna mata dan Maman ta kula da gaske baya son ta yi nesa da shi,suna isa kuwa ya daura ruwa a qatuwar tukunya, Mama ta shiga ta mai sannu tana tsokanar shi angon qarni, yana sunkuyar  da kai yana shafe qeya, fita ya yi yaje d'aki, ya isko Sakeenaah na ta bacci, tea ya hada mai kauri ya tada ta ta amsa tasha,su Shamsiyya kuwa dama ba yau suka Saba ganin yanda yake wa matar tashi hidima ba, Adnan mutum ne da ke kyautata wa matar shi kwatankwacin yanda take kyautata masa koma a ce fiye da hakan.

Kitchen ya sake komawa ya bud'e fridge da freezer dan ya tabbatar in akwai komai da suke da buqata ko Kuma akwai buqatar qarowa, ya na tsaye ya na nazarin wajen ya hango wata roba da aka shaqe da farfesun kayan ciki dakkowa ya yi ya bud'e ya ji yanda qamshi ke tashi Shamsiyya ya kwalawa Kira ta zo cikin hanzari ta durqusa ya miqa mata tare da bata Umarnin ta dumamawa Sakeenaah.

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now