KAI NE JARUMI PAGE 30

31 4 0
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼



WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



Page 30:

Iska ya shaqa tare da lumshe ido, ya d'auki a qalla second fiye da 20 kafin ya bud'e idon shi, kallon filin jirgin Aminu Kano yake kamar wani baqo a qasar, yayi matuqar kyau, fuskar shi ta yi fresh ya aje gemu me tsaho me sheqi kamar Wani baqin balarabe,fatar shi mai ruwan chakulan ta yi luwai luwai irin na 'yan hutu, ba qaramin kyau ya yi ba, yana kalle2 ne ya buge wata matashiyar yarinya, da ba zata wuce shekara 27 ba, juyowa ta yi cike da nutsuwa fuskar ta sanye da niqab ba a ganin komai a jikin ta sai idanuwan ta, hatta da hannayen ta da qafar ta sanye suke cikin safa, doguwar rigar da ta Sanya ta yi mata das a jikin ta gwanin sha'awa sai ta yafe Kan ta da mayafi baqi, Ido suka had'a da wanda ya buge ta, tsayawa ta yi tana kallon shi, ba qaramin tafiya ya yi da ita ba,tin bayan rasuwar Sakeenaah be tab'a tozali da idon macen da ya fizgi hankalin shi ba sai yau,yarinyar ta yi matuqar burge shi, yana yin shigar ta sai ya tina masa da margayiya, nan take ya d'auke kan shi, tare da bata hakuri, dan a tinanin shi matar aure ce, murmushi ta masa ta nuna mai ba komai, bayan ya fita ne ya tadda drivern shi, sai washe baki yake ,bakin nashi yaqi rufuwa, da gudu ya isa ya rungume uban gidan nashi, har hawayen farin ciki sai da suka zuba masa, shima cike da murna ya rungume shi, budurwar nan tana kallon su cike da sha'awa, itama motar da zata d'auke ta ne ta tsaya gaban ta, shiga ta yi drivern ta ya ja ta,Adnan Shima ya shiga tashi suka fara tafiya, drivern shi na ta bashi labarai akan abubuwan da ya Saba Sanar da shi tin bayan tafiyar shi ba tare da kowa ya san shi d'in ido da kunnen Adnan d'in bane,cike da jiman ta sabbin abubuwan da ya ji a yanzu ya ke jinjina Kan shi,har suka isa wani jibgegen gida Mai matuqar kyau da tsaruwa, bud'e masu gate d'in aka yi, tin kan motar ta gama shiga gidan wannan motar da ta d'auko yarinyar nan ta shiga gidan dake kallon gidan da Adnan ya shiga, juyawa ta yi ta kalli gidan, kan a rufe gates d'in kowanne gidan a tsakanin su, Mai gadi ma da sauri ya duqe gaban Adnan yana kukan farin cikin sake ganin shi,

"Ashe da raina Allah zai nufa na sake saka ka a ido na, kaiii Allah na gode maka,"

Daddy ne ya d'aga shi, ya miqar da shi, ya rungume shi suka gaisa a haka, sannan baba Mai gadin ya koma ya qara tabbatar da rufe gidan suka dunguma suka shiga ciki baki d'ayan su, direct d'aki Adnan ya shiga,ya rage kayan jikin shi, ya shiga bathroom ya yi wanka, ya dad'e yana zubawa kan shi ruwa, yana tsaye yana tina masoyiyar shi wadda bata tab'a barin zuciyar shi ba ko da da minti d'aya ne, haka ya fito ya shafe jikin shi da mayuka, ya fesa turaruka, ya saka jallabiyya, ya fita dinning dan kukun shi ya yi masa waya ya sanar da shi abincin is ready, zuwa ya yi yaci ya sha, sannan suka zauna dika suka sha hirar yaushe gamo, suma wannan abincin da yaci shi suka ci, Adnan ne ya ce,

"Da daddare zamu je ka kaini gidan mu na ga Abbana, da Mama na, ba qaramin kewar su na yi ba, ni yanzu Atiyyaerh ce babbar damuwa ta,ka na ganin in ta ganni ba zata ji haushi ba? Wanne irin reaction ka ke ganin za ta yi?"

Ya na gama fad'in haka se ya sadda kai qasa, idon shi, ya cika da kwalla,cikin tausayawa driver ya ce,

" Ranka ya dad'e kar ka saka wannan a rai ya dame ka, inshaa Allah fushin ta ba zai wuce yau ba, ka kwantar da hankalin ka, yarinya ce da ta haifu daga wajen marigayiya, yarinya ce mai biyayya da hakuri da yafiya, indai zata yafewa Waccan shaid'aniyar to ko zata yafe maka,"

Adnan ya gamsu da bayanin driver ya kad'a kai, a haka suka d'an taba hira ya je ya yi sallar la'asar, bayan ya idar ne ya fita dan shan iska, daga saman balcony ya hango wata kyakkyawar halitta, baqace doguwa mai shape mai kyau, ta saka riga mai siririn hannu, fara sol, sai gashin ta da yake a d'aure, ya zauna a dokin wuyan ta irin gashin nan ne na 'yan Afrika Mai cika da tsaho,hannun ta riqe da mug ta na kora baqin shayin da ke turiri, sai d'ayan hannun tana danna wayar ta, direct wajen wata kujera ta nufa, da qaramin table a wajen, ta aje mug d'in ta ci gaba da danna wayar ta, band din da ta d'aure gashin kanta ta cire ta baza gashin, tai gaba da shi sannan ta saka hannun ta ta baza qasan shi, kamar mai susa kamar me son shan iska a cikin gashin nata, Adnan bakin shi a sake ya na bin ta da kallo, d'agowar nan da zata yi, tana lumshe ido dan dad'in susar da take wa Kan ta,idanun ta suka sauka akan fuskar shi, dake kallon ta, cike da kunya ta fara dabur2 din me zata yi, d'aga hannu ya yi alamar ta yi hakuri, murmushi ta yi tai saurin miqewa ta nufi hanyar da zata shigar da ita d'akin ta, ko mug d'in bata tsaya d'agawa  ba tai gaba, daidai zata shiga ciki ne ta juyo suka sake had'a ido, murmushi suka yi wa juna ta shige ciki, Daddy ne ya shafa gemun shi, mai cilli2n furfura a jiki, ya yi murmushi, ya koma d'akin shi, fuskar ta kawai yake hangowa,can ya ce,

"Subhanallah in tana da aure fa?"

Tashi ya yi daga kwantawar da ya yi, yana nazari, nan jikin shi ya yi sanyi, dan yanayin ta ya mai kama da marigayiyar shi,

"Allah kasa bata da miji, tabbas zan gabatar ma da su Abba daddad'an labari na samun matar da zan aura na San za su yi farin ciki sosai, baffana har ya yi fushi ya dena d'aukan wayata saboda sun bani Umarnin neman mata na yi aure na qi, in Allah ya cika min buri na sai dai na je Sanar da su maganar aure" 

Da wannan zantukan ne ya miqe ya fad'a bathroom dan d'aura alwalar sallar magrib da ya ji ana ta Kira, sannan ya fita masjid dan yanzu ba gajiya a tare da shi kamar d'azu, ya na fita suka had'u da wani dattijo da in zai girme shi bai fi da irin 4 to 5 years dinnan ba, suka gaisa, suka shiga masjid d'in a tare, bayan anyi sallah ne sun fito zasu koma gidan su, suka qara gaisawa, inda mutumin yake sanar da shi shi maqocin shi ne ashe, sanar da shi ya yi sunan shi Alhaji Haladu Gwandu, yana da mata da d'iyar su da ta dawo ba jimawa d'azu daga Dubai  mai suna Fauziyyah a can ta yi karatun ta, ita d'aya Allah ya basu, shima sanar da shi ya yi taqaitaccen tarihin shi,nan take mahaifin Fauziyya ya masa ta'aziyyar rasuwar Sakeenaah, sannan ya masa fatan samun mace ta gari, sukayi sallama da juna kowa ya shige gida, direct d'aki ya je ya shirya cikin shigar da kowa ya gan shi sai ya qara, dan kuwa komai ya ji, fitowa ya yi yana baza qamshi, ya yi wa Auwal waya yace su had'u a gidan Abba, fita ya yi inda motocin shi suke ya shiga wadda driver ya tada, Baba me gadi ma tini ya bud'e gate shi kad'ai ake jira dama, driver ya ja su sai gidan Abba.

Kowa ya shirya cikin shiga mai kyau da Kamala kamar masu zuwa Wani event, Rasheeda ta tambayi inda za a je yafi sau ba adadi ba wanda ya kula ta, haka suka d'au hanya, ana tafiya ta gane ina za a ta ja tsaki da qarfi da yasa kowa kallon ta,

"Da ace min gidan gyatumin nawa za a ake ganin asarar hakan Allah ya kyauta to,"

Ko ci kan ki ba wanda ya ce mata, suna isa suka tadda wata jibgegiyar mota me numfashi a qofar gate d'in gidan, kowa sake baki ya yi yana kallon motar musamman Rasheedah da ta dinga zuba santin motar, suna tsayawa Auwal ya fito, shima Adnan ya fita daga cikin motar da taimakon driver ta hanyar bud'e masa motar ya tsaya a gefe Suna wa juna murmushi, dan tinda yazo gidan suke a tsaye a nan saboda ya rasa ta ina zai fara sa qafa ya shiga cikin gidan, kallon shi su Afrah suke, Yousuf kam tabbas ya san wannan shine Daddy, Auwal kam hawayen dad'in ganin Adnan ne suka wanke masa fuska, shima Adnan d'in haka,Rasheedah da ta fito daga baya tana mitar tsaiwar me suke, tana ganin Adnan d'in kusan zama ta yi a qasa a wajen, Afrah da Sulaiman ne suka taro ta,

Cikin wata iriyar murya me rawa ta ce,

"Waaa nake gani haka kamar Adnan?"

Cike da jin d'acin labaran da ya ji daga mutanen shi ya kalle ta,ya kauda kai, ya kalli Auwal ya taka ya rungume shi, shima qanqame shi ya yi kamar wanda aka ce wa zai sake komawa inda ya fito,yaran ma rungume shi suka yi,banda Afrah da ke gefe hawaye na ta zarya a idon ta, dama wannan shi ne Daddy kenan? Shine abinda take ayyanawa a ranta, me zai sa ya tafi ya bar Atiyyaerh, ta sha wahala wajen Umman su? Bayan da ga dukkan alama yana cikin rufin asiri, kauda kai ta yi ta shige gidan da gudu, dan in Atiyyaerh bata yafe masa ba itama bazai ga fara'ar ta ba, a ranshi ya tabbatar da labarin da yaji game da shaquwar Atiyyaerh da Afrah, jikin shi ya yi sanyi sosai da ganin hakan, ya tabbata akwai had'in kai,a tsakanin su, d'unguma suka yi ciki baki d'ayan su, har lokacin Rasheedah bata daina kallon shi ba.

Da kuka Afrah ta shiga, ta fada cinyar Atiyyaerh da take zaune ta shafa hadin Cinnamon da lemon tsami,kwai, zuma da d'an sugar kad'an a ciki ta shafe a jikin ta, tana ta danna waya,tana kallon hotunan Yayahn ta, daga ita sai qaramar riga iya guiwa, data matse ta daga sama, sannan ta sake daga qasa, mai siririn hannuwa,rigar na da aljihu a jikin ta, kalar yellow, ta daure gashin ta ta nannade shi, ta yi masifar kyau, wayar ta ta zira cikin aljihun rigar  hankalin ta tashe take tambayar Afrah me ya faru? Amma ta kasa magana, sallamar Abban su Auwal ne ta katse mata tambayar, tafe dashi akwai wani mutum mai cikar kamala, da zati wanda ta kasa tantance waye, amma zuciyar ta sai qara qarfi take wajen bugawa......

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now