KAI NE JARUMI PAGE 31

39 4 2
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼

        

WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH


*Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️*

*Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal*


Page 31:

Mama ce ta fito  daga d'akin su Abbah na biye da ita a baya, tana neman Atiyyaerh dan ta raba masu musun da suke akan kwanan wata,

" ke zo ki raba mana wannan gaddamar, yau nawa ga watan bat......."

Dakatawa ta yi da zancen ta,dariyar Abbah ce ta d'auke lokaci d'aya mamaki ya maye gurbin ta,

"ADNAN"

Suka had'a baki wajen fad'a,Juyawa Adnan ya yi daga barin kallon Atiyyaerh ya Maida idon shi Kan dattijan guda biyu, Cike da tsananin farin ciki ya tafi wajen Abbah da Mama da idanun su suka ciko da kwallar farin ciki,rungume Abbah ya yi, ya fashe da kukan murna, Abbah ma kyakkyawar runguma ya Masa ya na bubbuga bayan shi,bakin Mama ya qi rufuwa saboda farin ciki,

"Shekara 19 kenan rabon mu da Sanya ka a idanun mu Adnan sai yau Allah ya yi zamu sake saka a idon mu, ya ilahi kullum tinani na baya wuce Allah kar yasa na mutu ban sake ganin ka ba, mu nemi yafiyar ka akan sakaci da kuma cika wasiyyar da bata zamo alkhairi ba, dan babu abinda Atiyyaerh ta tsinta wajen Rasheedah sai uquba da bala'i gashi ita wadda aka yi domin ta har yau Imani da tsoron Allah da son zumunci be shiga zuciyar ta ba,a qoqarin cika wannan wasiyya Adnan mun zalunci marainiyar Allah,ka yafe mana Adnan, ka yafe mana,"

Kuka ne ya ci qarfin Mama a dole ta yi shiru da maganganun da take ta zubawa, Abbah ne ya samu waje a kujera ya zaunar da ita, yana lallashin ta, don yasan kusan kullum sai ta yi kuka akan hakan , ko yana gida ko ya fita,

"Mama ni ne zan nemi yafiyar ku, ku yi hakuri da saku cikin kewa da tinani da na yi, inshaa Allah na dawo gare ku kuma na dawo wajen 'yata ba abinda zai sake rabamu da ku, ina fatan kun yafe min?" Atiyyaerh ce ta ke bin shi da Wani irin kallo, cikin qasa da murya ta fara magana,

" Yafiya? Yafiya fa kace Daddy? All this years? What have you been doing that is so important da ya sa ka yi abandoning din mu? u ar there leading a luxery life, ni ina nan ina azabtuwa, kamar marainiya mara gata, mara galihu, mara dangi, sai mariqiyar da ta min riqo kamar bamu had'a jini da ita ba,me na muku, kullum na tina halin dana shiga ni d'aya ji nake kamar zuciya ta zata fashe ta tarwatse, Umma bata riqe amana ba, bata riqe zumunci ba, Mummy ta yi zaton zata iya canja mata halaye idan ta bata ni, bata san kuskure ta tafka ba, ta azabtar dani, ta azabtar dani, ta azabtar dani, ta min auren da bana so,na koma bazawara, na had'iyi baqin ciki irin Wanda in aka wa mutum auren da baya so ya yi hakuri ya danne domin biyayyar Allah da ta iyaye ya d'and'ana,Yan zu Kuma Ina had'iyar baqin cikin rabuwa da mutanen da na Saba da son su, saboda son zuciya irin nata, su nake gani na ji ina da iyaye, domin sun d'auke ni a matsayin d'iyar su ta cikin su, ba suruka ba, Ahmad ya gwadan soyayya mai tsanani da kulawa, kowa nawa ya gujen har ba a so a zo wajena, na San a lokacin nan dik uzirin da mama ke bani na rashin lafiya da ta so zuwa waje na a mota za a kawo ta ta zo ta ganni, amma har na gama rayuwa da Ahmad bata San ya d'aki na yake ba, na yi hakuri na shanye, hakan ta faru ne saboda ita ta dalilin ki ne Umma ke ce silar komai, ke ce silar shiga ta matsala da damuwa a rayuwa, habaaa ba zuciya a qirji na ne? Kar ku Yi zaton bana Jin zafi da radad'in yada ni da kuka yi, na zab'i na Maida komai baya na ne Dan kwanciyar hankalin kaina, amma ba Dan na manta ba,su kan su 'yan uwana da ke so na da Abbana da ke so na sai dai na ga soyayyar su daga nesa amma ba za a nuna min soyayyar ba yanda zan ji dad'i na San yess ana so na, Afrah ce kad'ai ke take duk wata doka ta nuna min so, me na aikata mara kyau? Me yasa ku ke tsoron ta ku ke kyale ta har ta ke abinda ta ga dama, ba zan tab'a yafe miki ba Ummaa, ba zan yafe ba, ba zan yafe ba, dan haka kar Wanda ya nemi yafiya ta,"

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now