KAI NE JARUMI PAGE 14

26 2 1
                                    

💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼


WRITTEN  BY HAERMREBRAERH




Page 14:






Suna nan zaune zuru zuru har rana ta take, hatta da abincin da Shamsiyya ta kawo ita da drivern Adnan ba Wanda ya Iya tabawa balle a ci,haka ta hakura ta tafi ta bar musu abincin tare da fatan Allah ya ba wa uwar d'akin nasu lafiya.

Mama ta yi wa Rasheedah waya yafi sau biyar kenan, amma shiru kk ji har wannan lokacin bata je ba,yanda take amsa wayar ma ya nuna ko alamar son zuwa ma bata da shi, kiran Auwal Mama ta yi daga qarshe ta sanar da shi rashin lafiyar Sakeenaah , nan take hankalin shi ya tashi, ya yi masu alqawarin zuwa shi da Rasheedah, lokacin daya same ta tana ma Sulaiman wanka ta gama yi wa Afrahn ta wanka ta goya ta, had'e fuska ta yi dan Jin me yake Sanar da ita, cikin tura baki ta ce,

"kai ni fa ban son zuwa na ga yanda suke wannan tarairayar tata kamar wani k'wai, ai Ina nan na yi mata addu'a Allah ya bata lfy, ya tada kafadun ta ba sai na je ba,ai ko dan wanan yarinyar ta ta ma zata tashi ne,"

Mamaki ne ya kama Auwal da tsananin tsoron halayyar Rasheedah, b'ata rai ya yi sosai sanan yace,

"Da na fad'a maki a tunani na zan ga kin fini shiga damuwa game da halin da take ciki saboda alaqar dake tsakanin ku ta jini qanwar ki ce fa Rasheedah uwa d'aya uba d'aya, na zaci zaki fini damuwa, amma yanzu tinda ta zama qanwata ba taki ba, ina mai baki umarni ne da ki shirya ki je duba ta sakarar banza kawai wawuya, ko ni ke da yarinya kamar Sakeenaah dole na tarairaye ta na nuna mata so da qauna,in ko ina da kamar ki kuwa, binne ki zan na b'oye sokuwa kawai, ki qara minti goma a gidan nan Baki wuce ba ki gani,"

ya sa kai ya fice dan zuwa asibitin, tsaki ta yi me tsaho irin na marasa mutuncin nan tare da ci gaba da mita, akan me zai matsa mata se ta je bayan iyayen su da ke lelen ta na wajen ta San baqin ciki kawai zata shaqa musamman wajen Adnan d'innan me tsinannen iyayi, ji yake kamar duk duniya ya fi kowa son Sakeenaah.

********************************

A hankali ta fara bud'e idanun ta da suka mata nauyi,ji tayi Kan ta ya mata nauyi da girma kamar wani qaton dutse aka ɗora mata a kan nata,yatsun ta na hannu ta fara motsawa a hankali,dik abinnan da take akan idon Adnan da  ya kasa ya tsare take yin shi, rudewa ya yi da murna, sai ya d'aga hannayen shi sama yana hamdala ga ubangiji, fita ya yi ya kira Doc., Likitan na gama duba ta ya qara mata allurai na magunguna a qarin ruwan da ke bin jikin ta, ya cire ledar da aka d'aura  mata na qarin jini dan ya qare, se ya miqa wa Adnan hannu ya taya shi murnar regaining conscious din ta da ta yi, sannan ya sanar da su kar a takura mata da hayaniya, ko wani abu da zai tada hankalin ta,in Allah ya yarda sauqi zai dinga samuwa a hankali,Doc ya ci gaba da cewa Adnan,

"Ni na hana mutanen gida zuwa duba ku jiyan saboda halin da take ciki kar a yi ta hayaniya zuwa yamma zan Sanar da su Suna Iya zuwa gobe Allah ya qara mata lafiya, ka qara daurewa d'an uwa"

"Na gode sosai qani na Allah ya qara d'aukaka ka, in ka je ka ce wa Baffa ya zo ya ga surukar shi ya mata addu'o'in shi da ya ke mana masu tasiri a rayuwar mu ko Allah zai duba ta ya bata lafiya"

"Kar ka damu d'an uwa  Allah zai bata lafiya"

Likita na fita Auwal ya shiga asibitin, da tambayar nurses da ma'aikatan wajen ya gano d'akin da su Sakeenah suke, Mama da ta hango shi shi kad'ai ba Rasheedah sai ta qissima a ran ta waccan rasan ba zuwa zata yi ba da alama, lallai kuwa in haka ta kasance qiyayyar da take ma Sakeenaah babba ce, abun na matuqar damun ta, dole Sakeenaah ta saka abun a rai matuqa, akan dalilin banza na hassada ya sa ta tsani qanwar ta uwa daya uba daya? Kaiiii Allah ya shirya mata wannan yarinya.

Shi yasa aka ce hassada mugun ciwo/babban ciwo, in mutum na da cutar hassada lamarin shi ba qaramin lamari ba ne sai dai a bi shi da addu'a Dan kuwa Yana Iya aikata komai Dan ya kawar da abinda yake hassada akai, ko da hannun shi ko da mugun bakin shi, Allah ya mana tsari da ciwon hassada.

KAI NE JARUMIWhere stories live. Discover now