💅🏼 KAI NE JARUMI 💅
Page 20:
Tin daga wannan ranar, ko hanya ce ta biyo da Atiyyaerh ta inda Rasheedah take sai dai ta bar wajen da kuka, danko sai ta mata wani abun muguntar da zai saka ta kuka, kullum Yousuf dayasanin fad'a ma mahaifin shi abinda ya faru yake, sannan ya qudurta a ranshi sai ya kama Ahmad ya baje qarfin shi akan shi, tinda shine silar abinda yake faruwa da Ablaerhn shi .
Kwance take a d'akin su bayan sun dawo daga islamiyya, ko kayan ta ta kasa cirewa, ashe da empty lunch box ta tafi ranar, sai da ta je zata ci abinci taga wayam, gashi da safe iya tea ta sha, tea din ma ba wani had'in kirki aka masa ba, Auwal tin da ya kula the more yana shiga harkar su the more Rasheedah na qara haukacewa da musgunawa yarinyar sai ya ja baya da shiga lamarin nasu,saboda ya kula idan zai jinyata Rasheedah ne akan Atiyyaerh da ta samu dama sai ta ninka abinda ya mata akan yarinyar,kawai sai ya koma yi mata addu'ar shiriya,dan haka lokuta da dama yana ji Kuma ya na ganin ta tana mata mugunta amma haka zai kasa tanka mata,yau har ya tashi zai Saka wa Atiyyaerh extra cake a jaka sai ya ga ta saka mata lunch box a jakar sai ya fasa aiwatar da qudirin shi,hakan kuwa shi bahaushe ke Kira da rashin sani ya fi dare duhu dan kuwa ba komai a cikin lunch box d'in,ko da suka dawo Atiyyaerh ta tambayi abinci Rasheedah ce mata ta yi ta je d'aki ta cire kaya tazo su ci da 'yan uwan ta, tana shiga ta biyo ta d'akin, tace in ta sake ta koma parlourn sai ta ji a jikin ta,ta zauna har sai ta kira ta, su Yousuf basu gane komai ba, suka zauna jiran ta,
" Afrah ku ci abinci mana ko kun cinye akwai da yawa a kitchen zan qara maku na zuba mata wani, maza kuci,"
Fara ci suka yi, amma Yousuf kwata2 bai jin dad'in ci ba tare da Atiyyaerh ba, a haka ya tura suna gamawa tace su je daki su yi wanka, su huta kafin lokacin islamiyya ya yi,'yan mazan tashi suka yi suka tafi d'akin su, Afrah ma ta nufi d'akin su ita da Atiyyaerh, se ta ga Atiyyaerh kwance tana kuka, ta riqe ciki, yunwa duk ta gama rarake mata ciki, Afrah ce ta je ta zauna a gefen ta ta tambaye ta meye, cikin kuka ta fad'a mata yunwa take ji,
" Umma tace mu cinye zata zuba maki wani,ki je ki ci naki a wajen Umma"
Cikin jin dad'i da kuma tsoron me zai je ya zo Atiyyaerh ta miqe ta fita, zaune ta ganta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya ta na kad'a ta, rara gefe ta fara cikin sanyin jiki da murya tace,
" Umma yunwa nake ji, kamar zan mutu,"
" Laaaaa kaji munafukar yarinya,yanzu ke a ina kk san mutuwa? Iyyeee, waya fada maki ana mutuwa in an ji yunwa, wahala kawai zaki sha ba zaki mutu ba in ma tsoron mutuwa kk kar ki bi uwale, matsa ki ban waje munafuka ki je ki shirya, ki saka kayan ki,na islamiyya lokaci ya kusa,"
"Umma abincin fa? Yunwa nake ji yau ban ci abinci ba fa"
"Dan uban ki Adnanu ba Zaki bar nan wajen ba se na b'ab'b'alla ki? Dan munafurci salon Wani ya ji a ce bana baki abinci ko? Kin b'ace min da gani ko se na mammake ki?"
Tini hawaye ya gama wanke fuskar Atiyyaerh, hankalin ta a matuqar tashe, dan ba qaramin yunwa take ji ba, haka ta koma d'akin,ta fara saka kayan ta na islamiyya, tana sharce hawaye, Afrah ma kukan ne ya kama ta, dan ta ji komai, haka suka gama shiri suka fita, Afrah ce ta gaya ma Yousuf komai, hankalin shi ya tashi sosai da jin haka, gaba d'aya tausayin qanwar tashi ya gama lausasa zuciyar shi,dan bai san ya zai ya bata a binci ba tare da Umman su ta gane ba, dabara ce ta fado masa,yace su yi gaba zai taho.
Sallama ya yi ya shiga gidan ya riqe ciki, da gudu ya yi band'aki, ta bi shi,"Yousuf lfy? Meya same ka? Ko gudawa kk ne?"
" Eh Umma, inna fito zan bi kitchen na sha magani na koma makaranta,"
"To Allah ya sawaqa, ni nayi d'aki ka tabbatar ka ja min qofa sosai kan ka fita,"
" To Umma"
Murmushi ya yi, bayan ta haye sama da dan mintuna kamar biyar ya fito ya yi kitchen ya nemo leda, ya d'ebi abinci, da ruwa a roba, ya d'au maganin gudawa ya fice da gudu, Atiyyaerh ta jingina a jikin windon ajin su tana hawaye tana kallon waje yunwa take ji ba ta wasa ba,can ta hango Yousuf na gudu, da leda a hannun shi, mamaki ne ya ishe ta,bata gama tambayar kanta meye a ciki ba ta ga ya shiga ajin su yana neman izinin an aiko shi wajen Atiyyaerh dan ta taho bata ci abinci ba aka ce ya kawo mata,
YOU ARE READING
KAI NE JARUMI
RomanceTalauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....