RAINA(The beautiful princess) Babi na Daya

4.7K 201 8
                                    

*1-5*               *RAINA*
*(The beautiful princess)*

©
*HUMAIRAH (melody)*

*Alhamdulillah rabbil alamin nagode Allah mai kowa mai komai daya bani ikon dawowa dawani taska wacce nake fatan Allah yabani ikon idar da wannan sako banyi don cin zarafi ga kowa ba koh batanci ga kowa ba Allah yasa mu amfana da juna Amin.*

         _INA KAUNARKU_
*UMMU SABREENA*
*FIRDAUSI SODANGI*
*ANEESA A RIMI*
*LUBBIE MTFSR*
*AUNTY SIS*💞
*SERDEYERH*😘

         _KUNA RAINA_
*ABEEDA*
*MARDIA NIJAR*
*SARAH*
*ZAINAB DUBAI*
*MISS XOXO*
*FATTY AZLAND*
*HAULERT SKT*
*MARYAM M SADI*
*FATTY NASHUKA*
*MIENERH HAMIDAN*

_JINJINA GA FAMILY AND FRIENDS_

   *YARA MANYAN GOBE SADIQ & FARUK(Twins)*
*MUHAMMAD*
*AMINA MAID*
*SAIF KT*
*AHMAD MS*
*SUHAILA*
*BEAUTY BOMO*

  _SANYIN IDANUNA MUSTAPHA (Abba)_

  *IYAYENA DR MB SHEHU DA HJY MALAMA DIJE WADA MANZO LOVING YOU IS MY PORTION MAY ALLAH BE WITH YOU FOR EVER AN EVER AMIN.*



_Bismillahir rahmanir rahim......_

*BABI NA DAYA*

     Dan sarki ne magajin sarki duk Dan bakin ciki saidai ya mutu babu wata mata cikin gidannan dazata fini rawan gaban hantsi kuda haihuwa sai dai kuji a makota badai cikin gidannan ba ehe duk me magana tafito ina dai-dai da kowacce bora,

     Wata matace yar k'arama sanye da alkyabba rikeda jariri a hannu dabai wuci wata biyar zuwa shida ba matar daganinta batada kunya babu sauran mutunci a fuskarka koh imani, Gimbiya Maimuna ce tafito tafiya take cikeda SARAUTA babu Wanda zai ganta bai kara kallonta ba saboda tsabar kyau kaman zai zube.

        “Maryam ke baki isa ki kirani bora ba wallahi kinyi tsururu, me akeda agola kowa acikin masarautar nan yasan cewa badan sarki bane saidai idan kin zama shawo maida Dan wani naka yau koh mutuwa sarki yafadi yayi bashi da gado kinga koh sai kisawa kanki salama da kwanciyan hankali” Duk cikin matan dake cikin gidan babu wacce ta iya tofa wani abu sai Maimuna wacce tasha SARAUTA ta koshi gabanta da bayanta.

     Haka suka gama cece kucensu kowacce tashige sashenta.

Maryam ce tsaye cikin falo ga kuyanginta sun zagayeta kowacce tana tarairayanta ta koh ina

    *Danish* kuwa sai tsala ihu yakeyi hankalinta yayi matukar tashi tarasa abunda yakeda buk'ata binta ce ta russuna cikin ladabi tace
“ranki yadade mai zai hana kibani rainon yarima ko kya samu ki huta”

Dariya maryam tayi.

     “Gashi binta nabaki amanarsa cinsa shansa duk nabaki ragamar komai sannan na baki wancan b'angaren kizauna aciki daga ke sai yarima don naga kina jidashi takowani fanni, daga ranan danish ya koma hannun Binta saboda tsabar kaunarsa Data keyi.

Sarki *MAMUDA* ne yashiga inda danish yake yana yimishi wasa cikin dabara shiko sai dariya yakeyi, yana bangale baki Hajiya Maimuna ce tsaye tana kallonsa, tuni taji takasa controlling kanta hawaye kawai yake ambaliya a idanunta.

“Tabbas mai martaba kana bukatan ganin k'wanka aduniya saboda nasan duk wani ikoh da MULKI na maryam zai ragu saboda dole mai martaba ya raba son da yakema danish gida BIYU.

   Maryam ce tazo wucewa taga Maimuna a tsaye a taga tana kaiwa da komowa dafata tayi tare da cewa.

     “Allah sarki juya aci ai kashi ki kwantar da hankalinki danish yariga zuwa duniya kuma babu yadda zaki iya da ikon Allah saboda shine yarima mai jiran gado koda SARAUTA saida MULKI” wucewa tayi tunkafin Maimuna ta lalubo amsar dazata bata amma ina kafin duk wani kalami ya shiryu Maryam tayi gaba.

              ******

*BAYAN SHEKARA GOMA*

     Ana cikin takun sak'a da maryam da Maimuna.

      K'watsam ciki ya baiyana ajikin Maimuna tuni jakadiyar sarki tayi fadan sarki aguje danta sanar dashi Abun farin ciki abunda ya dad'e yana nema ruwa ajallo ido rufe,

   Tana shiga fada ta zube a k'asa ta kwashi gaisuwa tace

   “Ranka ya dad'e gimbiya kuma sarauniya Maimuna tana dauke da juna biyu a gwaje gwajen da akayi likita yace cikine da ita”Farincikinsa yakasa boyuwa tuni yace,

     “Kibi sasa sasa ki shelanta ma kowa cewa yar sarki jikar sarki matar sarki mamuda tana daukeda juna biyu sannan duk wata bukata ta duniya jakadiya na biya miki likita nabashi kyautar mota da kujeran makka” jakadiya tace
“Godiya nake Allah yakara Nisan Kwana Allah yakara ma sarki lafya da karama takawarka lafya rijiya ba wajen wasan yara bane kafara dai”

     Haka jakadiya tagama kirarinta tayi waje guda kawai takeyi,

       Tayi yakaina tsawon minti goma bayi da kuyangu duk aka fito matan sarki koh an kasa kunne Duk sun baza kunnuwa jakadiya tayi kirari tayi kirari, kowa ya zak'u dajin abunda zata fada, Maryam kuwa tanajin gud'a tuni ta kasa zaune tak'asa tsaye takai gauro takai mari gabanta sai faduwa yakeyi dukda murnan saukan Al'quranin danta Danish, tuni fuskarta ta sauya zuwa akasin haka.


*_MELODY_*😍
Inafatsn zakuji dadin kasancewa dani cikin sabon littafina sannan inafatan zakiyi like sannan muyi comment don Karin karfin gwiwa Ngd HUMAIRAH bashir melody.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now