RAINA (The beautiful princess) BABI NA SHA BIYAR

1K 45 1
                                    

*66-70* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA BIYAR

         ★★★
BAYAN WATA BAKWAI

Raina ce tafito aguje tafada b'agirarran ban dakinsu tanata k'warai amai kamar wacce yan hanji zasu fito Goggo dai tsaye tayi tana ganin ikon Allah meyake shirin faruwa dasu
Fitowan Raina ne Goggo taga tayi wani mugun fari goshinta sai kyalli yakeyi riketa tayi suka zauna tace
“Raina lafya kike kuwa kodai ciki gareki?”
“Idanma cikine inna ai basaikin tambayi inda na rakito shiba koh?”
Inna tace
“Watanki nawa bakiga jinin al'adan kiba?”
Raina ta tabe baki ta cije tayi far da ido
“Goggo kusan wata bakwai kenan banayi kwata kwata koh digo kuma sai inji nauyi a cikina gashi zazzabi nakeyi da dare”
Goggo tayi salati tasanarda uban giji tace wannan wane irin kurman cikine?
Toh yanzu zaibar duniya yanzu zan burgeshi ai abun gorin sai yayi yawa
“Goggo babu inda zaki burgemun ciki haka kawai meyasa kafin ki haifeni baki burgeni ba kika barni ina rayuwa adoron kasa toh shima wannan cikin inaso kibarmun abuna in haifa ai babu Wanda baida uba kuma nasan ubansa haihuwa kamar nayi saidai idan yazo duniya ki maidashi yadda bakiji kunyan yin cikina ba haka nima bakaina farau ba kuma ba kaina karau ba”
Kwaf kakeji Goggo ta bige mata baki
“Toh kisani koh kinaso koh bakiso sai na zubar dashi”
Daki tashiga ta hado abubuwa da dama cikin kwanon sha taba RAINA dole tasha cikin mintuna Raina tafara juyi kamar zata mutu chan saiga jini ya balle Tuni raina ta daina motsi Goggo ta rude a dagudu tayi makota, Allah yaso mijinsu yanada mota aka dauketa sai Asibiti Zangon kyauta, nan aka shiga da ita emergency akayi mata taimako Goggo sai muzurai takeyi kamar wacce tayi karya, likita ne yafito yace
“Waye mijin wannan yarinyar?”
Malam Musa yace
“Likita batada miji budurwace fah”
“Kace budurwace toh waye yayi mata ciki shi muke nema” nan Goggo taji kamarta nutse ga matan Malam Musa ai kowa saiya koma yar kallon kallo.

Nan akace hantarta tasamu matsala sanadiyyan maganin datasha na gargajiya, sai anyi mata aiki ai Tuni Malam Musa da matansa suka bar asibitin haka Goggo tadinga tumami tana kuka maicin rai da zuciya, likita yace
“Baba hakuri zakiyi wannan yariga yafaru kisamo kudi muddin kinaso yarki ta rayu” haka aka kwana biyu kwatsam saiga Fu'ad acikin Asibiti shida Idi ai Goggo wani kunya taji haka Fu'ad yabiya musu komai harda raran dubu Dari sannan yayi mata fatan samum sauki suka wuce, Anyi aiki RAINA tayi garas, kwanansu ashirin da hudu aka sallamesu garine yacika tundaga shigowarsu,
“Inna lafya naga gari yacika kodai mutuwa akayi koh sarki ya kara dawowa ne?”Goggo tace wane irin sarki kuma mexaizo yayi?
Wani suka tambaya akace musu Fu'ad ne Dan gidan mai gari yake aure RAINA tayi saurin cewa
“Kana nufin Fu'ad ne yake aure wacece ya aura? ”
Yaron yace
“Sadiya ya aura yar gidan lanti mai kwakumeti yau zasu wuce Kasar India ma don naji ance achan yake aiki”
Ai jinkin ta kaura yayi la'asar Ni HUMAIRAH nasan Fu'ad baxai auri RAINA ba saboda sun cutar dashi sun kasa gane cewa Allah shike azurta bawa sun manta cewa Allah ke fidda shugabsn k'asa daga mahaifar uwarsa, sun kasa gane cewa bawa da arzikinsa yake zuwa duniya, gida suka wuce cikeda kakabi haka Raina ta rame ta kanjame har cewa ake cutar zamani gareta, duk suka dode kunnensu.

★★★
BAYAN WATA DAYA

Da asuba aka doka uban sallama goggo ta fita taga mai gari tsaye shida mutanensa “Sannun Ku ”
“Dakata tsohuwar kilaki wakika maida yaro acikin garinnan babu yar data taba cikin shege sai yarki toh kisani zaman ki a garinnan ya kare karuwar banza karuwar wofi makira addababba kawai nabaki awa ashirin da hudu kibar gidannan idan ko kikaki sainasa anyi holi daku, kafa kafa muka taimakeki muka baki gurin zama amma kingawo mana annoba zata bata mana tarbiyan yaya, tsohuwar yar bariki toh ki kara gaba ”
Raina dake bayan Goggo dukta gama jin abunda mai gari yafada ta kutsa ta tsaya a gaba cikeda tsiwa da tashanci tayi guda tace
“Tafi nono fari maigari baka burgeni ba dakace awa ashirin da hudu naso kace yanzu Mu tattara yanamu yanamu da sai ince koh zaka tayamu daukan gidan, don nasan siya mukayi da kudi toh kasani in kaga munbar garinnan sai munsamu mai siyan gidan an bamu kudi kannan mutafi,
Dakake kirana shegiya naji labari matarka itama yar k'wararo ce don haka karka cire rai da sumun shege koh shegiya, duk mai zagin Dan wani shima saiyaga jarabawa, Maigari adinga Sara ana duban bakin gatari, wannan Abu tamkar saukar malkade muna jira ayiwa gida kudi Mu kara gaba” tsaki RAINA taja tace
“Goggo Mu shiga daka ciki”

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now