RAINA(The beautiful princess) Babi Na Biyu

1.9K 103 0
                                    

*6-10        RAINA*
*(The beautiful princess)*

               *_BY_*

© *HUMAIRAH (Melody)*

*BABI NA BIYU*
   

       Jakadiya tace

     “Mun samu k'aruwa acikin gidan nan gimbiya kuma sarauniya maimunatu tana daukeda juna biyu ance in shelanta Sarki yace a tayashi farinciki Ashe yanada rabon ganin k'wansa a duniya,

   Ras gaban Maryam ya yanke yafad'i takasa zaune ta kasa tsaye kowa Na murna amma banda ita har bak'in ciki take nunawa a fili bata b'oyewa saboda rashin tunani,

     Haka ake rainon cikin cikeda kulawa lokaci guda Maimuna tazama wata katuwa Abu abinda ba'a girka mata daga zogale, rama, lansir Dan gauda duk abunda tace haka jiki ke rawa za'ayi mata.
Safiyar lahadi ne mai martaba yashirya zuwa kilisa kamar yadda yasaba a bayan gari,

    Haka kowacce tafito take yimasa adawo lafya ciki harda Maimuna Wanda ciki yafito yayi titsitsi.

    Dubansa yakai gareta yana mai yalwata murmushin sa yace “Ki kulada kanki da abunda ke cikinki ki kwanta ki huta don yanzu ke yar hutu ce Indai *SARAUTA* ce kin gada,”

    Charaf Maryam tace.

    " *MULKI* kuma shi muka gada saidai akaimu bola”

   Dariya yayi don yasan halin Maryam saboda mugun kishin datake da maimunatu saboda ita ke bimata,
Jakadiyace tace,

 
     “Uwar gida yakamata kidinga motsa jiki kin Dan zagayawa koh zaki dinga samun kuzari”
dariya tayi tace

           “toh”

    Tafiya take itada kuyanginta suna zagaye suna bata labari mai sanyaya zuciya sai dariya takeyi,

         Maryam dake d'aki tasa Danish ya ruga da gudu ya tokari cikin ya zube haka ya rugo tuni kuyanginta suka tareshi sukace,

     “Ranka ya dad'e yarima lafya waya biyoka da gudu ”?

  saboda gaskiyarsa yace,

       “Mum ce tace inzo da gudu in bige miki ciki kuma Na gayamata ni inason ki haifamun kani yadda zamu dinga kilisa tare”

    Tab'e baki yayi kamar zaiyi kuka.

    Maimuna ta kalleshi saboda yarima Danish yashiga ranta tun ranan dayazo duniya taji sonsa ya mamaye mata ilahirin zuciya ko d'an bata haifa bane Allah kadai yasani,
    

       “Karka damu danish kazama yaro mai gaskiya da rikon amana sannan kazama mai tausayi saboda Allah yanason mutane masu tausayi da imani,

    Ji tayi kamar daga sama ance,

    “Wane hud'ubar akewa d'ana?

    Fisgan danish tayi tana huci karki sake koda wasa ki sake tabamun da saboda ba tsaran abunda zaki Haifa bane wayasani koh cikin bayi kika samu wani yayi miki ciki kikace Na mai martaba ne?
Maimunatu tayi dariya Wanda yake bak'anta ran Maryam

“Allah kadai yasan uwar kwaddo”

   Tana gama magana tayiwa kuyanginta magana suka ci gaba da tafiya suna shewa suna dariya,

   Maryam ta mace a tsaye dole tace

      “In samu mafita akan wannan cikin saboda banaso tazo duniya da rai koda tazo da rai saina San yadda nayi aka fitarmun da ita daga cikin gidannan”

tana juyowa taga binta tsaye ta rike haba tace,
   
    “Uwar dakina meyasa kike damun kanki? Maiyasa kike tada hankalinki akan waccan abun hmmm tunda ki keda Binta saina share miki hawaye duk wani makirci daya kwana ya hantse nasan shi wani darene jemage bai ganiba?”maryam tace Daren haihuwarsa.

Anata shirye shiryen saukar danish gida yayi tankam da mutane haka akayi saukar aka gama washe gari aka wuceda Danish k'asar madina inda acan zaiyi karatunsa daga sakandiri har jami'a, nan akabar Maryam da kewa hakan yakara bata daman shirya magun abunta dabazai kaita ga komai ba sai halaka

       Haka suka dinga k'ullawa suna k'wancewa itada kuyangarta binta suna cikin zancenne jakadiya taji komai ta kulle a hab'ar zaninta, ranan da watan haihuwar Maimuna ya tsaya sune gaba gaba wajen zuwa clinic din cikin gidan, inda aka kira likitan bayan  ta haihu ne aka samo matacciyar ya mace akasa mata tuni binta ta Goya yar ta gudu da ita koh wanketa ba'ayi ba.

      Haka aka sanar da maimartaba wannan mummunan labarin amma tuni jakadiya ta karbe tace karya akeyi tuni ta kwashe komai tafadi,

      Inda mai martaba yashiga cikin rud'ani don zan iya cewa harda kuka saida yayi kowa Na gidan yayi kuka tuni aka kama Maryam da dakta akayi wani akurki dasu inda a k'aidar al'ada duk Wanda aka damk'a da laifi nan ake kaishi koda mai girman muk'ami ne a masa rautan,

    Rayuwa tayi musu kunci amma suka fawwalawa Allah komai.


*_MELODY_*😍

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now