RAINA (,the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

978 37 0
                                    

*131-135* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_


BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI









“Kiyi Hakuri Raina nasan kina cikin rudani nasan kina cikin matsanancin damuwa na Rashin Adalci dana nuna miki tun zuwanki cikin gidannan nayi hakanne saboda wani kunci dake dawainiya Dani, amma naji matukar dadi dakika zo inda nake hakan yanuna cewa kemai kaunar uwar data kawoki duniya, dakwai wata magana mai matukar muhimmanci Wanda nakeso inyi dake Ansa ranan aurenki nanda sati biyu keda dan'uwanki DANISH amma kisani yanada mata mai Suna Unaiza tana zaune acikin garin Kaduna ne” Ras RAINA taji gabanta yayi mummunan faduwa taji duniya ta tsani Danish Wanda shima take ganin alaman ya tsaneta budar bakinta tace
“Ummi A gaskiya banida raayin yin wani aure saboda nayi banji da dadi ba sannan Danish bayasona saboda babu wata magana data taba hadani dashi koda cikin Garden na shiga saiya watsamun kallon tsana yabar wajen Dan'uwanka mai sonka kuwa Janka zaiyi a jiki ganin yafaranta maka rai amma duk abunda kuka yanke a shrye nake da inyi muku biyayya a matsayin iyayena” Maimuna taji dadi tabbas da ace RAINA a gabana ta tashi nasan data zama abun kwatance saboda daga dukkan alamu tanada ladabi da biyayya.

Nan sukayita hira amma koda wasa RAINA bata taba fadin tanada yara har biyu ba rayuwa ta sauya RAINA taxama yar gari takan fita domin shakatawa tana samun kulawa daga mahaifinta sosai haka mahaifiyarta, kwatsam hanya tabiyo da ita ta wani labi dake cikin gidan kawai batayi auneba taci karo da mutum dagowan daxatayi taji an dauketa da mari, Agigice ta dago ganin Danish ne itama ta daukeshi da gigitaccen Mari Wanda saida taga taurari sannan RAINA tace
“Kul agolan gida kabi a sannu don karkaga kanka na rawa kayi tsammanin kafi yar masu gida iko da mallaka kul Dan mulki wannan yar saurautace a gabanka, Uwata yar sarki jikan sarkice kuma matar sarki uwar Gimbiya RAINA Idan ka mance in tuna maka yau shine rana na karshe dazaka sa wayannan doyan hannun naka ka mareni Ina umurtanka daka bani hanya kafin inbaka kunya” tsayawa yayi ya rike kunci yana mamaki RAINA yar karamar yarinyar dayaba shekara goma bangajeshi tayi ta wuce tana wasa dayan yatsunta, bangarenta ta wuce tafada kan royal bed dinta ta fada kogin tunani
“Dole inyi biyayyar aure Idan harna Auri Danish tabbas gwarzon namiji ne maijida kansa kyakkyawa ne ajin karshe ohhhh toh niwai meyasa Abbi ya zabamun Danish a matsayin miji da gudarin tunani ne bacci yayi awon gaba da ita, misalin karfe hudu ta farka  Sallah kawai tayi akayi sallama cewa malaminta yazo mai koya mata duk wasu hukunce2 musulunci lokaci guda ta rikesu Kullun cikin istigfari take tana Neman gafaran ubangiji haka take sanarda Malam kan maganar aurenta.

Haka yayi mata Karin bayani akan Zaman *Istibra'i* da mace takeyi tsawon wata uku matukar tayi yawon bariki koh tayi zaman kanta sannan tana holewa da wasu maxan don haka yabata babban Sha'awaran a k'ara watannin aurenta zuwa wata uku da komai zai kammala, haka akayi bata zuwa koh ina daga gida sai gida babu wani namiji dayake zuwa inda take sai Azumi takeyi sallar dare kuwa kamar akanta aka saukar da Aya Abun gwanin ban shaawa kowa yayi mamakin Gimbiya RAINA yadda lokaci guda ta canza saidai batason raini koh nuna isa, Dayawa cikin family dinsu tsoronta akeji, Tuni aka fara nemawa RAINA gurbin karatu Wanda ake cewa yaki da jahilci Raina gata babu irin wacce bata samuba a halinda take yanzu.
*************
BAYAN WATA UKU
Komai ya daidaita Anfara shirin biki Gidajen radiyo babu inda ba'a shelanta ba,  Zainab  kuwa jin mijin ta zai kara aure kaman zatayi hauka saboda tsabar Rainin wayo irinna Danish bai sanar da itaba yace taji a gidan rediyo, Shida abokinsa ne mai suna Shureim ne suka zauna cikin wani folo dake kirada Tarazo suka aika ayi musu iso da RAINA batayi mamakiba haka ta tambaya waye akace da ita yarima Danish ne, saida tayi wanka tashirya cikin wata bakar doguwar Riga tayi mafla da gyale Green, tasa takalmi Shika Green tafito tareda rakiyar kuyanginta tana isa falon tace sukoma ciki ta kutsa kai Shureim ne kadai ya iya amsa sallamar RAINA harya kalleta shiko Danish wani garwashin tsanane ya turnukeshi babu abunda yake tunawa sai Marin data taba yimai........

RAINA (The beautiful princess)Onde histórias criam vida. Descubra agora