RAINA(the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA BIYU

941 38 0
                                    

*106-110* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_

_*This page goes toh AUNTY SIS💞 Thanks for all the love and care you hv for me am very greatful you are a QUEEN MOTHER👑 U'R different among odas Glory be to Allah may Allah continue to Guide and protect you from all Hypocrite and all Evil May you be the Shining STAR in our daddy's EYES Amin👏🏻*_LYSM😍





BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Jiki na rawa yakawo, akwana a tashi wajen Allah ba wuya, ciki sai girma yakeyi yana dad’a fitowa yayi titsitsi zama da kyar tashi da kyar amma hakan baisa sun daina rayuwar aure ba don ba haramum bane a musulunci idan kinada ciki daga randa yashiga har ranan da zaki haihu an yarda miji yayi jima'i da matarsa saidai idan shine bashida buk’ata  koh ita matar wallahu ta'ala wa'alam.
Farid sai fafutukan Neman aiki yakeyi da kwalin degree dinsa don har masters yayi k'watsam yasamu aiki Raina tayi murna da farinciki k'warai, Albashin farko farid a matarsa yak'are da dansa me shirin zuwa duniya Sannan ya saya musu kayan abinchi da sutura lokaci daya duka murmure Farida ce zaune cikin Dakin Raina tazo tayasu murna dukda Farida na gida batayi aureba, saboda duk Wanda ta kawo sai suce baimusu ba harta hak'ura, amma Kullun cikin Adu'a takeyi Allah yazaba bata da Alkhairi, haka ta yini kannan ta wuce gida.

Kwatsam wata safiyar Asabar Raina tana k'wance kan kafar mijinta yana mata tausa mugun kofa sukaji na rashin hankali Farid yace
“Raina waye wannan yake buga mana k'ofa kamar ya zautu? Raina ta tsbe baki tace
“Mijina kaje ka duba”.
Yana budewa hajiya tasallah yagani Wato mahaifiyar Farid sanye take da Atampha Super Aura mai ruwan bula ga jaka handbag tayi kyau kwarai amma fuskarta babu sauran annuri illah huci datakeyi Raina dake tsaye Farid ma tsaye yake Amma yakasa motsi bare yayi magana,
“kun kafeni da ido koh bazaku bani hanya bane in wuce?”ai tuni suka matsa tashiga ta tsaya tana karewa dakin kallo cikeda tsana
Gaisheta Farid yayi koh kallonsa batayiba Raina ta durk'usa a gabanta tace
“Sannu da zuwa hajiya kinzo lafya?”.

A fusace hajiya tasallah ta juyo ta daka mata tsawa
“Ke dallah rufemun doyin bakinki har kinada bakin gaisheni bayan kin  rabani da dana Allah wadaranki matsiya ciya kawai yar tasha” hamb'are Raina tayi batareda taga cikin ba Farid da sauri ya daga Raina
“Haba hajiya bakiga halinda take ciki bane tsohon ciki gareta kika tureta Dan Allah hajiya karkiyi sanadiyyan kashe mana da Wanda zaiyi mana Adu'a bayan ranmu”
Hajiya tasallah ta kurewa Raina kallo tabbas cikine ajikin wannan makirar,
“Raina har wani ciki gareki ? Waya miki cikin? Kina nufin jikanane? Kina nufin kinada rabo ajikin dana? Kodai cikin shegene har kinsamu k'wanciyan hankali harda daukan ciki? Toh kisani wannan cikin ba jikana bane tun wuri ki nemamai uba”
Raina ta gama rudewa dafe cikin tayi tana kallon farid da idanunsa sukayi jawur yace
“Hajiya ina rok'onki da karki sake sheganta mun da ciki nawane nida Raina Hajiya irin kwanciyan hankalin da muke ciki shugaban kasa baya ciki yadda kuka kujeni saboda Raina babu gudu kuma babuja dabaya ina tareda Matana da dana, kusani da Allah kuke jayayya shiyace Mu auri karuwai musasu a hanyar k'warai wannan yanuna cewa mutum yayi jihadi kuma ladansa dabanne”.

Hajiya ta mutu a tsaye tace
“Kasani yau zama tsakaninka da wannan jarababban yakare, keda uwarki kun taru kun lashemun da dangin maita wayasani koh mayune Ku toh kisani wannan cikin saidai kiyimai uba amma ba jinina bane, koda kasuwa zaki Haifa kin Dade baki haifaba kaska kawai kisani yau kafana kafar dana” hannu Farid ta rike ta jashi waje tace
“Mutafi”
Zare ido yayi yace
“Hajiya intafi kike nufi inbar Raina da ciki? Saidai Kiyi hak'uri matata bata fikiba amma kuma bazan iya tafiya inbarta ba” komawa Farid yayi yarike hannun raina wacce take kuka kamar Ranta zai fita tace
“Farid Dan Allah karka tafi kabarni kadubi Girman Allah ka taimakeni da rayuwar abunda ke cikina” tunu mutane aka taru kamar anacin dank'o Ummin Abrar itama hayaniya tajiyo tafito ganin Raina na kukane tasan cewa ba Lafya ikoh hajiya sai masifa takeyi
“Karuwa kawai kin mannewa  dana kin rabani dashi kisani saidai hawayenki su k'afe ko kuma suzama kogi don yawa amma Farid saiya barki dakeda shegen cikinki, woooo dakeda uwarki wayasani koh mayune”
Kara zuwa tayi taja hannun farid takaishi bakin mota tace yashiga amma Farid yak'i RAINA tace
“Farid karka tafito kabarni ka tausayawa abunda ke cikina ” dawowa yayi hajiya ta dak'atar dashi tace
“Muddin ka koma wajenta saidai kazaba koh ni koh ita ko kuma in tsine maka kabi duniya” ai Farid cik yatsaya Raina kuwa toshe baki tayi saboda kada kukan yafit.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now