RAINA( The beautiful princess) BABI NA UKU

1.7K 86 1
                                    

*11-15          RAINA*
*(The beautiful princess)*

    
               *_BY_*

© *HUMAIRAH (Melody)*

  *BABI NA UKU*

        Tun tafiyar Binta basu sake sata a idoba bare labarinta, haka Kullun iyayenta suke kukan rashinta mahaifiyar Danish kuwa tashiga tsaka mai wuya axabar yau daban nagobe daban, tundaga haihuwar Raina baa sake wata haihuwa ba, daman tun kafin tazo duniya yasa mata suna RAINA wato beautiful princess _( Kyakkyawar Gimbiya)_
kuma hakan take......

        ******
     *Tushen labarin*
        Wai sai yaushe zakiyi hankaline ne ke Kullun saina miki magana kan ki daina shigowa gida kina ihu kin mata cewa ke macece namiji aka Sani da karaji ba mace ba maza kiyi yadda nace farayi ingani, Abu gwanin ban dariya duk Wanda yaga yarinyar da ake koyawa bariki saiya rik'e baki saboda tabar mamaki yarinyace yar kimanin shekara goma da ko irgan dangi bata faraba illah iyaka Dan jiki datakeda shi,

     “Raina kalleni haka zakiyi da ido duk Wanda yakiraki sai kinyi yauki kannan zaki bashi cikin yanga” haka inna yalwa tadinga koyawa RAINA abubuwa daban daban dabarun bariki iri iri daga bisani ta daura mata mashe Wato wainar gero zuwa tashan garin Wato  zangon Mati, inda ake cinchirindo wajen kawo abun soyarwa, haka fuskar Raina taji mai sai sheki take ga wani digi digo datayi kamar wata aljana, tana tafe tana yanga harta isa runfarsu da zuwanta yara suka dinga kwashe kayansu, suna ya mutsa fuska suna cewa ke mutashi kinsan halin wannan shegiyar dabatada uba, wata tace wayasani ba koh yar tsintuwa ce? Oho sukayi tafi sukayi shewa.

RAINA batako tankasu ba ta kallesu ta watsar tace

    “Banda abunku *MULKI* baya Koran *SARAUTA* yara saidai saurauta ta kori *MULKI* saboda ita mulki wa'adi gareta *SARAUTA* kuwa saidai tayita zagaye mtwwww” taja tsaki taci gaba da saida mashenta kan kace me RAINA ta siyar duka bokitin ta dauka ta juya ta kallesu tace

   “Shegiya ta siyar tabar masu uba da dangi” tafe take tana taunar cingam Wanda ya Dade tana ci salon ya fafe mata ciki, bakin shagon Kb ta faka ta siya gero Na wainar gobe sannan ta wuce gida tana shiga ta ajiye bokitin ta mikawa inna yalwa kudin tace “Inna waini meyasa yara suke cemun shegiya Mara uba? Nidai inna waye ubana?” tafadi tareda buga kafa, taba zunbura baki uwa durin jaka, Inna tace

  “Tabbas ke kaskan tacciyace Mara usuli shiyasa suke cemiki haka ina ruwanki dasu kifita harkarsu kiyi rayuwarki ke kadai koh tare dasu kukazo duniya?”.

RAINA tace
“Ah ah”

    Haka suka ci gaba da rayuwa cikin talauci da kaskanci inna yalwa tazama kamar karya itace fada da wannan fada da waccan kima Duk akan RAINA akeyi, saboda iyayen yara sunce basuso RAINA tana shiga cikinsu karta bata musu tarbiyan yara,

     Indo ce kawai take kula RAINA saboda jinisu yayi masifan haduwa da juna.

      Raina dai bata zuwa makarantar boko bare islamiyya zagon Mati babu makarantar arabi bare ta boko tsantsar jahilci ke dawainiya dasu yaron mai garine kawai yaje birni karatu wayo FU'AD.

     Tunda sanyin safiya inna yashiga ta watsawa raina ruwan tsanyi a gigice ta mike

“Ubanwa ya baki Hutu maxa ki mik'e kikai nik'a”

    Jitayi gabanta yayi mugun faduwa tace
“Inna wallahi banason kai nik'a matan gidan kyarata sukeyi,"

    "Sucemun Mara usuli abunda yake batamun rai kenan haka zakiga yara sunata kallona suna yamutsa fuska wai inna meyasa bazasu gane cewa ba laifina bane?
   Kaddara ce tafada mam”kuka ta barke dashi inna yalwa koh kallo bata isheta ba tace “Yida jiki kije ki dawo kar gari ya gama wayewa”

      Haka takai nik'an ta dawo ranta babu dadi, inna yalwa Kullun batada wani buri sai Na RAINA ta kawo mata kudi tako wani hanya shiyasa take koya mata duk wata baraka, tuni Raina ta baci dason kudi idan taga kudi jikinta har b'ari yakeyi.

      Yauma kamar Kullun ta dauki talla da barkakken zani silipas din Duk ya sud'e, RAINA babu zancen sallah bare salati saboda bata iyaba tafe take cikin layi tazo wucewa ta k'ofar gidan mai gari tun daga nesa Musalle yake tab'a abokinsa

     “Kalli RAINA yar gidan inna yalwa mai waina inason yin harka da ita saboda nasan zatayi maik'o” lashe baki yayi itakoh sai wani rangwada takeyi kamar wata tsohuwar kilaki, tana isowa wajensu tace “Zaku siya?” da sauri musalle yace eh zan siya haka ta sauke tana wani juya idanu wanda gaba dayansu saida sukaji wani tsar.

      Sun dauki waina ta murtala suka siya sukace tajeta dawo  tabiya  ta shago, tana siyarwa ta wuce sai shagon musalle ta tsaya ta rik'e k'ugu “Ah ah raina yan mata har an dawo shigo ki amsa kudin”

      Haka ta shoge tace itadai ya miko mata haka yadinga janta harta shiga ta zauna irgan kudi yakeyi sulalla tuni ta zauna don tana ganin yau zatayi chamama haka yace ta tayashi irga kudin tanayi tana sokewa a haban zani, duk yana kallonta tana gamawa yace “nawane?”

    Raina tayi far da ido tace “Na murtala biyarne” batasan yarigada ya irga murtala shida da goma bane ta zari talatin,

      Musalle bai damuba saboda yanaso yaga yayi nasara cewa yayi
“Raina yan mata dauki kudin duka nabaki” ba musu babu Jan aji ta karbe yadauko murtala kudin waina yabata shima ta karbe

  “Musalle kenan haka kakeda kudi?”

      “Hmm Raina kenan inda zakizo shagona da dare kinga wayannan kudin wallahi duka zambaki” tuni ta zare ido tafita sai gida sallaman datayi ne yajawo inna ta waigo 
“har an siyar haka nakeso maza shiga ciki biskin ki nanan kidauka, RAINA tace toh tana fadawa ta zuba kud'in cikin baki




*_MELODY_* 😍
Hope you guys are Enjoying my story? Pls vote and comment.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now