RAINA(the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA UKU

1K 41 1
                                    

*111-115* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA ASHIRIN DA UKU





Tsaye yake tace
“Ga takadda inaso ka saketa saki uku babu kome” Raina tak'ara sakin wani kukan Farid kam shima kuka yakeyi kamar Ransa zai fita Hajiya tak'ara cewa
“gashi rubuta”
“Hajiya saidai Kiyi hak'uri gaskiya bazan iya sakinta Matata ba saboda addini baice hakaba, Malamai da dama sunce inhar matarka tana cutarda Mahafiyarka kuma tace ka saketa toh ya halasta ka saketa saki daya idan babu cuta kabata hakuri cewa bazaka saki matarka ba, in tsinema tace zatayi toh tabbas tsinuwanta bazai taba tasiri akanka ba muddin kana kyautata mata don haka Kiyi hakuri Hajiya kibarni da Raina, bazan iya sakinta ba itace jigon rayuwata kidubi girman abunda ke cikinta Hajiya” ya marairaice
“Farid muddin baka saki waccan k'arfar ba toh saidai kazaba koni koh ita kana iya sauya mata amma uwa bazaka sauyaba”
Jin haka yasa Raina tace
“Farid kabi umurnin mahaifiyarka kabita amma kasani wannan cikin inhar yazo duniya karka kirashi da danka don bazaka sake ganina ba bare har kaga danka ke kuma uwar banza kinyi abunda kike buri kinji dadi inhar wannan cikin shegene Allah yana gani inkuma Farid danki shine ubansa toh insha Allah bazaki taba ganin jika daga wajen Farid ba”ta fadi hakanne badon batason mijinta ba ah ah saidon Mahaifiyarsa taga ishara Allah baya Goyon zalunci.

Juyawa Raina tayi har takusa shiga gida ta juyo tace
“Bani takadda ta” hannu ta mik'a Farid yabata saki daya yana kuka “Allah yagani inason matata da dana Amma hajiya kin tauyemun hakkina yanzu idan Allah ya amshi Aduar Raina kina ganin duniya ban muzanta ba?”Raina ta juyo wajen Hajiya tace “Ayyiiiiriiiiiii Jama'a gobe kuje Kaduna isa kaita road koh kafur ana auren Farid da uwarsa hajiya tasallah hajiya saiki zuba ruwa akasa kisha inaso ki aurawa Farid mace mai gindin gwal wacce tafini gata da iko harma da mulki, Uwar banza kisani kin Haifa kuma duk abunda kaiwa Dan wani toh wallahi rubutacce ne sai anyima” tsaki taja Wanda saida ni humairah na tsorata don yakai kusan second talatin haka hajiya ta turashi cikin motan sannan tace
“Ai farid koh mai gindin azurfa yace zai samu me akeda Kaska mai bak'ar kafa irinki andaiji kunya dakeda uwarki yan iska” hajiya yasa kai suka wuce suka bar *RAINA* cikin damuwa amma yata iya da Ikon Allah, cikin wata guda Raina ta haihu yara biyu mace da namiji Wato yan'biyu acikin gidan Ummin Abrar data rik'eta bisa yarda da amana itace cinta Shanta har mijinta yasan da zamanta don haka tana haihuwa tacewa Ummin Abrar
“Nagode k'warai da kulawarku keda mijinki saidai wani hanxari ba gudu ba nabaki yarannan bisa amana karki taba cewa nice uwarsu saboda zamana yak'are a cikin Kaduna zan koma Dinya wajen Goggo Kiyi hak'uri nabaki aiki amma ke kadai kika chanchanci wannan kyautar”
Abban Abrar yayi murna saboda yana k'aunar yan'biyu haka suka bata kud'ad'e suka kaita tasha ta tafi badan batason yaranta ba ah ah tabarsu wajen dazasu samu gatane Sanadiyyan yan'biyu Komai ya daidaita gidan Ummin Abrar, sunan yan biyun FA'IZ DA FA'IZA son kowa kin Wanda yarasa kyawawa ajin karshe duk inda suka kutsa sai an tanka haka aka dage dayimusu adu'a.

*DINYA*
Goggo na zaune tana karta itada tsaffi a zaure k'watsam Raina tagani tsaye tace
“Goggo barka da hutawa” Sannan ta wuce jiki ba k'wari ai tuni karta ta watse Goggo tafada gida tana mamakin yadda Raina takoma kamar wacce ta haihu zama tayi dirshan tace
“Ke lafya na ganki kamar daga sama lafya dai koh” Raina ta fashe da kuka tasa kanta a kafan Goggo tana kuka ta labarta mata komai duk abunda yafaru har cikin data haifa, Goggo tace
“lallai nema tace wani Abu karki damu yanzu bari afara wankan jego ki murmure kiyi fes acigaba daga inda aka tsaya” Goggo wai yaushe zata natsu tasan me duniya take cikine tambayan danake yiwa kaina kenan batada wani buri saina lalata rayuwar RAINA wacce batasan me ake cikiba tun zuwanta duniya,
Akwana a tashi wajen Allah ba wuya Raina ba karamin kyau tayiba a shekarunta Wanda basu wuce Ashirin da shida ba, amma wani ya rantse yace tsakiyan sha shida take tuni ta juya kambunta ta koma ruwa tsudum kamar yadda tasaba fita tadawo haka ta iske anyi chinchi rindo a kofar gida da isowarta mutane sukace gata ga mamaki naga ansa mata handcuffs a hannu motoci sai jiniya sukeyi abunda ya daure mata kai ganin Goggo dabatayiba, haka suka isa police station saida akasata a bayan kanta kannan ake sanar da ita abunda yafaru, ASP yana zuwa yaga Raina sai yaji tabashi tausayi k'warai tuni yace a fito da ita suka shiga office yayi mata nasiha har yace yana sonta amma bafa so irinna holewa ba don a rayuwarsa karuwa bata bashi shaawa asali ya tsani karuwa Amma a zaton Raina sone na hakik'a haka Kullun saita kirashi bayan ya sallameta wata rana ne taje office dinshi ta matsa kusa dashi tayi hugging dinsa lokaci guda yaji ransa yayi mugun bace ai jikake Tas tas mari takota ina Raina tuni tashiga rudu matsananci yace
“Kina tunanin inada lokacin yar iska irinki wacce batada kima bare daraja a idon mutane kina tunanin sonda nake miki na so ne? Me zanyi da karuwa irinki kisani koh mata sun kare bazaki taba zama uwar yayana ba tunda anasha a nono, this is the First and the last koh ahanya karki kalleni bare kice kinsanni get out of my office” karuwa kenan Mara kamun kai rayuwarta daman ta gaji rashin mutunci daga kowa babu Wanda yake ragamata saurayi yadaka kuma gobe yazo yace saurayi nake tabudemai kafa, tazama bola kowa ya zuba kazantarsa aciki Allah kasa mudace Amin.

RAINA (The beautiful princess)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora