RAINA (The beautiful princess) BABI NA TAKWAS

1.1K 44 0
                                    

*31-35        RAINA*
*(The beautiful princess)*

_*STORY & WRITTEN BY*_

© *HUMAIRAH (Melody)*


*BABI NA TAKWAS*

Fuuuu ya fice yabar Fu'ad k'wance hawaye ke zuba a gurbin idanunsa sai tsiyaya yaketa gefen ido ni humairah nace hawayen masoya ta gefe yake kwarara,

        Haka ya kwana baici wani abinchin kirki ba banda kuka babu abunda yake masa dadi a rayuwa, washe gari koh sallah yakasa zuwa acikin daki yayita yakoma ya kwanta tsawon kwana biyar babu wanda yasashi a ido illah satar hanya da RAINA takeyi ta kawo mishi abinchi, daya ganta saiya warke tana tafiya zai shiga cikin k'unci da tunani
“Malam wai kwana nawa Fu'ad bai shigo ya gaidamu ba koh lafya, indai lafya Fu'ad bazaiki shigowa ba yadda ya keda k'awa zucci”

     “Banda abunki meyasa zaki damu kanki yaron dabaida tunani Mara hankali mezaiyi dawata shegiya Mara uba kaskantacciya bafatada usuli inajin akan maganar danayine na cewa ya rabu da ita kuma aure da marka ba fashi shine yake azabtar da kansa don naji ance koh kasuwa baya zuwa”

Inna tashi tayi tace

“Haba Malam idan baa auren shegu ya za'ayi a rage irinsu agari,

    Inhar ana k'yamarsu ya za'ayi a daina haihuwar su karka manta ina daya daga cikin shegun duniya kuma haka ka aureni amma ace yau kaike k'yamar wacce bata da uba?

      Kayi kuskure hakan ya nunamun cewa abisa kaddara kake zaune dani badon soba hmmm malam kenan inhar ina numfashi aure sa shegiya sai anyi”

      Mai gari yace

     “Toh bada yawuna ba wallahi kuma bada kudina ba inyanada kudi zanje in nema masa auren yaje chan ya k'arata,

      Dakike zancen kema irinta ce toh kisani mahaifiyarki agaban iyayenta take harna ganki na aura kuma kaddara ce kuma sun baki tarbiya wacce tadace shiyasa har nayi shaawan aurenki kuma banyi Dana saniba”.

     Fitt ya fice haka tashiga Dakin taganshi kwance danuwansa a sama sallamar ta ne ya  ta saka shi tashi murmushi yayi amma ga rama da damuwa fal acikin ransa,

    “Fu'ad Ka daina kuka kaje ka nemo kudin aure mahaifinka ya aminche, wani tsalle yayi saboda murna yace “ya Aminche in auri RAINA?

   Alhamdulillah Amma naji dadi inna Allah yaja kwana Kiga jikokinki yanzu zanje in sanarda RAINA don nasan tana cikin irin wannan damuwan,

    Aii takalmi yasa tuni yayi waje garda gudu yake k'arawa nace Allah sarkin dadi soyayya maisa zumudi, soyayya mai sanya nishadi.

    Yana isa k'ofar gidansu RAINA ya tadda tana zaune a zaure tana cin Dan gauda, sallama yayi tana ganinshi taji wani dadi Wanda baxai misaltuba tace,

     “Fu'ad bakaji irin sanyin danaji ba Danaga kana murmushi yadda kasabayi mani ada kafin komai ya rinchabe”

Murmushi yayi yace

“Mai gari ya aminche da za'a turo akawo kudin aurenmu shiyasa kikaga naketa dariya saboda burina yakusa cika RAINA akanki na kizama uwar yayana”
Dad'i kamarya kashe RAINA Goggo ma tayi farinciki dajin wannan batun,

      Bayan kwana biyune Fu'ad ya yanke shawaran ya siyar da kayan shagonsa yakai kudin auren raina saboda inba haka yayiba bashida inda zai samu kudi bare harya iya biyan kudin Neman aure, da sanyin safiya ya isa kasuwa yakira Idi abokinsa suka nemi guri suka keb'e,

      Nan Idi yadinga kod'ashi idan ba raina ba sai rijiya rijiyarma mai k'walabe, Na Raina bada kanka asare aje gida kace yafadi, ina kafito RAINA ina zaka RAINA.

“Fadi ka kara Idi amma dakwai abunda nakeso kayimun,

     Inaso kasiya sauran kayan shagona inaso zankai kudin aurena da RAINA sauran kuma inaso zani birni karatu daga nan kaga sai'in kama wata sana'ar, koh NCE ce kaga sai inje inyi tunda inada k'walin sakandiri, inaso Raina taji dadi ne inaso wata rana indauketa inmunyi aure inkaita birni”
Dariya Idi yayi yace
“Lallai abokina kayi nisa lallai RAINA tasace zuciyanka Allah yasa karta watsama k'asa a ido don mata halinsu saisu, ka kare akansu sukare akan wani banza chan dayazo daga D'oshe, muje shagon muyi lissafi muga nawa kayan suka kama”

    Haka akayi lissafi kaya dubu hamsin da biyar ni humairah nace aiba wasu kud'in arzik'i bane ma, haka ya k'washe kaya zuwa shagonsa yamik'a masa kud'i yayi mishi fatan Alkhairi sannan sukayi sallama,

    Ankai kudin aure wanda Goggo ta amsa batareda wani namiji ba abundai babu kyan gani majina a gefen hanci.

*EDITED BY SERDERYERH😘*

_*MELODY*_😍

RAINA (The beautiful princess)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant