RAINA (the beautiful princess) BABI NA SHA UKU

1K 47 0
                                    

*56-60* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA UKU
_*Wannan shafin nakune masoya RAINA Allah yabarmu tare Yakaremu da katewarsa Allah yayi mana tsakani da mugaye Amin Basira ce Allah yabani ba don wayona ba ko iyawana ba*_LYSM😍😘❤




Cewar RAINA dake tafe tana shafa bango babu kowa acikin gidan Dan ko motsin mutum guda banjiba bare na tsuntsaye, ciki suka shiga suna shiga wani Parlour Raina tayi wani ihu tace
“Aljanna kenan”
“Ah ah sweet ba Aljanna bace wannan cewa zakiyi Aljannar duniya ”
Wani daki suka nufa banda batan baseerah irinta raina kiga gida Empty ai dole ranki yabaki wani Abu amma abunka da hakki Duk bata kawo komai ba
“Waw home sweet home RAINA wannan gidanki ne ke kadai sai yaran dazamu Haifa Ki sakata ki wala kinga idan kika huta anan zuwa anjima saimuje gidan Mu idan yaso saimu koma Zangon Mati ”
“hahaha Toh aiba matsala ni koh anan kabarni ainaje kauyenmu inba Sadiya labari dukda naga bakin ciki takeyi da soyayyarmu”
Tashi yayi
“bari inje insiyo miki abinchi da abun sha koh??????”
Haka ta amsa ficewa yayi yabi kafur road gaban BT motors yasiyo mata naman rago daganan yasiyo mata abun sha tafe yake naga ya tsaya gaban wani chemist wallahi bazan iya cewa ga abunda ya siyaba, saboda acikin envelope akasa mishi.

Gidan ya koma ya tadda raina zaune koh sallah batayiba bare salati, Sallah bata cikin agendan Raina saboda uwar dakinta batayiba bare tasata tayi, yar islamiyyan datake zuwa tasha ruwan waladaina, haka ya mik'a mata naman yakara ficewa haka taci tayi gytsa
“Inama Goggo tana nan kusa dana kaimata ta dangwala Arziki” kan me karatu yasha ruwa yadawo karatu raina ta dinga k'wada uban hamma Wanda saida ta jera ashirin, daganan kuma bacci yayi shillo riya da ita don har garinsu Mardia takai Wato nijar, koh minti goma batayiba da k’wanciya Uncle Aymel yashigo wani dariya yayi na mugun ta Tuni ya ida mugun nufinsa akan RAINA saida tayi mata facha facha da gaba wani ya rantse yace wuk’a aka chacchaka mata yadda jini ke zuba ni humairah saidana tsorata tsigar jikina ta tashi nace bai dace a hada mazan dawaki waje guda da matan dawaki ba saboda tabbas za'ayi batatta, abunda yafaru yafaru haka uncle Aymel ya kadawo bujensa iska ya barta k'wance tana bacci kamar matatta, inta k'aitama mai karatu pills Aymel yabata Wanda ake sharan Awa ashirin da hudu ana gantali a sararin samaniya.

Washe gari ne RAINA ta wastsake tasan me duniya take ciki kannan tafara kuka maikama da sautin wak'a, tana Kurma ihu saboda ganin halinda take ciki ba wuya tabbas yau ranar bakinciki ce agareta saboda abunda yafaru yafaru kuma abunda tarasa ta rasashi har duniya ta nad'e,
“Nashiga uku ni Raina Allah Kaine gatana Goggo duk kece silar komai nashiga uku yanzu shikenan nazama bola a idon duniya kenan waiyo duniya Tabbas Allah ba azzalumin kowa bane sai Wanda yaso ya zalumci kansa, Fu'ad wannan ishara ce nagani tabbas dole innemi yafiya a gareka, Ashe gaskiya kake gayamun Dana Sani daban biyewa zuciyana ba Allah shizai isarmum tsakanina da Aymel” bata gama rufe bakiba taji ana bude kofa cikin sauri ta waigo tana kallon mai shigowa, wani k'aton mutum tagani baki sidik babu alaman rahma a fuskarsa, ga wasu majiya k'arfi a gefensa da alama take masa baya sukeyi, tsawa suka daka mata
“Keeeeeee!?!!! In Wanda kuke tare dashi? Halama ke karuwarsa ce koh kwana wuni mukayi dashi gashi har kwana kukayi toh kudina zai bani ko kuma asan yadda za'ayi ” RAINA a tsorace takallesu tace
“Wannan gidan na Aymel ne akan me zakuzo kuna kumfar baki? Dan Allah kuyi gaggawan fita inji da abunda yake damuna”wani daga cikin yaran yace
“yarinya yaudaranki yayi kuma kisani bamu taba saninsa ba Dan garin Adamawa ne bakone zuwa yakeyi yayi holewarsa da yan mata yakara gaba ke karuwarsa ce koh” Raina tace
“Wallahi niba karuwa bace” daganan dukta labarta musu komai mai gidan yace saiya fanshe kudinsa haka ya tube ya kara hayewa kanta ai Tuni RAINA ta daina numfashi.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now