RAINA (the beautiful princess) BABI NA SHA TARA

983 38 0
                                    

*86-90* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_


BABI NA SHA TARA





Da isarsu Hajiya tasallah ba abunda takeyi sai yatsina fuska ta window raina ta hangi matar acikin ranta tace kindade baki yatsina fuskaba Daganin matar nan yar bala ce amma sainayi maganin iskancin mata ciki suka shiga sukayita k'wada Sallama ta fito tayi musu sannu da zuwa suka shiga, kan Chinese carpet suka zauna hajiya sai toshe hanci takeyi Farid sai kyafta mata ido yakeyi amma ina koh kallon bai isheta Raina tace
“Ina wuni hajiya kinzo lafya”? Hajiya tasallah tace
“Daban zo lafya ba zaki ganni wannan wane irin dakine farid saikace Masai sai doyi takeyi, wannan ai saiya janyo maka cuta akasa gane maganinta a Asibiti.
Ai tuni Farid ya dafe kai saboda tsabar kunya farida kuwa arsnta tace ai nasan a rina, Raina tacika da mamaki k'warai bin Hajiya takeda wani shu'umin kallo tace “Hajiya ga ruwa ga abinchi” ai tuni Hajiya ta watsawa Raina ruwan da abinchin Raina tayi dariya lokacinda Farid ya tashi don zuwa kusa da ita tace
“Basaika zoba Farid dadin abun mulki koh arziki baya tasa SARAUTA gaba saidai SARAUTA tasa mulki da Arziki gaba, Farid kai nakeso ba mahaifiyarka ba Kaine jin dadina ba wannan matarba, karkace naji haushi ah ah kodaya don na fuskanci Rayuwa wacce tafi wannan zafi dacin rai, Sannan kisani Duniya tafi bagaruwa iya jima, Ban nufin kowa da sharri sannan bana saka sharri da sharri sai in tura takai bango”.
“Farid daman irin wannan yarinyar zaka auro harta zama surikata toh bazata sabuba bindiga a ruwa, wane ni da daura zani uwar miji na yawo tsirara.

Fuuu ta fice batareda ta koh waiga ba kafin su gama rarrashin Raina ai hajiya tayi Nisa suna fita da mamaki babu ita babu labarinta, haka sukaci yawo wajen nemanta amma babu ita babu labari Raina aranta tace
“Yar iskan mata haka kawai ki addabi mutane wallahi danice baxan nemeta ba saidai ta bace mtwwwwww”
Nikoh HUMAIRAH nace Raina ba laifinki bane bakisan dadin uwaba bakisan soyayyar uwaba shiyasa kike tunanin kowa ya wulak'anta uwarsa..
“Farida Princess gaskiya daganan I can go beyond nan wajen am tired so tired yakamata Farida mukama hanya saboda bamusan abunda zai faru da hajiya ba”
Kallon Raina yayi cikeda so da k'auna yace “bari Mu tafi kinji saura dakwai kudi Dana ajiye miki banda bukatan komai na kayan daki ke nake bukata ranan daurin aure da'an daura kisa aranki zamu wuce kaduna, Goggo kuma nasama mata gida ita kadai Sannan na bude mata shago Wanda zata dinga siye da siyarwa, RAINA believe me you are my destiny you are my life I love you toh the moon and back”
Pec yayi mata yashiga mota Raina sai daga musu hannu takeyi, haka ta gyra kanta iya gyra amma sabo daban yakeda second new (Wato tsoho) amma Farid ya yarda ya aminche daduk yadda zai sameta,
Da isarsu gida farid ya kutsa hancin Motarsa cikin gida abunda ya tada mishi da hankali shine ganin fuskar kowa na gidan babu fara'a babu walwala,  lokaci daya taji gabanta ya fadi tafiya sukeyi kaman kwai ya fashe musu aciki wucewa sukaje yi Ayman daya kasance Yayan Farid   yace
“Dakata Mara mutunci Mara tarbiya zaka bige a yarinya fitsararra, wacce batada wani usuli yar cikin shege” .

Lokaci daya cikin k'araji Farid yace
“Karka sake Yaya karka kuskura ka sheganta mun mata ita nakeso kuma ita zan aura, Ku kukace inbidi mata kuma nasamo sai kuma yaxama abun gori Duk abunda Raina tayiwa hajiya ita taso kuma ta siya da tsabar kudinta don haka let me be on my own after ol inada madogara idan kukace inbar gidannan zan Bari koda kuwa yin hakan sabo ne yaya na gwammace in dauwama cikinsa”
Tas tas kakeji Ambassador Garba ne ya kwashe Farid da mari yace
“gobe za'a daura maka aure kuma a gobe zakabar gidannan don naga abun naka harda cin mutunci”
Farid yarike kunci yana zubda hawaye yace “Nagode kwarai daddy nagode da duk wata dawainiya dakayi dani daga haihuwa zuwa yanzu Allah yasaka muku da Alkhairi nagode” wucewa yayi yasamu wayar mahaifinsa yayi transfer din kudi naira Miliyar Goma ya ajiye kamar baiyiba, Sannan yashiga daki ya hada komai nasa Farida sai kuka takeyi Rumgumeta yayi yace
“Takwarata kar kiji komai Allah yana taredani a duk inda nake kuma jihadi zanyi na auren Karuwa mai zaman kanta, kuma ta dalilina indai me shiriya zata shiryu kukanki yana dagamun hankali”
Shuru Farida tayi nadan lokaci a inda take sauraren wayarda Farid yakeyi tasan bada kowa yake wayaba saida RAINA,

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now