RAINA (the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

940 37 0
                                    

*121-126* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY*
*HUMAIRAH (Melody)_*

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

“Maryam itace tasa na saceki saboda nata Manufar, tabbas idan tabarki a cikin gidan Danta *DANISH* bazai samu wata kulawa ba  saboda sarki MAMUDA bashida wani buri Wanda ya wuce ganin k'wansa a duniya Shiyasa muka kulla wannan makircin muka musanyaki da matacciya na gudu dake akan kudi kalilan Wanda basu amfaneni da komai ba, shiyasa nakasa baki tarbiya mai kyau saboda banaso kizama abun alfahari a duniya, tarine ya sarke Goggo Wanda saida tayi wani amai harda jini, ASP yace
“Ko zaki iya sanar damu inda zamu samu gidan Sarki MAMUDA?”
Goggo da kyar take magana tace “Yana cikin garin Kaduna dazama a k'aramar hukumar Kajuru..........

Tana gama magana tayi shak'uwa har sau uku daganan tasaki wani razanannen kara ai sai kuma akaji shuru, RAINA wani irin kara tayi ta rungume Goggo tana kuka tana “Goggo maiyasa zaki mutu kibarni? Dan Allah ki tashi” ikon Allah kenan kudubi girman laifinda Goggo tayiwa RAINA amma soyayyar Goggo yana cikin ranta harda zuciya nasan duk Kukan da Raina takeyi na tsantsar shakuwane, haka aka lullube Goggo cikin Zanen Asibiti, tuni yan sanda suka nufi Kaduna tun safe sai dare suka dawo saboda tsabar nisa jiniya kawai nakeji abun mamaki ina lekawa cikin harabar Asibiti motoci nagani convoy bak'ak'e wani mutumi nagani black beauty yana tafe cikeda kasaita cikin Alkyabba.

Ana takamai baya suna shiga Dakin da Goggo keciki sukayi tozali da RAINA jiyayi gabansa yayi mugun fadi kallon kallo kawai sukeyi kujera aka sa masa ya zauna RAINA koh takasa kuka takasa dariya saboda tsabar farinciki, Danish ne tsaye yana kallon raina jiyake ya tsaneta saboda tundaga kallon fuskarta yaga dukta kone saboda tsabar bilicin, Kirari kawai ake yiwa Sarki MAMUDA haka likita ya budema sarki fuskan Goggo yana gani yace
“Ai wannan binta ce” tuni ya Umurci RAINA data matso kusa dashi haka yadafa kanta yacema likitoci ayi gaggawan yimata sutura don su daganan Kaduna sukayi komin dare, haka aka yiwa Goggo sutura Harda ASP a wucewa kajuru kafin isarsu gida yacika yayi makil sai sarewa akeyi da kalangu abinchi kuwa kala kala saboda tarban Gimbiya RAINA, basu isa garin kajuru ba sai misalin Asuba amma gidan yadda kukasan rana, Haka raina tafito harabar tank'a sheshen gidansu acikin ranta cewa tayi yanzu Ashe nimai gatace amma aka shiga dani duniya na wulakanta?  Kaico duniya Allah Kaine gatana, kuyangune sukazo suka wuce da Gimbiya RAINA zuwa bangarenta da tunkafin zuwanta duniya aka killa ceshi.

Ciki Raina ta kutsa kai tashiga Tunda take bata taba katari da kayataccen daki irin wannan ba  kalle kalle kawai takeyi wata daga cikin kuyangin tace
“Ranki yadade wannan shine dakinki mune masuyi miki hidima duk abunda kikeda buk'ata muzamuyi miki , suna cikin magana akayi sallama jakadiya ce tsaye daukeda wasu kaya masu kyalli da shek'i
“Gimbiya ranki yadade Allah yaja kwana Wayannan kayane saga sarauniya Maimunatu mahaifiyarki tace ki sanya idan kin kammala wanka”
kuyangin ne suka amsa suka ajiye tuni aka hada mata ruwa mai tsafta turaruka kuwa sunkai kala goma da'aka acikin bath din ciki tashiga tayi minti Talatin tana wanka ita kanta tasan tayi wankan dabata taba bata lokacinta wajen yiba, fitowa tayi tuni kuyangin suka dau towel suna tsane mata jiki zama tayi tana shafa mai masu kamshi sannan ta shirya cikin kayanda aka kawo mata har bayan Sallah Asuba hidima akeyi gari na wayewa fada tacika makil da Al'umma haka aka kawo RAINA tafe take jitake kanta yakara girma, Jitayi tabbas SARAUTA tafi mulki kuma SARAUTA ajini take baa  kudi koh dukiya ba, haka akayi Adu'a akayiwa Gimbiya barka sa dawowa daular mai martaba sarkin Kajuru.

RAINA (The beautiful princess)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang