RAINA(The beautiful princess) BABI NA SHA TAKWAS

998 34 0
                                    

*81-85* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA TAKWAS

Juyawa tayi afusace yashige daki tana keta uban zufa
“yanzu ni Farid zai watsawa kasa a ido lallai saina hanashi kwanciyan hankali acikin gidansa muddin ina raye”
Wayarya ce ke kara tana duba tankamemen Screen din iPhone 7 dinta taga ansa unman Farida gabanta yafadi tace Allah yasa ba sun fasa bane don inkan bakana, karaf ta dauka tace
“Hello hajiyar Allah ykk ya sirikata?”
“Hajiya babu lafya fah Farida tace itafa batason Farid tace itafa tanada Wanda takeso tace do or die aure tsakaninsu da Farid babu gata tanata masifa tana farfasa kayan gida”
Jikake tas tas tas
Ni humairah dake labe don kar a jehomun flower vase ai tuni na fita aguje, katse wayar sukayi kowa yana jimami, Tuni suka shirya sai garin Dinya inda RAINA suke zaune dayake sunbar gidan karuwai, Raina itace karuwa mai ladabin kunama, RAINA yayi musu girki kala kala iri daban daban amma babu dadin sisi bare kwabo, Haka akayimusu tarban girma, tunda Farida taga Raina taji gaba daya ta kamu da sonta tana jinta tamkar yar'uwarta tajini haka sukayi hira mai kwantar da zuciya, Farid kuwa saboda tsabar kwaliyan RAINA har kasa magana yakeyi bare yayi mata kallon minti biyu ji yake kamar ya dau hannu ya tabata,
Raina dai jar fata ce son kowa kin Wanda ya rasa siririyar fuska gareta ga saje ta kowane gefen fuskanta, Bakinta bawani karami bane kamardai nawa, hancinta shima Dan daidai Wanda za'a iya misaltashi da dogo amma ba kwarai ba, idanuwanta kanana kamar maijin bacci, sannan sun danuwanta kamar na maciji yayi shape sosai, Raina dai baxamu kirata gajera ba haka baxamu ce mata tanada tsawo ba tana tsaka tsakiya, gashin kanta baida wani yawa bacin acuci datakeyi ai sai a gudu saboda kamar hammatan San iska yake,
Wannan kenan.

Misalin karfe uku Farid yace
“Princess zamu wuce duk abunda muke ciki zakiji sannan karkiji komai sannan ina umurtanki dakiji ki kiji saboda akwai wasu matsaloli, haka sukayi Exchange din number da farida suka wuce sai Kaduna,
Fitarsu keda wuya Raina takoma ciki tace
“Goggo yanzu yaxamuyi kina tunanin kezaki amsa kudin aurena kamar yadda kika amsa na Fu'ad? ”Goggo tace
“K'warai nizan amsa Susan cewa ke mara galihu ce Mara usuli bare tushe, koh kinada Wanda zai amsane bayanni?”
Goggo ce ke magana cikeda iko da isa da MULKI Raina tace
“Goggo kinsan cewa mulki baxai kori SARAUTA ba? Kinsan da haka toh inaso kisani baki isa ki amshi kudin aurena mutukar bazaki nemomun ubana ba saboda ba kimata bace bare daraja ace kece zaki amshi kudin aurena baxai taba yuwuwa ba, idan kuma kince ah ha maxa ki nemomin mahaifina, nasan cewa bazai ki jininsa ba”Tuni Goggo tafara ba RAINA hak'uri tana lallashinta haka Goggo tasamo mutane uku Wanda sune suka amshi kudin saboda kimarsu da darajarsu saida Ambassador Garba Buba yayi musu kyauta,
Sadaki dubu dari aka bada da akwatina guda goma cikeda kaya.

Bayan tafiyarsu ne Goggo ta fito daga inda ta boye ta amshe kaya tayi musu godiya abunda yabata musu rai kenan, har saida kyauta ya tsaidata yace “Me kike nufi tsohuwar kilaki koh kin manta yarda mukayi ne miko”
Hannu ya mikawa Goggo haka ta debo kudi tabasu adai rabu lafya, Ranan sati biyu akasa sannan a masallaci za'a daura auren,
Bayan k'wana Uku da kawo kaya hajiya tasallah tamatsa sai ankaita taga Raina sannan hankalinta zai k'wanta, Farid bashida yadda zaiyi haka yakira Raina yasanar da ita komai haka ta shirya cikin tsadadden lace tayi makeup komai yaji,
Sauraren zuwansu Farid kawai takeyi,
Dazasu wuce saida farid yabiyata gidansu farida yace tafito su wuce tare, sai garin Dinya.
“Farid wai ina kuke shirin kaini ne kar dai kacemun yarinyar anan take?”saboda yana tuki yarasa wace irin amsa zai bata shuru yayi baice komai ba
“Farid magana nakeyi kayi shuru”?
“Hajiya me kikeso ince miki kinsan dai Asalin kowa kyauye don wannan garin birnine akan wasu kyauyukan” tundaga haka bai kara cewa uffan ba farida kuwa Adu'a kawai takeyi kar umman farid ta wulakanta RAINA don raina bazata raga mataba saboda yar bariki ce.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now