RAINA (The beautiful princess) BABI NA SHA DAYA

1K 41 0
                                    

*46-50        👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA DAYA

Washe gari an tashi daga makaranta tafe take tana wasa da yatsunta, Sadiya tace “Raina daman inata so inyi miki magana yau naga gaba daya kin canza yadda kike walwala yanzu babu meye dalili?”Raina tayi murmushi tace
“Sadiya tunani nakeyi wazan zab'a? Tsakanin Fu'ad da Aymel a gaskiya ina son Aymel yanzu fiyeda Fu'ad, tunda Fu'ad ya tafi yakasa koh sau daya yazo ya ganni baisan a wani hali nakeba shiyasa na yanke hukunci Uncle Aymel ya turo gidanmu muyi aure”
“A gaskiya Raina idan kikayi haka kinyi tsantsar butulci kar kizama butulu mana ki tuna irin hidimar da Fu'ad yake miki amma ace saboda baixo ba zaki auri wani meyasa kikayi mishi Alk'awarin zaki rike mishi amana? Kiyi tunani dakyau ki tuna saboda ke ya tafi birni Neman ilimi don Ku tsira da mutuncin ku amma kiyi hakuri idan na bata miki rai”Sadiya tana gama magana tayi wayi hanyar gidansu batareda ta karabi takan RAINA ba.

Tafe RAINA take tana lissafe lissafai horn taji Tuni ta juyo a firgice har Aymel saida yagane RAINA tana cikin tsananin tunani, packing yayi yafito yace
“Dafatan lafya yadda naga kike tafe bakisan Wanda ke bayan ki ba, shiga mota inkaiki gida”
Tsaye tayi don inzaa yankata batasan yadda ake bude motarba ga girman kai rawanin tsiya tak'i tace bata iyaba gajiya yayi ya fito ya bude mata motar ta shiga kannan ya shiga wajen direba,
RAINA tayi kaman ruwa ya cinyeta saboda tsabar tsoro bata taba shiga motaba, Tuni ta fara rawan Dari saboda tsabar sanyin AC Allah Allah tayi su isa kofar gida, suna isa ya bude mata murfin motar tafito kamar wacce ruwa ya cinye ya dawo da ita, “Gimbiya ina sauraren amsa daga gareki saboda na kosa in kaiki ga iyayena” gyara tsayuwa tayi tana shirin magana k’watsam ta hangi Idi abokin Fu'ad.

Tuni ta bata rai ta hade giran sama Dana k’asa ta isa wajenshi tace
“Malam lafya kazo kofar gidanmu? Mekazo yi kallonta yakeyi ido cikin ido yana mamakin Raina ce take gayamai wannan maganan? Dariya yayi yace
“Saboda kina tareda wancan matin ne kike wani hura hanci mtwww yaja tsaki kinsan ke kinyi kadan inzo wajenki banza Mara tarbiya Goyon mace gashi Fu'ad yace inbaki”
Watsa mata kudin yayi yana huci yace
“Yadda kikazo a wulakance haka ga kudinnan na watsa miki a wulakance banza yar Mara asali banda kaddara me Fu'ad zaiyi dake Taxi kawai motar kowa da bamusan Asalin angulu ba saitace daga missra ta taho”
Fuuuu ya kama hanya zai wuce ta gaban Uncle Aymel Tuni yasamai kafa saiga Idi warwas a k'asa haka Aymel yayi biji biji da Idi harsaida mutane suka zo ceto saboda kar ayi kisan kai, kudin dake kasa ya kwashe yaciro kudi bansan iya yawansu ba yace
“Gashinan”
ya watsa mishi yace
“Kasani Kaine Mara mutunci da ka kasa ganinta a matsayin kaddara wacce ta Riga fata, meyasa kuke sheganta abunda Baku San asalin zance ba bari kaji babu wani shege a fadin duniya kowa da ubansa da uwarsa Allah ne kadai bashida uwa bashida uba bai haifaba ba'a haifeshi ba”
Miyau ya tofawa Idi sannan ya juyo yace
“Gayamun abunda kikeso ki gayamun kam zuwan wannan garban?”

Gyra tsayuwa tayi
“Uncle Aymel na aminche zan aureka katuro manyanka zuwa gidanmu”
Wani dadi Aymel yaji ya juyo yace
“Wa yakeda suna Fu'ad kowa? Kace mishi yayi lissafin abunda ya kashema RAINA zan biyashi, sannan ina gargadinka banaso in k’ara ganinka bare fuskarka koh a hanya inba hakaba saina takeka da mota, duk abunda akeyi nida Aysha sayedi muna gefe kowacce ta rik'e haba tana jin karfin hali irinna Uncle Aymel.
Haka sukaci gaba da soyayya kamar da gaske, har Aymel yasa ranan da Raina zata gaida iyayensa haka Goggo ta aminche, yayimata siyayya nagani na fada a gari komai too match, nikaina saida na roller.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now