RAINA (the beautiful princess) BABI NA SHA BIYU

1K 44 1
                                    

*51-55* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA BIYU

A gari kowa gulmansu yakeyi yar makarantar da Raina ke zuwa bata zuwa haka kauyen Zangon Mati yaci gaba kowa kagani burin dansa yaje makaranta, Haka y'ay'a mata cikin kashi Dari kashi 85 sun rage talla,
Babu wani Abu da iyaye zasuba yayansu Wanda ya wuce TARBIYA don shine ya kori komai a rayuwa matuk'ar kinbawa danki tarbiya toh kisani ko bayan ranki wallahi tamkar baki mutuba, saboda komai sukayi na Alkhairi ke za'a yabawa keda kika daurasu akan turba mai kyau, yau Uwar gida\iyaye ina dadi ace yau an wayi gari baki bakya numfashi Ace ga danki chan yana zagi koyana fada kinga kinbarmai abun fade babu abunda zai fito bakin jama'a sai suce ai Uwarsu ce bata basu tarbiya ba, wallahi koda Dan gaba da fatiha ne kika bashi tarbiya wallahi yaxama na k'warai zakiga yadda mutane suka sha'awarsa Alfaharinki ke uwa ki ba yayanki tarbiya saisu zama abun kwantance musammam yaya mata saboda sune rayuwarsu take cikin hadari wajen fuskantar rayuwa.
Ranan wata ladi ne Raina ta shirya tsaf cikin lace mai ruwan madara sai shek'i yakeyi komai too Match Goggo tsaye take gwada mata yadda zatayi tafiya da magana idan taje gidansu Aymel babu komai aciki sai fitsara keda zaki ganin surukai har wani dama gareki babu wani kunya bare kunyan sarkin gari Allah kasa mudace, Raina da Goggo sunyi nisa ba'a cewa komai.

“Goggo saimun dawo”Goggo ta rakata da d'umi fita tayi ta iske Uncle a waje sai dariya yakeyi yana kod'a Raina saboda kyau datayi, nikaina mai karatu ban ganeta ba saboda takoma Rainan gaske bata Zangon Mati ba,
Suna tsaye mashine yazo wucewa da Fu'ad abun mamaki yaga raina tana shirin shiga mota da sauri yace mai machine ya saukeshi, cikin sassarfa ya Isa inda Raina take yana dariya
“Raina kece haka Alhamdulillah gani na dawo wannan waye” duk a Jere yayi mata wannan tambayar tsawa ta dakamai tace
“Dakata Fu'ad wannan da kake gani shizan aura shine annurin raina shine miftahul Qalbi na shine nake burin yaxama uban yayana, kafadi kudin daka kashe akaina abiyaka don ba talaka bane irinka, mai shiga rana yasamo”
Da mamaki Fu'ad ke kallon RAINA cikin tashin hankali yace
“Raina kar kiyimun haka”
“Na nawama”cewar RAINA
“Kiyimun rai idan kika rabu Dani raina ina zansa Kaine kece farincikina, RAINA zan iya rasa raina idan kikamun haka Raina kalleni nine masoyinki na asali Nina chanchanta da'in zama Uban yayanki, Kituna Raina munyi Alkawari sannan nabaki amanar soyayyana meyasa kike kokarin badamun kura a ido, kisani Allah dakansa yace duk Wanda yaci amanar wani toh tabbas Amanar Allah saita ci mutum, RAINA Alkawari kayane duk Wanda ya dauka burinsa ya sauke, Raina banida wani tunani sai naki ki taimakeni, Raina ciwonso bashida magani Wallahi Daganin wannan ba aurenki Zaiyi yaudarace tsantsa acikin idonsa”
Kuka kawai Fu'ad keyi Wanda nikaina naso in tayashi don nasan zafin rabuwa da Masoyi babu dadi, Raina kuwa watsa mishi kallo tayi tace
“Banida lok'aci haka ta shige mota batako saurari Fu'ad ba haka Aymel ya figi mota wani kurane ya tashi Wanda Tuni Fu'ad ya fadi kasa yana wani irin tari abunka gamai ASMA, Tuni mutane sukayo kansa aka daukeshi sai gida.

★★★★
Raina ce cikin mota suna tafiya banda k'yauyenci babu abunda take zubawa, Shiko Aymel yana dariya kamar yaga wawan zama, Da haka Raina tadinga murna ganin sun shigo cikin birni tsundum, Cikin garin Kaduna ne a Isa kaita road, wani layi mai suna kafur road, wani katon gidane Wanda ya amsa sunansa gida ya tsaru iya tsaruwa, babu ne kawai babu acikin gidan,
“Allah sarkin dadi inji barawon mando”

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now