RAINA (The beautiful princess) BABI NA SHA SHIDA

1K 43 1
                                    

*71-75* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA SHIDA

Haka Raina taja Goggo data kasa cewa komai abun duniya ya isheta, shiko magari tsaye yayi yace
“kumu tafi daman barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba shine da Fu'ad yake shirin jajibomun irin tsiya irin jaraba da haka zata dinga tsigeni nida marwa” haka suka koma Tuni akayiwa gida kudi Fu'ad ne yasiya har naira dubu Dari biyar badan komai ya siyaba saboda RAINA dayasan cewa duk abunda yafaru da ita daga Allah ne amma yajin baxai iya hada zuria da RAINA ba, haka aka kaimusu kudi washe gari tunda duku duku suka tashi basu sauka koh inaba sai Wani gari *Dinya* Gaba da SOBA inda akwai matattaran karuwai da masu zaman Kansu, haka suka samu hayan daki daya k'ato suka sai katifa Dadai sauran kayan aiki, nan RAINA tafara baje gwanjon tsiya itada yan gidan saboda samari suna kawo mata bara cewa suna sonta ita kuma kowa yitake dashi, indai zaka sak'ar mata kudi yan dubu dubu farare, Goggo itace magajiyarsu itake ba RAINA duk wani salon yaudara da samun kudi Haka basu zauna ba wajen bin bokaye don Neman sa'a, Raina koh tajik'u  sosai da mugunguna don tace bariki tun ina k'arama na iya toh yanzu nasa kafa wancan sharan fage nayi, kowacce mercy kallon docas nake mata, Goggo batada wani buri saina ganin Rayuwar raina ta Daidai ce saboda kin jininta da Tayi tun zuwanta duniya kawo yanzu.

Raina dai tazama abar kwatance a gari tazama maiji da kanta a shekara Ashirin RAINA ta mallaki gida da mota Wanda babu kamar sa acikin garin soba da kewayenta haka bangare daban tayiwa Goggo sannan aka girke rikakken malami koh ince boka, Shike mata aiki don duk namijin daya kawo kansa gidan Sunanan sa sorry don bata amsan kudi a hannu sai Check dukda ba arabi ba boko wani yaga Raina zaice tayi digiri harda digir gir Abu yayiwa raina yawa ga sata ga maita, ga zina ga madigo babu Wanda batayi Alhaji bello shine Wanda ya tsarewa RAINA komai na rayuwa sannan ya hanata mu'amala da kowa wata rana k'watsam Matarsa takira shi don taji rade radin ya ajiye karuwa, kin dauka yayi saboda tsoro, RAINA tana kwance daga ita sai yar shimi sai pant nashiga Swimming pool ta dauki wayar ta kara a kunne
“Hello Ranki ya Dade uwar gida saurautar mata mai suna biyu lafya mijin naki bacci yakeyi pls kiyi hakuri zuwa gobe koh jibi don banison takura bare damu”
Kafin matar tace wani Abu an kashe wayar gaba daya haka Raina tafada kan jikinshi tana shafa mishi katon cikinsa tana mishi hirar love shiko Tuni ya sakankance yabada kai bori ya hau yana gamawa yashiga wanka yace zai wuce RAINA tace
“Miliyan daya nakeda bukata inaso zanyi yan wasu hidimomi ne kafin ka dawo daga England koma Mu wuce tarene?”

Alhaji yayi dariya
“Hmmm RAINA kenan sonki kawai nake kaunarki tana dibana mezai hana mutafi tare Visa akayi mata rana guda saboda dakwai kudin haka suka wuce kasar England saida suka Shari wata daya suka dawo,
Ni humairah nace
Raina tauraronki yana haskawa yanzu toh wata rana saiya dusashe yakoma hasken gulob daganan hasken rechargeable gaba gaba harken fitilar kwai sai kuma na aci balbal mai hayaki sai kuma dundim, komai yanada lokaci  Allah yasa mugane ngd Allah daya bani iyaye masu kula ba irin Goggo ba daman batasan zafin haihuwa ba sannan batasan zafin lalacewar rayuwar da ba, zeenert ce kishingide akan kujera tana waya tana gamawa ne RAINA tace
“Zeenert kenan dole in tsula tsiya yadda nakeso saboda inada wacce ta tsayamun sanadiyyan Uncle Aymel rayuwata ta lalace sannan kinsan wacece silar? Goggo, babu wani makircin daban iyaba babu salon daban iyaba zeenert Abu daya nakeso shine a duniya yanzu in Sani waye ubana sannan yar wace Garice ni haryau Goggo taki gayamun amma nasan wata rana dole ta sanar dani komai”
Zeenert tace
“Tabbas kuma ai ranar wanka ba'a boyon cibi”
“Maganarki dutse yar uwa ”

RAINA (The beautiful princess)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora