RAINA (,the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA TARA

1.1K 58 17
                                    

*141-145* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_



_*Wannan page din nakine MARIYA AHMAD ILIYASU Son da nake miki is different ngd da karamcinki gareni @Anatare 😍😍 lets keep chillingGulx💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_



BABI NA ASHIRIN DA TARA



Akwana a tashi wajen mai rai RAINA babu abunda take zullumi sai gamuwarta da DANISH Wanda k'wata k'wata bayasonta haka ranar daurin aure ya rage saura kwana uku, UNAIZA ta dawo cikin gidan sarautan wajenta dabanne nesa da inda RAINA zata zauna, Unaiza ce tsaye a bakin taga inda take hangen masu kaiwa da komowa hankalinta yayi kololuwar tashi
“Yanzu nice zaayiwa kishiya? Tab lallai daman hakan nuwaira taji lokacin da AB zai kara aure?” Jitake kaman zata hadiyi rai ta mutu saboda tsabar son danish datakeyi sai yanzu tasan cewa miji mijine wacce ta raba miji da wata tayi gagarumin sake.

Wata sain ba sake bane kaddara ne kuma rubutaccen Al'amarine ana gobe daurin aure Unaiza ta fita mike k'afa ga gida ya cika dankam da mutane bata zarce koh inaba sai hanyar dazai sadata da bangaren RAINA tafe suke itada Kuyanginta da'aka bata don yimata hidima suna isa k'ofar RAINA tayiwa kuyanginta umurni dasu jirata koh sallama babu ta banka kofa, Raina tana sama itada zeenert k'awarta tafitowa tayi da sauri lokacin duk kuyanginta basa kusa, daga saman bene tace
“Wace yar akuyarce Mara tarbiya bare dabi'a take shigomun falo ba sallama? Koh bataje islamiyya bane?”
Unaiza data kulu tace
“Kul yar tasha ragowar bariki Karki kuskura ki zageni har kinada bakin zagin wani mara tarbiyya gaki BABBAR Mara tarbiya wacce rayuwarta ta kare a bariki inaso kisani igiyar rak'umi tayi nesa dana kaza kiyi gaggawan rabuwa da mijina kafin a haifi da Mara ido”.

Raina ce tafe zata sakko zeenert kuwa tana sama tana kallon abun al'ajabi,
saida RAINA ta zagayeta sannan tayi guda tace
“koh ba'a mijiba danish dan'uwana ne kuma inada right din aurensa tunda ba nono daya mukasha ba sannan Kuma ba uwa daya uba daya mukeba bare kice ba aure, kisani saikinyi kishi da Raina kafin in irga uku kiyi gaggawan fita inba hakaba kiji kunya ” Unaiza shuru tayi don abun yasha karfinta kishi da Baban miji Fita tayi a fusace cikin sauri kuyanginta ke biyeda ita tana shiga daki ta fada kan gado zufa kawai takeyi abun duniya ya isheta Kuyangarta ta aika aje a nemo mata Danish ace tanason ganinsa amma Ina abun yaci tura yana cikin garin Kaduna gidan Ab abokinsa, Unaiza tak'asa rintswa takai gwaro takai mari har misalin shadaya nadare lokacin dataji gunjin motar Danish bata tsaya bata lokaciba tafita da gudu tayi inda yake fadawa jikinsa tayi lokaci daya ya hankadata batareda yasan itabace yace
“RAINA ina kyautata zaton kinyi kuskure wajen zuwa ki rungumeni dis is the First and the last kisani banza kawai kina tunanin zan iya hada jiki dake toh kisani *Auren jeka nayika zamuyi* ba auren Darai yake muradi ba”.

Yana gama magana Unaiza tace “Baby ba RAINA bace nice matarka Unaiza kayimun rai kazo gareni ka ceceni don duniya ina cikin duniyar ladama nayi dana Sanin yimaka wasu abubuwa a baya pls forgive me i dont mean to hurt your feelings any more Darling” wani gigitaccen tsawa yayimata Wanda saida taji kaman zata gudu Yace
“Unaixa kinyi kuskuren zuwa inuwata bari Kiga yadda ake ganar da mutum irinki kuskurensa, kin manta cewa kinyi rantsuwa bazaki sake zuwa inda nakaba?” ai rufe baki tayi tana gunjin kuka
Ai batayi auneba saijin belt tayi tako ina sai hambareta yakeyi babu imani koh tausayi saboda Unaiza ta cutardashi ta inda mai karatu baya zato, Danish yana masifan son Unaiza lokacin da yakamata tayi amfani da damarta lokacin ta watsar saboda sonshi yafi nata tasiri, Akan Unaiza bata biya masa hakkinsa yafada ga aikata zina duk lokacin daya buk'aci mace saidai yaje waje tur da halin Unaiza wacce sanadinta mijinta yashiga halaka mata muyi imani mu kare hakkokin mazajenku.


Comment dinku shizai karamun karfin gwiwa

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now