RAINA (the beautiful princess) BABI NA ASHIRIN DA HUDU

944 38 0
                                    

*116-120* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA ASHIRIN DA HUDU


Haka rayuwarsu Raina da Goggo yaci gaba saboda tsabar iskancin Raina gari gari take zuwa bata Abuja bata Port Harcourt bata Tafa wata ranan asabar ne aka tashi da fada acikin gidan da Goggo take inda aka samu wata mai suna BELA ta zage Raina tas tayi mata wankin katon bargo sannan tayi mata gorin dangi hardana yan'uwa
RAINA bayau aka asaba yi mata gori ba hakan yazame mata tamkar Riga yar shara haka tashiga daki ta tasa Goggo dole ta sanar da ita inda danginta suke kodan tanunawa duniya ta wuce gori kuka take babu kakkautawa, Goggo ce zaune shurum takasa cewa k'ala bare tayi motsi mai karfi jiki ba k'wari tace
“Raina kinaso kisan asalinki?”
Raina tace
“kwarai Goggo maizai hana Ido rufema kuwa” Goggo ta yunk'ura tace
“Jeki bayan layi siyo mana k'osai idan mukaci muka gama sai in sanar dake inda yan uwanki suke batareda bata lokaci ba” haka *RAINA* ta mike badon ranta nasoba ta fice ai koh second sittin  batayiba Goggo ta mik'e ta k'ulle kayanta ta k'washi yan kudi a lalitan RAINA kafa mainaci ban bakiba Goggo nafita ta tare Dan achaba tace yakaita cikin gari Dawowar Raina keda wuya ta kutsa daki da mamaki ba Goggo babu labarinta saida ta zauna tsawon minti Goma a tunaninta kewaye tashiga amma shuru kakeji Malam yaci shirwa.

RAINA ce tafito a hargitse tacema wata K'aruwar Gidan
“Dan Allah koh kinga Inda Goggo tayi?”
Budar bakinta tace
“Tafita da kullin kaya akai batayiwa kowa magana ba illah wuce mu datayi” RAINA tayi ihu ta tuma a kasa tace
“Waiyo nashiga uku ni Raina Goggo Dan Allah karki tafi kibarni ina zan dosa kiyimun rai Goggo kece gatana kece abun alfaharina yanzu idan kika tafi Zargin Mutane ya tabbata akaina duniya banida wani gata kashe kaina zanyi in huta Waiyo kaico duniya Ni Raina naga takaina” kuka mai tada hankali Wanda saida wasu suka tausaya mata
Tana cikin burari ne wayarta tafara k'ara cikin hanzari ta dauka ganin lambar Goggo tace
“Hello Goggo Dan Allah kidawo” harda dariyarta amma saitaji namiji ne yake magana Murna saita koma ciki.
“Baiwar Allah idan da namiji kuzo bakin kasuwar soba anyi hatsari kuma matar RAINA kawai take kira” karaf aka kashe RAINA ta hauk'ace kuka takeyi mara sauti da gudu ta fice gudu kawai takeyi tana zuwa taga Goggo k'wance acikin jini wani ihu tafasa ta mance da salati bare yadda akeyi.

“Goggo Dan Allah karki mutu idan kika mutu inazansa rayuwana Goggo kar kice yadda nazo duniya haka zan koma Goggo ke kadai nasani a duniya idan kika rasu inazan dosa Karyata tak'are  Goggo ki tashi Dan Allah” jijjiga Goggo takeyi amma batasan halinda take cikiba zuwan Roads safety ne yasa akasa Goggo a mota sannan ga police da mamaki Raina tana daga ido tayi arba da ASP Ahmad Yari tuni taji sonsa ya karu cikin zuciyanta har suka isa Asibiti RAINA takasa daina Kallonsa saboda shak'uwar dake tsakanin zuciyarta da Asp, haka aka shiga da ita Emergency room inda likitoci  sukayi cha akanta anata iyakar kok'ari haka Raina ke leken Yadda Goggo ke burari waiyo kawai takecewa babu alaman Rahma a tattare da jikinta bare sauki Babu Adu'a bare salati saboda mugun abunta daman karshen azzalumi kenan mutuwar Fuji'a mutuwar gaggawa Asiri Goggo, Zina Goggo, makirci Goggo, zalunci Goggo abun yayi mata yawa wai shege da hauka, Itadai RAINA fatanta Goggo tasamu sauki donta sanar da ita tushenta koh kuma Asalinta........

Bayan wasu awowine Goggo ta Umurci dason ganin RAINA haka ASP yakirata tafe take hawaye na k'waranya acikin gurbin idanunta tana zuwa ta rungume Goggo tace
“Allah yabaki lafya Goggo kece abar Kallo inji dadii karki mutu kinji”
Dariya Goggo tayi Wanda bata taba irin taba tace cikin Murya k'asa k'asa
“Raina mutuwa tazama dole Kuma nan bada jimawaba zan bakunci inda kowa saiyaje kiyafemun Saboda nayi miki laifi wanda girmansa yana iya wuce dutsen Mambilan”
Tuni Asp *Ahmad yari* yadauko Biro da takadda saboda ya dauki Statement din Goggo
Taci gaba dacewa
“RAINA ke yar Gata ce gaba da baya Duk wani kaskanci Nina jawo miki dana rabaki da iyayenki alokacin dasuke matuk'ar bukatanki Sunanan na Asali Binta kuma ni kuyanga ce acikin masarautar mahaifinki Wato *Sarki MAMUDA* Saboda tsabar makircina Yasa na saceki adaidai lokacin da Mahaifiyarki Maimuna ta haifeki Mahaifinki yafi kowa bakinciki Haka naji labari har ciwon hawan jini gareshi itako mahaifiyarki saboda kuka idanunta basu buduwa sun shiga matsanancin rayuwa wanda nake fata ki rokanmun su Alfarma su yafemun”
Raina da ASP dama likitoci sunyi masifar razana kallon Raina kawai sukeyi saboda ga kamanan wacce bata boyuwa Goggo taci gaba da labari...................

RAINA (The beautiful princess)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang