RAINA (the beautiful princess) BABI NA TALATIN

3.7K 153 89
                                    

*146-150* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BY HUMAIRAH (Melody)*_

 

BABI NA TALATIN

_*Wannan page nakune yan group dina Wato Melody novel group Allah ysbar zumunchi yabar kauna LYSM😘😍*_

Ai da gudu ta wuce cikin gida tana kuka washe gari Aka daura auren DANISH DA RAINA a babban masallacin dake kofar gidan Sarki MAMUDA inda manyan Mutane suka halatta daurin auren ciki harda sarki KAMAL Wanda shima sarkine Wanda ake jidasu a fadin Nigeria, Gida sai hidima akeyi Sarauniya Maimuna kuwa bakinta har baka gida yacika da jinin sarauta takoh ina harma jinin mulki ni humairah saida nagani abun masha Allah Amarya da Ango sunyi kyau Unaiza saboda bak'in ciki kamar zatayi kashi ajiki babu kowa a bangarenta saboda kowa ganin laifinta yakeyi dabata hana danish aure ba tafita zakka cikin yayan gidan Ambassador MB shehu, Misalin karfe uku ne aka wuceda Amarya nata sashen a al'adarsu mace bata Sallar La'asar a gidan iyayenta sai a gidan miji Nidai saboda tsabar son ganin Dakin amarya mai karatu saida naci tuntube, A gaskiya RAINA tazama ya mai gata mai yanci duniyace tayi mata kamun kaxan kuku lokacin datake matukar buk'atan iyayenta a kusa da ita babune babu acikin bangarenta yaji kaysn kwaliya na zamani wani bangaren na yar saurauta kirari kawai ake mata
*Yar Sarki jikar sarki yar sarauniya Maimuna takawarki lafya Allah yakara ma Yarima Danish lafiya Allah ya tsole idon makiya mahassadanki fadawanki kyakkyawar Gimbiya tun kan zuwanki duniya akasa miki suna kikazo duniya sunan yabiki Duniya Mai yadda yaso da bawa ke macece mai kamar maxa masu irin imaninki sai an tona Allah yasa muji albishir mai dadi Uwar yan biyu in Allah ya yarda*
Tunda Jakadiya tace yan biyu raina taji wani mugun faduwan gaba yaranta kawai ta tuna amma tasan yanzu sun zama na wasu bata burin karbarsu Amma tanajin irin sonda take musu har kokon zuciyarta kuka kawai tasaki Wanda babu Wanda yasan dalili.

Bayan an shiga da itane aka gama yan Al'adarsu ta masarautan kajuru, daga bisani akabarta daga ita sai jakadiyarta sai kuyangu tunda dole tasamu jakadiya saboda tazama matar aure al'adarsu, Zaune take bisa katon gado Wanda yasha ado Royal bed ne Wanda kansa ya kusa rabi da k'watan bango sai fifita ake mata misalin karfe Goman dare lokacin da Danish yadawo abun mamaki tana zaton inda take zaizo amma saitaga Akasin haka Jakadiyace tashigo hannunta rikeda wasu kayan bacci masu kyau da tsada
“Gimbiya kitashi kisa wayannan kayan muje in rakaki wajen Mai girma yarima” cikeda mamaki baki bude raina tace
“Jakadiyya kinada hankali kuwa? Mutum yana sonka yaka k'are dashi bare kuma bayasonka kakai kanka? Nifa bazansaba inace miji kebin mace har dakinta?” ta zunburo baki ta mike ta nade hannu tana kai gwaro takai mari, jakadiya ce a durkushe tafara magana cikin siga mai kashe jiki Nanta labartawa RAINA irin rayuwar Auren
“Gimbiyata mai zai hana mu gwada tamu baseerar saboda gani yake matan duk saya suke kije Gimbiya ta kidaure har hakarmu ta cimma ruwa” haka raina ta shirya cikin kayan ta sanya Alkyabba suka kama hanya jakadiya daga kofa ta koma RAINA kuwa gabanta sai dukan goma goma yake, tayi minti biyu a tsaye kannan ta zauna a gefen gado da alaman mutum a cikin Dakin cire Alkyabba tayi ta kwanta ta juyawa toilet din Dakin baya tasan duk yadda akayi wanka yakeyi.

Tanajin motsi tayi saurin rufe ido DANISH daya fito saura kadan ya arta a guje saboda bai taba ganin mace mai kira irinta RAINA ba, lokaci guda ya gusar da tunanin hakan a ransa yana Neman tsari da shaidan din sake Neman yin tasiri acikin Ransa Juyowa RAINA tayi tace  “Barka da fitowa ranka ya Dade yayana yarima mai jiran gado Allah yabaka sarki ka nadani Sarauniyar masarautanka” tafadi tana murmushi ta sakko mai yake shafawa tayi saurin amsa cikeda kissa zata shafa masa tunda wani darene jemage bai ganiba dakatar da ita yayi yace
“Malam bansakiba banason Shishigi maxa ki tashi daga gabana kafin inyi ball dake ” RAINA tayi saurin dagowa takasa cewa komai ba laifin Wanda take gani sai nata dana jakadiyya bakin gado takoma sai satar kallonta yakeyi
Barcine tayi awon gaba da ita shiko sai daukanta hoto yakeyi yadda tayi masifan kyau cikin silk milk din kayan baccin amma fah yarasa meyasashi daukan hotonta *Koh me karatu yasani?*misalin karfe biyu da rabi raina ta tashi DANISH dai motsi yaji Alwala tayi ta shimfida sallaya ta dubi gabas tafara kiyamun lai Shiko Yarima Danish kallonta kawai yakeyi wai daman RAINA tana sallah? Tsmbayar kansa yakeyi nida mai karstu mukace Ah ah Batayi tunda Kaine kadai musulmi a duniya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 16, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now