RAINA(the beautiful princess) BABI NA BAKWAI

1.2K 58 0
                                    

*26-30         RAINA*
*(The beautiful princess)*

_*STORY & WRITTEN BY*_

© *HUMAIRAH (Melody)*



*BABI NA BAKWAI*

Hankalinsa yayi k'ololuwan tashi,

     Aii bai tsaya bata lokaci koh Neman shawaran wani ba ya d'ebi yan fad'ansa sukayi musu diran mik'iya,

    Sallama suketa kwad'awa amma shuru kakeji Inna tana labe taga ko waye amma taki ta amsa saida taga suna niyyan shigo mata gida tayi sauri tafito koh mayafi,

         Tuni ta zube a kasa tana kwasar gaisuwa “Dakata tsohuwar najadu, tsohuwar karuwa, makira addababba,

     Kina tunanin Duk ayar da kike shek'ewa keda yarki banida labarune? Toh kin yaudari kanki kuma saikin bar Garinnan keda shegiyar yar taki Marar uba yar kwararo,

       Ina akuya zata da kayan tankai me zuwan biri da gada Dana baxai auri yar ki ba koda itace autar mata kisani, Duk wani bin boka dabin malamai nasan babu Wanda baki iyaba toh ahir d'inki akan D'ana,

     Kun me damun da saniyar tatsa dakeda shegiyar yarki Duk kun cinye mishi jari saboda son abun duniya toh koh Duk ranarda naga Fu'ad da RAINA take kowa sainayi holi daku daga garinnan, dayawa mutane suna kawomun k'ararki saboda fadanki da rashin mutuncinki inazan hada zuri'a daku mutanen da ba'asan Asalinku ba, nan kikaxo Allah annabi nabaki guri Ashe a kaina zaki kare”

     Yana gama magana ya wuce batareda ya saurari Goggo yalwa ba.

       Tsaye tayi tana maida numfashi Niko mezanyi banda dariya Ashe gaba da gabanta Aljani ya taka wuta, ciki gida ta koma taga RAINA zaune tanata razgan kuka babu ji babu gani sai sheshek'a takeyi,

       “Lafiya kike kuka? Indai akan Fu'ad ne karkisawa kanki damuwa tunda kinadani kin gama samum komai mai gari dani yake Batu yanzu wajen ALU zani ya rufemun bakin shegu saidai suga yana bauta mana basuda ikon magana”

    Sai a lokacin raina tayi murmushi taji dadi Fu'ad shine namijin daya fara furta mata kallaman *LOVE* shiyasa take ganin shine karshen maganarta, shi takeso ta aura Duk runtsi amma ina tana ganin ta makara saboda iyayensa sun fara nuna kyamarta a fili.

      “Yanzu ni narasa gane me Kalmar shegiya take nufi ance banida uba taya aka sameni nasan dai saida namiji ake haduwa asamu da toh ita Goggo a ina Tasha kodai a randa tasha?

     '''Ohh Allah magani ni RAINA ina cikin gararin rayuwa, bansan suwaye dangina ba gashi Goggo tak'i ta nunaman mahaifina koda baxai amsheni ba nasan k'ila dashi nake kama don babu wata kama danayi da Goggo”'''

Da wannan tunanin ta k'are har Gwaggo tadawo tace,

       “Maza kije ki daga wancan dutsen kisa layarnan” tana sawa sukaji sallama ana kiran RAINA lokaci guda bugun zuciyarta ta karu Goggo tace tana zuwa kace waye
Tashi tayi ta wanke fuskarta da tasha kuka ta mustsuka mai da hoda tafiya,

    Tsaye taga Fu'ad ya k'ure ta da kallo Wanda yake nuna tsantsar son da yake mata.

    “Raina inaji ajikina wani Abu yafaru karki  boyemun kisanar dani wallahi sai inda k'arfina yak'are, akan ki raina zan iya amfani da numfashina na karshe in yaki Duk Wanda ya keda niyyan bata miki rai.

      Shuru tayi tana kare masa kallo tace

     “Fu'ad kenan inajin wannan mutumin baxaka iya fito na fito dashiba saboda yagama maka komai a Rayuwa tunda ya kawo ka duniya, inajin watan rabuwarmu tazo saboda dazu yace bani bakai mezakayi da shegiya Mara uba kaskantacciya Irina katafi kar aje a gayamai ya koremu Dan bansan inda zamu dosaba danida Goggo ba”.

    Kuka takeyi sosai har saida tasa Fu'ad kuka saboda indai zata zubar da hawaye baiga abinda zai hana shi ya zubar da nashi hawayen ba,

     “Kiyi hak'uri ga wannan kiba Goggo hak'uri abubuwan sai a hankali ne jarin nawa duk ya narke ga kudin tara na gobe kiyi sammamako naji ance baki zuwa islamiyya toh kidage saboda anan ne zaki samu aljannanki”

          “toh” tace

Tashige gida shikuma ya wuce wajen IDI abokinsa donya sanar dashi abunda yake faruwa amma sai akasamu sabani bayanan,

      Haka ya karkata ya wuce gida fuskarsa babu koh walwala bare fara'a daki yashiga ya kwanta yafada kogin tunani tsaki,

      Yayi yace

     “Bahaushe mai ban haushi da uwarka da ubanka ya shegantaka mai makwan yace bada aure aka haifeka ba sai yace mata shege kuma abun haushi babu Wanda aka jeho daga sama wallahi wallahi aure danida RAINA babu fashi saidai mutuwa kamar daga sama yaji ance
“Saidai ka mutu don baxan hada zuri'a da yar maceba wacce batada asali wake daya shike bata gari Fu'ad wani irin makanta zuciyarka keyi ka amince ma waccan yarinyar toh kasani bakai ba ita kuma ka shirya nanda sati zan daura maka aure da marka koh kanaso koh bakaso”.

*EDITED BY SERDERYERH*😘


_*MELODY*_😍

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now