RAINA (The beautiful princess) BABI NA SHA HUDU

1K 40 0
                                    

*61-65* 👸🏻 *RAINA*
*(The beautiful princess)*👸🏻

©
_*STORY & WRITTEN BYHUMAIRAH (Melody)*_

BABI NA SHA HUDU




Inda mutumin nan bai saurareta ba haka suma yaransu suka dinga hayeta inta kaitawa mai karatu nidai gani nayi har numfashi raina batayi, bayan sun kammala ne suka dauketa cik suka sata cikin mota gudu kawai sukeyi babu alaman zasu tsaya, awata maraba suka tsaya suka turo RAINA waje suka k'ara gaba koh tausayi babu, haka rana tagama dukanta daga bisani ta farka da kyar take tafiya duk Wanda tagani saita daga mishi hannu amma ina duniya tazama abunda tazama babu maison taimako, ana yar tsoron tsoro.
Wani mutumine ya tsaya ganin halinda take ciki yayi matukar tausaya mata a yadda yaganta tana bukatar taimako,
“Yan mata lafya meya sameki haka”
Raina tayi karfin hali tace
“Fyade wasu mutane sukayimun shine na farka naganni a bakin dajinnan ka taimaka kakaini wajen Goggo na inma mutuwa zanyi in mutu a gabanta”
Mutumin achan kasan zuciyansa yace
Dubi yarinya wacce shekarunta basu wuci sha takwas ba amma an lalata mata Rayuwa kaico duniya Tabbas da yata akayiwa haka na tabbata mutuwa zanyi daganin wannan yarinyar dakwai nak'asu a rayuwarta wajen rashin samum isassan tarbiya daga iyayenta sannan da rashin kula da yayan da Allah yabasu don muyi Alfahari dasu.

Haka yataimaka mata tashiga cikin motan sannan ta gayamai inda zasu nufa Wato Zangon Mati, da shigarsu mutane sai kallon motar sukeyi cikeda tuhuma saboda motar bakin mudubi gareta, har kofar gida ya sauketa yashiga da ita Goggo na ganinsu tayi wata zabura tace
“Raina lafya ina kika shiga meya sameki haka”
Raina takasa magana illah kuka da takeyi maicin rai tasan cewa rayuwarta ta gama lalacewa,
“Goggo abakin hanya na samu yarki cikin bukatar taimako shine na daukota nizan wuce amma inaso Ku kula da baiwar da Allah yabaku saboda Allah zai tambayeku ranan gobe ” Goggo tayi magana Tuni ya fice nan raina tace
“Goggo duk kece silar lalacewar rayuwata a doron duniyannan kekika lalatani da son abun duniya har ya kaini ga sadaukar da rayuwanta amma tabbas namiji Dan kunama ne amma kuma tsakanina da namiji tamk'ar kifi da kaska zamu zama  kura da nama babu sauran sassauci tsakanina da namiji sannan sainayi silar rusa ma duk namijin da yashigo Rayuwa, duk Wanda yashiga tarkona Allah kadai zai fiddashi badai mutum ba” tana gama magana ta kara rushewa da kuka Wanda aranta tasa sai kowani namiji yayi kuka da ita dago idanunta tayi jajaye ta mike tayi waje bata zarce koh inaba sai inda zata ga Idi da Fu'ad tabasu hakuri, ilai ta aika yaro bata ce injita ba saboda tasan halin Idi yana iya cewa bazaizo ba,
Da isowarsa taji wani kyamar RAINA yakeyi
“Lafya naganki koh koh wani sharrin kika kullo in nemi tsari dake?”
“Ah ah Idi nazone kaya tani ba Fu'ad hakuri tabbas nasan ban kyauta mishi ba Dan Allah kataimakeni tabbas duniya ta rudeni Idi” dariya Idi yayi yakuma daure fuska.

“Raina kenan yau da iska ta kad'a gashi munga takashi kaza, kin makara kinzo lokacin jirgin ya d'aga, inda kinsan halinda kikabar Fu'ad na tabbata saikin tausaya masa saida aka hada da rokon Allah kannan yasamu kanshi, yanzu dai duk labari yakare Fu'ad yana kasar India saboda gwamnati ta kaishi karatu kuma daman cewa akayi yazo yatafi da matarsa kinga yanzu kin lashe bai tafi da mataba amma zai dawo nan bada jimawa ba, dazu jirginsu ya daga RAINA adinga Sara ana duban bakin gatari, kisani cewa duk kyau rakumin dawa bazai kaiga na gidaba”
Kafin tasamo abun cewa Tuni ya wuce ysbar ta tsaye da cizon yatsa, ai da gudu takoma gida koh zafi bataji tana shiga ta fad'a kan Goggo tana kuka sosai “Goggo nashiga uku inaxan sa kaina duniya nashiga uku meyasa rayuwata tazo da sabani kala kala, inhar jarabawa ce wannan inna yaci ace nafara cinta ba inta faduwa ba”
“Raina kaddara ce kidauka”
“Wane irin kaddara Goggo meyasa bataxo tuntuni ba sai yanzu tabbas nayi ladama akan wulakancin danayiwa Fu'ad nasan cewa baxai taba yafemun ba, nasan cewa Alhakinsa ne yake binmu”haka aka gama kakabi uncle Aymel dai yasha tsinuwa k'wando k'wando wajen Goggo haka ta gyra RAINA tadinga dafa mata sassaken baure da bagaruwa da ganyen magarya tana tsomata tana ihu haka akayi kwana bakwai kannan RAINA takoma daidai, tafara tafiya daidai, akaci gaba da rayuwa.

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now