RAINA (The beautiful princess) BABI NA GOMA

1.1K 47 0
                                    

*41-45        RAINA*
*(The beautiful princess)*

*STORY & WRITTEN BY*

© *HUMAIRAH (Melody)*

*BABI NA GOMA*

      Haka yaciro kudi yabata babu koh Jan aji bare godiya fita tayi tana mai mugun farinciki aranta Allah yakawo mata dauki
“Daganin Aymel Dan gidan masu hannu da shuni ne,

    Suna da k'umbar Susa aiko kamar Goggo taji irin wannan abun arziki hmmm ai Aymel soyayya dakai ba fashi me akeda wani Fu'ad shid'in banza”

''' _Niko humaira saida cikina ya murda nace gwarama kenan wannan shine Bankad'an,_'''

     Da gudu tashiga gida tana kwalawa Goggo kira haka tafito xane a hannu sai fatari sai lalitar boye kudi wacce akasawa suna MATA SUNWAYE,🤣

     “Lafya kiketa kirana saikace kin makance?”
Tsalle takeyi nonuwan suna sama suna k'asa
“Goggo hakarmu takusan cimma ruwa kinga wayannan kudin Uncle Aymel ne yabani wai insai sabulu in wanke kayana, kuma karya nayi Goggo rigarce ban ganiba”.

Tuni ta anshe kudin tace

      “Haka nakeso yata takaina ai ina gayamiki saimun tatseshi mun kwalkwale shi tsaf kannan zamu sakeshi yasha ruwa,

     Ki maza kije ki siyo mana nama muyi dagwargwajiya”
RAINA Tuni aka hau sukuwa da gudu taje tasiyo aranan su Goggo rai fes ba hawan jini ba ulcer bakincikin da namiji ya kwaranye,

   Da yamma lis Uncle aymel yazo ya aika aka kira RAINA ciki na kyarma ta mik'e zata zuba aguje,

     Goggo tadawo da ita ta dankwafar tace
“yau naji yar iskar yarinya sai wani sukuwa kikeyi saikace wacce tasha baliyon( kwayar doki) tashi ki gyra tafiya sannan kinatsu bakije kiyita magana kamar injin din markadeba, Dan farin ma kin daina da rangwada”.

  Ya mutsa fuska tayi tace “Haba Goggo inayi mana kema kinsani haka tafita tana rangaji, sunan wata haleema Rangaji, Aymel tagani tsaye ya harde hannun sa jingine da mota wani murmushi yasakar mata abunda ke kara fito da zunzurutun kyawunsa, Aymel kyakkyawa ne ajin karshe farine dogo amma ba kwarai ba idanunsa farare kal kamar madara,

  Bakinsa kam jawur tamkar yasa chougzuh wani jambakine da yan China suke sawa,
 
   Gashinsa luf luf kamar bakarabe Amma zuciyarsa batada wani Alkhairi illah sharri,

    Kuma haka yasamo Asaline daga wajen iyayensa ganin shikadai suka Haifa hakan yasa suka kasa bashi tarbiya ta kwarai,

     “Barka da fitowa ya ma'abociya k'yau da kwarjini, ganinki kadai yana Sani nishadi ganinki yanasani zama wani sarki,

   Murmushinki kadai yana sanyaya zuciyana” dariya tayi taji wani ni'ima ya ziyarceta takasa boye farin cikinta ga hak'oran ta jawur sai doyi yakeyi banda kaxanta babu abunda Raina bata taraba duk talauci ai tasa gawayi da gishiri ta gurje bakin don haushi har na juya zan tafi naji muryar,

     Aymel yana cewa

_“will you marry me”?_

Wani abune ya doki kunnena nayi saurin juyowa kafin yaci gaba da magana
“RAINA kisoni Kiga gata kisoni Kiga yadda duniya zata sanki cikin k'ank'anin lokaci,

Mahaifina gawur taccen mai arzik'ine gidajen mansa sunfi a k'irga duk sati a makka muke ummra duka gidanmu, sannan yace innemi kowacce yarinya zai auramun ita duk talaucin su don haka ki aminche in daukeki in kaiki birni ki gaida iyayena ”

Nidai ina tsaye Nace wannan shine Zubit din amma Dana duba fuskan RAINA sai naga gaba daya ta rude chan kuma naga ta bata rai duban daxan kara mata naga ta turbube fuska,

“Uncle Kaine mutum na biyu daka taba cewa kana sona bazan iya cewa ah ah ba amma akwai kudin aurena da Fu'ad,

   Basan yadda zanyiba kusan shekara biyu babushi babu labarinsa amma inaso kabani daga yau zuwa gobe zanyi shawara”

   Sallama suka yi ya d'auko kud'i naira Dubu goma yaba ta,

     Hannu na rawa koh godiya tana juyawa Aymel yace

    “Hmmm nagane laggon Ku kunada son abun duniya, toh kashin ku saura kad'an ya bushe don saina fanshe kud'ina ajikin ki RAINA”

_*Gwarama kenan muje zuwa...........*_👌🏻

_*MELODY*_😍

RAINA (The beautiful princess)Where stories live. Discover now