FAIROOZ LITTAFI NA FARKO

1.3K 100 13
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

FAIROOZ!

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar✍️

Babi na farko.

BISMILLAHIRRAHMANIR-RAHEEM

Daddad'ar iska ce take kad'awa cikin sanyin safiyar ranar Laraba wanda masu iya magana kewa kirari da Laraba tabawa ranar samu.

Kishinged'e take kan kujera mai kama da gado, yayin da iska ke kad'awa da siraran gashin da suka zubo a gefen goshinta.

Cike take da farin ciki tare da nishad'in, ganin cewa yau ta yi nasarar d'auko LITTAFIN da kullum Mahifinta ke mata shamaki a kansa. Tana sa ran yau lallai zata ga abin da ya dad'e yana b'oyemata a cikinsa!.

      MARYAM kenan 'ya a gurin Malam Hafiz, shahararren Malami mai bincike a kan a bin da ya shafi TARIHI na Duniya.

Maryam ita ce 'ya d'aya tilo a gunsa bata san kowa ba sai Mahaifinta. Kasancewar a daji suke da zama. Tun bayan kammala karatunta suka tattara komai nasu suka koma cikin daji, ita kanta ta rasa dalilin aikata hakan daga wajen Mahaifinta!.

Mahaifiyarta tun bayan haihuwarta ta rasu. Wannan shi ne dalilin da yasa bata san kowa ba sai tarin littattafan Babanta wanda a kullum yake cikin aikin nazarce-nazarce dasu. Maryam tana da ikon tab'a duk littafin data ga dama a cikin d'akin karatun Babanta, sai dai akwai littafi d'aya daya hanata tab'awa wanda iya abin da take iya hange a jikinsa shi ne wasu zane da a kayi da wasu launika guda uku. Red, blue and green(wato launin ja, shud'i da kuma kore).

Amma sai dai ba ta iya fahimtar abin da aka rubuta da sauran launinka ba, face rubutun k'arshen da aka yi sa da manyan bak'i FAIROOOZ......shine abin da take iya ganewa a jikin littafin.

Yadda aka yi har Maryam ta sami nasarar d'auko wannan littafin sirrin baban nata a yau shine.

Ya kasance a duk ranar laraba ta duniya Maryam takan gyarawa Mahaifinta cikin d'akinsa ko'ina da ina, kasantuwar Malam Hafiz yakan bar gida ya shiga daji, in ya tafi tun safe sai yamma yake dawowa, duk da tilon 'yar tasa tayi-tayi akan ita ma ya rink'a zuwa da ita ko ba kullum ba, amma Sam! yak'i amincewa, ta kuma rasa dalilinsa a kan hakan.

Tun tana jin tsoro idan ya tafi ya barta har tazo ta sabar ma kanta, shine dalilin kuma da yasa takan yi gyare-gyaren kowane sak'o da lungu na ciki gidan idan baya nan.

Yau ma ta kasance ranar Laraba ce, kamar kowane mako yadda ta saba yi, ta kammala gyara ko ina sai d'akin littattafansa kad'ai ya rage.

Inda ta shiga ta fara goggoge littattafansa wad'an da suka yi k'ura, tana cikin haka kwatsam! Saita hango wani k'aton akwati akan tebur wanda yaja hankalinta ga barin goge gogen data keyi.

K'arasawa tayi daidai kan tebur d'in. Akwatine gashi nan duk k'ura ya b'ata shi.

Sai ta sanya hannuta ta d'an share samansa a hankali, Nan take kuwa wani haske ya fara bayyana akan saman akwatin wanda tsananin fitar hasken yasa dole sai da taja baya.

Bayan b'acewar hasken da 'yan wasu dak'iku, wasu manya manyan zanen rubutu ne suka fito b'aro b'aro kala d'aya sak! Da launikan rubutun nan da ta ke gani a jikin (littafin SIRRI na Babanta) kamar yadda take kiran littafin a wajenta!.

Ba wasu launika bane, face kalar nan na red, blue & green (launin ja, shudi, da Kore) Har' ila yau ma, rubutun na k'asan wancan littafin shi ta k'ara gani, rubutu ne da manyan baki ya fito kamar na littafin nan data ke son bud'ewa FAIROOOZ............taga an rubuta ajikin akwatin.

Daga k'asan sunan kuma wani d'an kogon rami ne mai madanni, wanda ga dukkan alamu nan ne wajen mabud'in akwatin.

Maryam da karambani, tasa d'an yatsarta a daidai saitin ramin dake jikin madanni ta danna nan take akwatin ya fara darewa gida biyu!.

Wani kyakkyawan takobi ta fara yin tozali dashi, yana shek'i da haske daga tsakiyar cikin akwatin, daga gefe guda kuma kwari ne da baka, sai sulke sannan da wani d'an k'aramin akwati mai yanayi kamar daidai da girman littafi.

Hannu tasa kan k'aramin akwatin ta d'auko shi, ba tare da yin wani dogon tunani ba ta bud'e....jikinta sai rawa yake yi domin ta san lallai yau ba k'aramin karambani tayi ba, na tab'awa Mahaifinta akwatin sirrinshi.

Bude k'aramin akwatin da tayi, idanuwanta suka gane mata wani sabon littafi fes dashi! Wanda bashi da maraba da irin wanda Mahaifinta ke hanata d'auka cikin tarin littattafansa, domin gani tayi komai na jikin littafin iri d'aya ne, shi ma wannan har da rubutun nan masu launin ja, shudi da kuma Kore.

Cike da farin ciki ta sanya hannunta gami da ciro littafin daga akwatinsa, har zata rufe akwatin sai idon ta yakai kan wani kyakkyawan k'yalle mai launin fari da ja, wanda ya burgeta sosai, shi ma a cikin d'an k'aramin akwatin yake.

Hannunta ta sanya ta d'auko kyallen, ta kara shi a hancinta wani tattausan k'amshi mai sanyi ne ya shiga ratsa illahirin duka k'ofofin shak'ar iskarta, uhhhmm......... ta shak'i k'amshin tare da lumshe idanuwanta.

A hankali ta bud'e idanuwanta, tana jin wani sabon yanayi a tare da ita, maida d'an karamin akwatin littafin ta yi ta ajje.

Sai kuma ta fara tunanin 'Yanzu idan Baba ya dawo kuma fa! Ya zanyi in yazo ya fahimci cewa na bud'e wannan akwatin!?'

Akwatin da kwata-kwata bata tab'a sanin dashi ba, domin idan ya fita duk iya dube-duben da take yi cikin d'akin bata tab'a ganinsa ba. Sai gashi yau yayi kuskuren barinshi a fili, har ita kuma ta shiga ta bud'e masa akwatin sirrinsa!.

Tsaye ta yi jim, na wani d'an lokaci. Kafin ta ci gaba da zancen zucin da take yi

'Na san lallai dai duk yadda aka yi mantawa ya yi yabar wannan babban abu mai mahimmancin gaske a wurinsa, idan ba mantuwa ba, babu abin da zaisa Baba ya bar akwatin nan waje, balle har ni kuma na kai ga samun damar d'aukar abin da nake matuk'ar muradin son ganin ko me ke cikinsa. Wato littafin nan mai suna FAIROOZ!'

Sai ta rungume littafin a k'irjinta, tana lumshe Idanuwanta.

"Dole nasan abin yi, kafin Baba ya dawo ya fahimci abin da aikata!'' Ta fad'a a fili.

Ayshnur Pyar💗

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Onde histórias criam vida. Descubra agora