FAIROOZ
Daga Alk'alamin Ashnur pyaar✍️
BABI NA SHA BIYAR
BAYAN SHEKARA TALATIN.
Hafeez ya zama cikakken _*historiology*_ mai ilimi a fannin da ya shafi tarihi ya yinda shi kuma Abbas ya zama *Medical Doctor* Cikakken likita.
Bayan kammala karatun nasu ne kuma aka d’aura masu aure da kyawawan ‘yan Matan da suka zab’o, wanda dama tuni suka dad'e da k’ulla alk'awarin Aure a tsakaninsu.
Hafeez ya sami Matarsa wacce ake kira da Zeenat Aman 'yar k'anwar Matar Harukhan, Abbas Kuma Darweesha Shehu, ita kuma 'ya ce a wajen abokin Harukhan, dukansu Indiawa.
Ranar bikin kam an sha shagali, bayan d’aurin aure aka kai kowacce cikin d’akinta, aka barsu daga su sai angwayensu.
Ko da Yusuf yaga ‘ya’yansa sun sami ilmi mai inganci gashi kuma har sun kai ga munzulin yin Aure! Shi kuma ga tsufa ta fara cimmasa sai yayi niyar sadasu da ainihin Mahaifarshi Nigeria, domin su san asalin gida ko da ta Allah ta kasance.
Ya sanar da amintaccen abokinsa Harukhan, nan take ya karb’i wannan shawara tashi domin ganin dacewarta, sai dai a gefe guda ya nuna jimaminsa k’warai na wannan rabuwa da za suyi.
An sanya ranar da zasu koma gida Nigeria daga India bayan bikinsu da wata d’aya, ranar kuwa nayi suka biyo jirgi sai k’asar gado Nigeria.
Bayan komawarsu, babban fili Mahaifinsu ya siya aka yi ginin gida gini na musamman, don filin da aka ware wajen yin ginin gidan, za’a iya sake yin wasu gidaje a cikinsa, ba tare da an takura ba.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Детектив / ТриллерTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...