BABI NA SHA BIYU

501 41 13
                                    

                 

          
        FAIROOZ

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar✍🏻

     BABI NA SHA BIYU

Bayan Maryam ta rama sallolin dake kanta duka ta idar, ta d’aga hannuwanta sama tana rok’on Ubangiji, muryarta a bayyane take fad’in.

“Ya Ubangijina Allah! Kaine Mahaliccin sammai da k’assai kai kad’ai ke da iko akan komai daka halitta.

*MUTUM DA ALJAN* mu duka *halittarka ne*! Ina rok’onka ya Allah, da ka bayyanamin wannan b’oyayyen al'amari dake faruwa dani, ya Allah ka ganar dani duniyar da nake ciki! da kuma inda nake a yanzu, da dalilin zuwana, ka kuma taimake ni ka bani ikon komawa gida gun Abbana......''

Kuka sosai take yi, lokacin da ta ambaci sunan Mahaifinta.

Ta ci gaba da cewa,

“Ya Allah a duk halin da Abbana yake ciki dalilin rashina, ka sanya masa nutsuwa da sassauci cikin zuciyarsa, ka kuma fitar dani daga wannan sark’ak’iyar dana jefa kaina ciki!."

Haka Maryam ta d’au dogon lokaci mai tsawo tana ta Addu'a! Sannan ta shafa.

Ta d’an jima zaune a wurin da ta yi sallar, kafin ta m’ike tana mai yin hamdala ga Allah mad'aukakin sarki, domin ko ba komai taji ta sami nutsuwa cikin zuciyarta.

Tafiya take sannu a hankali, ya yin da iskar lambun ke kad’awa da lallausan bak'in gashin kanta, wanda ya fito ta jikin mayafinta.

Duk wannan badak’alar da tasha gashinta yana nan da shek'insa, sai dai d’an k'ura kawai da ba za a rasa ba.

Cikin lambun ta shiga sosai tana zazzagawa, inda a k'arshe ta tsinko wasu ‘ya’yan itatuwa.

K’oramar nan ta d’azu ta koma, ta wanke su fes!.

Daga nan ta koma zuwa cikin wannan rumfar da ta hango d'azu lokacin da tunanin k'aramar yarinyar nan ya gifta cikin k'wak'walwarta.

Daidai saitin wasu kujeru biyu masu fuskantar juna ta tsaya, nan take ta tuno da Fairooz d’inta! Kamar yadda ta sanya masa suna.

Janyo kujera guda d’aya tayi ta zauna, sannan ta fara cin 'yan'yan itatuwan da ta tsinko, ko za ta samu su yi mata maganin yunwar da take ji.

Tana kammala shan fruits d’in, ta koma bakin k’oramar nan, inda ta sake d’ibar ruwan cikinsa ta wanke hannayenta a gefe guda.

Sannan ta sha ruwan tayi hamdala ga sarki Allah.

Ta koma bakin runfar tana wasu ‘yan tunane-tunane cikin zuciyarta, can sai ta ji sha’awar komawa bakin swimming pool d’in nan na d'azu, ko za ta samu ta d’an d'auraye jikinta.

Hakan kuwa tayi, bayan ta koma wurin kwamin wankan, ta d’auraye wuraren da take so a jikinta, sannan ta zauna daga bakin pool d’in.

Kallon ruwan take cike da sha'awa, inda a hankali ta d’an zirara k’afafuwanta tana k’arkad'a su cikin ruwan.

Wal! Wannan abin mai haske ya sake gittawa ta cikin k’wak’walwarta, da sauri Maryam ta kama kanta, ya yin da wani sabon hoto ya sake bayyana k’arara a cikin k'wak'walwarta.

Kamar d’azu k’aramar yarinyar nan ce wacce ba za ta wuce shekara sha biyu ba, tare da wannan saurayin wanda a k’alla zai iya kai kimanin shekaru ashirin da bakwai, su ta sake gani a  bakin swimming pool d’in, wanda take zaune ita ma a gefensa daidai wannan lokacin!.

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Where stories live. Discover now