FAIROOOZ
Babi Na Bakwai.''Yeih Fairoooz koun hei! Yeih sab kya hei? (Wai shin wanene wannan FAIROOZ d'in? Me wad'an nan abubuwan duka suke nufi!?'' Maryam ce duk ta fad’i haka cikin harshen indianci, muryarta kamar za ta yi kuka, kana kallon fuskarta za ka ga tsantsar rud’ani gami da tashin hankali!.
A hankali Maryam ta tashi daga inda take zaune. Dalilin wata hanya da ta hango.
Hanyar ta doshi wani makeken gida, wanda ke can gaba da inda rumfar da taso yake.
Wanda kwata-kwata da Idanuwanta basu hango mata wannan gidan ba.
Kafin Maryam ta k’arasa ga k’ofar gidan, sai kuma ta tsaya cak! Tana shawara.
'Ta k’arasa ne ko kuma ta tsaya, shin idan taje yanzu ta shiga gidan ta san gidan wanene? Kuma ba ta san menene a cikin gidan ba!'
Tana nan tsaye dab da k’ofar gidan, daga inda take tsaye tana iya hangen d’an mak’ulli da aka sagale a jikin k'ofar, da alama shine mabud’in shiga cikin gidan.
Maryam na nan tsaye tana ci gaba da tsake-tsakenta, ba ta kai ga yanke shawarar abin yi ba, kamar daga sama sai taji ance,
"INA ZAKI KUMA?''
Da saurinta, ta juyo dan ganin mai maganar.
Kyakkyawan saurayin nan ne ma’abocin murmushi ta sake gani yana yi mata murmushinsa.
''Ina zuwa haka da sauranki ta fairoooz!?”
Ya sake fad’i cikin murya mai taushi.
Dubawan da Maryam za ta sake yi sai ta ga wayaaam! Babu wannan gidan da take harin zuwa.
'Yanzu-yanzu nan kenan shima ya bace, babu shi babu alamarsa?' Ta tambayi kanta.
Cikin tsoro da firgici ta sake dawo da dubanta ga kyawawan saurayin, kafin tace wani abu ya rigata yin magana.
''Ya aka yi ke dana bari cin Abinci kuma shine kika taso zuwa nan! Shin kinsan ina ne nan kika zo kuwa?''
Cikin muryar kuka Maryam tace, ''Don Allah bawan Allah kai wa Allah ka daina razanar dani, ka taimakeni ka fad’amin ko kai wanene? Kuma waya kawo ni wannan duniyar!?”
Sunkuyo da kansa ya yi dai dai fuskarta, ta yadda har suna iya jin saukar numfashin juna.
"D’ago idanunki ki kalleni, tun da kince Allah!''.
Ba ta musawa umurninsa ba, cikin sauri ta d’ago da kyawawan fararen idanuwanta, ta saukesu a cikin nasa. Wani irin abu yarrrrr taji a jikinta.
Yace, "Sunana FAIROOOZ ibn ABBAS! Idan kina muradin son jin cikakken labarin koni wanene, sai kin saki jikinki dani, bazan cutar da ke ba, kin ji?”
“To...h.” Ta amsa mishi cikin raunatacciyar murya me d'auke da sautin kuka.
''Taho muje kici Abinci kin ji, na san yunwa kike ji sosai, ga shi karambani bai bari kinci Abincin dana bar miki ba, kuma na san baki yi sallah ba, ko da yake kina cikin fashin sallah kwanakin da suka wuce, amma yau ai kin fara kafin ki shigo nan."
Cikin mamaki Maryam ta d’ago kanta!.
Aiko tana d’agowa suka had'a idanu, Fairoooz ya kanne mata ido d’aya, a lokaci guda kuma ya haskata da wani kyakkyawan murmushi. Cikin sauri Maryam ta sa hannu ta rufe idanuwanta.
Haka kawai sai taji ta tsinci kanta cikin jin matsanancin kunyarsa, wani nauyinsa ya saukar mata, sannan ga wani sabon yanayi da ta soma tsintar kanta ciki game da wannan kyakkyawan saurayi mai k’warjini da haiba, wanda har yanzu ba ta san cikakken wanene shi ba!.
''Tunanin me kike yi? Na ce ki taho muje ko!?''
Firgigit Maryam ta sake yi, dalilin farkawar da ta yi, daga kogin begen da ta shiga.
Cikin nutsuwa suka fara tafiya, har suka k’arasa ga rumfar alfarman dake d’auke da kayan Abincin da ta bari a d'azu.
Yanzu ma sake zama sukayi suna masu fuskantar juna.
Ganin bata ce komai ba sannan kuma tak’i tab’a wani abu daga cikin jerin tarin Abincin dake gabansu, shi ya sanya Fairoooz yin Bismillah, ya fara cin Abincin, wanda ko da Mutum Ashirin ne suka taru wurin kowa zaici ya k'oshi, ba tare da sun iya cinyewa duka ba.
“Kici Abinci nace, ba na son maimaita magana fa fiye da sau d’aya! Gashi ke nayi maki magana yanzu ya kai sau uku.''
Sai da ya lumshe Idanuwansa, sannan yace,
''Kawai idan na yi magana ayi abin da nace.!”
Maganarsa ta sake dawo da Maryam daga duniyar wasi-wasin da zuciyarta ke ciki.
Tunani ta keta sak’awa tana warwarewa, tambayar kanta take 'Shin ta ci Abincin nan ne ko kar taci?
Gashi dai ina jin yunwa sosai, sai dai ban san ainihin daga inda aka samo wad'an nan Abincin ba, shin yanzu idan naci, Abincin Mutane ne naci ko na ALJANU? Sannan FAIROOOZ Mutum ne shi ko kuma AlJANI?"
''Kibar tunanin da kike yi tukunna, ki daure ki ci Abincin, idan kin gama ci zan miki bayani, na san akwai tambayoyi masu yawa k’unshe cikin zuciyarki.
Sannan ina buk’atarki da ki daure ki saki jikinki dani, ki d’auka cewa tamkar mun dad’e da sanin juna ni da ke, idan kin yi k'ok'ari kin gama ne, sa’annan sai na fad’a maki ko Abincin na su waye? Da kuma wanene Fairoooz d’in naki!.”
Kallonsa ta kuma yi da sauri, tana mai mamakin yadda a ka yi yasan abin da take tunani cikin zuciyarta.
Suna sake had’a idanu sai ya kanne mata ido d’aya, ''Kinsan ni mallakinki ne ke kuma tawa ce!”.
Sai da ya d’an dakata, tare da sauke numfashi a hankali, sannan ya d’ora da cewa, “Na san tambayar da za ki yi min shine, ya aka yi nasan abin da kike sak’awa cikin zuciyarki? To ka da ki yi mamaki a kan hakan, domin ni ke da mulkin zuciyarki! Ni muradin zuciyarki ce! Nine masoyinki na hak’ika, kinsan da ni dake soyayyace ta gaskiya a tsakaninmu, Allah ne ya had’a soyayyarmu tun muna K'ANANA. Saboda haka komai naki nawa ne, nawa kuma naki ne, har da tunaninki ma duka mallakina ne, musamman kuma ma yadda ya kasance a kaina kike tunanin naki!''.
Maryam da dai taga babu sarki sai Allah. Ga kuma kalamai masu rikirkita tunani da Fairoooz ke ta jero mata, tamkar yana son ta tuno wani abu, ita kuma Allah ya sani bata tuno komai!.
Sai ta yi Bismilla kawai ta fara cin Abincin.
'Tun da na ga alamar kamar yana sona, nasan ba zai cutar dani ba. Kuma kowa ya dogara ga Allah to ya isar masa a kan komai!'.
Cikin zuciyarta take wannan zancen.
Ashnur pyar❤
naam hei mera.Don't forget to vote✌🏻nd comment🙌🏻

YOU ARE READING
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Mystery / ThrillerTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...