FAIROOZ
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
Babi Na Hud'u
Ga mamakin Maryam sai ganin kanta tayi ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce muke ciki!.
Domin duniyar da ta tsinci kanta, ko da ta duba sararin samaniyan-sa saita gansa launin green da blue ( kore da shuɗi) sharrrr....
Maryam ta duba inda take gaba da baya, gabas da yamma, ba ta ga kowa ba.
Daga can gefe guda kuma ta hango littafin da take kallon hotuna cikinsa yana nan kamar yadda yake bai canza daga shafin da ta buɗe ba.
"Ikon Allah! ta ya aka yi nazo nan kuma? Wannan wace irin duniya ce!?""
A lokaci ɗaya kuma tsoro ya ziyarci zuciyarta, nan take ta fara karanto Addu'oi a bakinta, bakin nata har rawa yake yi saboda tsoro da firgicin da ta ji sun hana ta sak'at.
Bata jima tana tasbihi ga rabbussamawati ba! taji wata 'yar nutsuwa ta shigeta, nan take ta ji ta sami k'warin gwiwa sosai!.
Tafiya ta fara yi zuwa inda ta hango littafinta, tana zuwa daidai wurin ta kai hannu domin ta d'auka, sai littafin ya matsa daga inda yake, ta sake kai hannu karo na biyu nan ma littafin ya sake matsawa, ba tare da kuma ta ga wanda yake taɓa littafin ba. Zuwa yanzu Maryam taji tsoro yayi k'aura daga zuciyarta, dan haka sai ta ci gaba da bin littafin.
Babban burinta kawai shine ta samu damar rik'e littafin a hannunta, ko da Allah zai sanya taga hanyar da littafin zai maida ita duniyar da ta baro.
Bin LITTAFIN Maryam ta ci gaba da yi, amma har ila yau bai tsaya ba, tana cikin haka ne taga littafin ya bi wata hanya, ya shige cikin duhuwan wasu bishiyoyi. Dai-dai da irin wad'an da ta gani a hotun dake cikin littafin me sunan FAIROOZ!.
Ba ta tsaya yin wani dogon tunani ba, ita ma ta shige cikin duhuwar da ta ga littafin ya shige, wanda har yanzu ba ta san wanene ke janye littafin yake tafiya da kanshi ba.
Addu'a ta ci gaba da yi har ta shige gaba d'aya cikin duhuwar, anan ne kuma ta nemi littafin ta rasa babu shi babu alamarsa.
Ita kanta ba ta iya ganin ko da tafin hannunta, bare kuma littafin da ta biyo cikin wurin.
"A'a! Lallai yau ni dai na san na d'ibo ruwan dafa kaina". Maryam ta fad'a a fili.
Kamar walk'iya kuma, sai taga haske faal! ya mamaye gun a lokaci d'aya, ba tare da ganin wanda ya kunna hasken ba.
Faruwar hakan ke da wuya, ta hango wani d'an k'aramin zomo, amma kalar jikinsa a madadin fari, sai ta ganshi blue da green (shud'i da kore). Kama baki ta yi.
"Wannan shi kuma wani irin zomo ne haka?.'' Kafin Maryam ta gama mamakin kalar dake jikin zomon da ta gani, sai ta hango zomon ya doshi wata hanya da 'yan tsalle-tsalle irin nasu, ba tare da b'ata lokaci ba ita ma tabi bayansa, a zuciyarta tana tunanin k'ila ko zata samu hanyar fita daga wannan sabuwar duniyar da ta tsinci kanta ciki.
D'an zomon nan na zuwa wata k'ofa sai ya jingina da jikin k'ofar, hakan na faruwa sai gani tayi ya b'ace, babu shi babu alamarsa.
Ita ma ba ta yi wata- wata ba, ko jiran yin shawarar komai ba, taje ta jingina da k'ofar irin yadda zomon yayi itama tayi tareda fad'in komai ta fanjama....fanjam... b'at! Itama, sai ta b'ace.
KAMU SEDANG MEMBACA
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Misteri / ThrillerTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...