FAIROOZ
Babi Na Takwas.
"Rai da so!'' Fairoooz ta ji ya kira sunanta da haka, a dai dai lokacin data had’iye lomar farko na Abincin da ta d’ebo.
Binsa tayi da wani irin kallo, don ita yanzu kusan ma lamarinsa ya fara dai na ba ta tsoro sosai, sai dai mamaki!Ta riga ta gama tabbatarwa kanta cewa kawai da ALJANI take tare, Duniyar da ta zo kuma na ALJANU ne!
In ba haka ba ta ina mutumin da bata sani ba yasan sunanta! Har kuma yasan ana kiranta da rai da so? Sunan da k'awayenta na makaranta kad'ai suka santa dashi.
''Kin yi mamaki ko?” Ya jefe ta da wata sabuwar tambayar. Tun ba ta gama nazarin sunanta da ya kira a farko ba.
D’ago kai ta yi ta sake kallonsa. Wani sabon murmushinsa ya sake jifanta dashi.
Ba zato ba tsammani ita ma kawai sai ta tsinci kanta da mayar masa da martanin murmushin da yayi mata.
''Nasan kina mamaki ne akan sunanki dana kira, alhali kuma nace ki dai na mamaki a kaina, domin ni masoyinki ne, kinsan kuma ba’a tantama akan lamarin k’auna, saboda haka ki dai na mamakina!”.
''Ta ya zan cirewa zuciyata mamakinka, alhalin har yanzu bansan cikakken ko kai wanene ba!?Ban kuma san ta ya a ka yi, kai ka sanni farin sani har irin haka ba?”
"Kina mamaki ne?
Masoyi ai dole yasan masoyinsa farin sani kuwa. Tamkar yadda kema na san cewa k'arfin soyayyata ce, ta kaiki ga yin bincike a kaina, har gashi Allah yasa yau mun kai ga had’uwa!.''Maryam ta yi saurin d’ago kanta, suka sake had’a idanu, wannan karan a tare suka sakarwa junan murmushi.
Ita ma har ta d’auki d'abi'ar nashi, wato yawan murmushi, domin Fairooz ko wane lokaci fuskarsa na d’auke da k'ayataccen murmushi mai cike da nutsuwa.
Daga nan babu wanda ya k’ara magana cikinsu, inda suka maida hankali ga cin Abincinsu, har suka kammala.
Sun d’auki tsawon lokaci shiru, babu wanda ya k’ara cewa komai.
Shi Fairooz ya juyarda kansa ne gefe guda yana kallon wasu kyawawan tsuntsaye dake ta rera kuka cikin sauti mai dad’in sauraro, yayi shiru tamkar yana ji ko nazarin abin da suke cewa.
A gefe guda ita kuma Maryam kanta na k’asa tana tunanin ta yarda zata sake yi masa wata tambayar, don sallah take son yi.
Tana nan tana ta sak’e-sak’e, shi ko kamar bai ma san abin da take yi ba, saboda ya mai da hankali sosai ga kallon tsuntsayen da yake yi, can dai ta yanke hukunci yi masa magana, amma kuma sai ta rasa ta yadda za ta kira sunansa, ita dai haka nan kawai taji tana jin nauyinsa!.
Can tayi k’arfin hali cikin sanyin muryarta tace, “Yaa Fairoooz ina son inyi sallah don Allah!?''
Bai waigo ba, bare ta sami tabbacin cewa ya ji abin da ta fad'a ko bai ji ta ba.
Da ta ga yayi shiru bai ce komai ba, sai ta sake maimaita abin da ta fad’a, nan ma shiru. Ana nan dai a gidan jiya.
Haka nan kawai sai ta samu kanta da mik’ewa tsaye, gabanshi ta nufa daidai inda yake zaune.
Sai da ya rage saura kamar taku biyu tsakaninsu sai ta sake maimaita abinda ta fad’a d’azu, “Yaa Fairoooz nace ina son in d’anyi sallah pls!''. Har da had’awa da hannuwanta tayi alamar rok’o.
Nan ma shiru Fairooz bai tanka mata ba.
Wasu hawaye ne masu d’umi taji sun sauko mata akan k’uncinta, “To ko ya dai na magana ne kuma?” tace da kanta a fili.
![](https://img.wattpad.com/cover/120700986-288-k665469.jpg)
ESTÁS LEYENDO
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Misterio / SuspensoTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...