babi na biyu

921 68 13
                                    

FAIROOZ

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

Babi na biyu.

Maryam na nan tsaye tana sak'e-sak'e cikin zuciyarta, sai dabara ta fad'o mata!

D'ayan d'akin Babanta Malam Hafeez ta nufa da d'an k'aramin akwatin a hannunta.

Littattafansa ta d'auka, ta rink'a gwadawa, ko za ta sami wanda girmansa zai zo d'aya da akwatin hannunta.

Cikin ikon Allah ko ta sami wani littafi da ya shiga daidai, sai ta sanya marfin ta rufe. Ta koma da gudu d'akin da ainihin babban akwatin yake, ta sanya k'aramin aciki, sannan ta jawo b'ari da b'arin marfin akwatin daya bud'e dazu bayan ta danna madannin nan, ta had'a akwatin ya kulle.

Ta kalli littafin dake hannunta ta rungumesa a k'irjinta cike da jin dad'i.

Har ta juya da nufin barin d'akin sai wani tunani ya sake zuwar mata kuma, wasu k'ullin kaya taje ta d'auko masu datti da k'ura a jiki ta kakkab'a su akan akwatin, ya dawo kamar yadda yake a farko, "yauwa! Yanzu ko Baba ya dawo bazai gane na shigo wurin nan ba, bare yaje ga tunanin na bud'e akwatinsa!" Ta fad'a a fili.

Fitowa waje tayi gami da janyo k'ofar ta rufe.

Lambun gidan nasu ta nufa cikin jin dad'i gami da walwala.

Kujerarta da ta saba hutawa a kai ko da yaushe nan ta zauna.

CI GABAN LABARIN

K'urawa littafin idanu ta yi sosai.

'SHIN WANENE FAIROOZ?'

Tambayar da taiwa kanta kenan cikin zuciyarta. Wanda daman ta dad'e tana yiwa kanta wannan tambayar ba tare da ta tab'a tunani ko mafarkin samun amsarta ba!

Wani tattausan murmushi ta saki, kafin ta furta, "YAU ZAN SAN KO WANENE FAIROOOZ!"

Hannunta ta sanya ta bud'e littafin dake kan cinyarta....shafin farko1..... fuskar kyakkyawan saurayi fari mai k'warjini da cikar zati ta fara yin tozali dashi, yana zaune akan doki fuskarsa na fidda murmushi mai cike da annuri!

 fuskar kyakkyawan saurayi fari mai k'warjini da cikar zati ta fara yin tozali dashi, yana zaune akan doki fuskarsa na fidda murmushi mai cike da annuri!

Oups ! Cette image n'est pas conforme à nos directives de contenu. Afin de continuer la publication, veuillez la retirer ou mettre en ligne une autre image.

Maryam ta k'ara b'ude shafin dake gaba........sai ta sake ganin hoton saurayin a bakin wata k'orama ya d'aga hannu sama da alama wasa yake yi da wasu zanen tsuntsayen da ta gani saman hoton nasa.

Murmushi ta yi abin ya burgeta.

Sai ta k'ara bud'e shafin gaba shafi na uku......nan kuma kwance ta gansa cikin filawowi yana wasa da wata 'yar tsuntsuwa a hannunsa! Adaidai nan Maryam ta rufe littafin tana murmushi.

"Daman fuskar wannan kyakkyawan saurayin ne Baba ke b'oye min kullum! To me ya sanya?

Me yasa Baba yake b'oyemin littafin nan? Ashe ma ba komai bane a ciki."

Sai dai da ace Maryam ta san abin da take k'ok'arin tonowa kanta a dalilin wannan littafi da ta rik'e a hannunta, da ba ta yi marmarin d'aukosa daga inda Mahaifinta ya b'oye shi ba, bare har ta kai ga bud'ewa!

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Où les histoires vivent. Découvrez maintenant