SIRRIN BOYE......

447 42 10
                                    

                      FAIROOOZ

    Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar

            BABI NA SHA TAKWAS!.

Sabon lambun da aka sake yanzu yafi na farkon k’awatuwa da birgewa, cikin sabon da aka yi akwai wurin hutawa na musamman da aka ware a gefe guda, an cikasa kuma da fitilu masu fidda hasken launi iri daban-daban, akwai wata rumfa kuma da aka yi tana d’auke da babban teburi na cin abinci da kayan marmari nau'i daban-daban, sai kuma kujeru wad’an da suka zagaye babban teburin cin abincin da ke tsakiyar rumfar.

Daga can gefe guda kuma cikin lambun wani babban swimming pool (tafkin wanka).

Amma sai dai Alhaji Yusuf bai nunawa Fairoooz wannan sabon lambun ba.

Yanzu shekarun Fairoooz goma sha d’aya, amma har ya kai class 5 (aji biyar ) a *primary school* saboda early study da aka sanya shi, idan ka ganshi yana zubo karatu gwanin ban  sha’awa.
                                        
Wata rana Zeenat tana shirya Fairoooz domin tafiyarsa Makaranta, ya lura da ita ta nayi tana d’an daddafe kanta gefe guda, alamar tana jin ciwo a kai.

“Mami ba ki da lafiya ne?'' Ya tambayeta cikin raunatacciyar murya, damuwa kwance a fuskarshi.

“Haan mera beta'' (eh d’ana)

''Me ke damunki ne?''

"Kawai dai ina jin d’an ba dad’i ne, amma ba wani abu, kar ka damu kaji."

Ya fidda d’an yatsarsa guda, kamar yadda suka saba yi fa ita, ya nunata, tare da fad'in,

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Où les histoires vivent. Découvrez maintenant