FAIROOZ
Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar✍️
Babi Na Sha D'aya.
Tana zare mabud'in daga jikin akwatin, wani irin haske ya biyo bayan wurin da ta d'auke key d'in.
Inda za ta sanya key d'in ya fito sosai tana gani. Hakan ya sanya ta saita mabud'in daidai jikin ramin, sannan ta murd'a.
Ga mamakin Maryam wannan tangamemen ramin da take cikinsa, taga ya rikid'e ya koma wani babban fili wanda babu komai, sai face wani dank'areren gida guda d'aya tak! A tsakiyar cikin filin.
Daga inda take tsaye wani lallausar darduma ne mai d'auke da launin ja, shinfid'e tun daga inda take har zuwa bakin k'ofar wannan babban gidan dake tsakiyar filin da ta b'ullo.
Ba tare da tsoro ko jin wani shakku ba, Maryam ta yi Bismillah tare da d'ora k'afafuwanta a kan wannan jan darduman, domin ta san abin da ake nufin ta da ta aikata kenan.
A hankali ta rink'a takawa har zuwa k'ofar gidan, hannu ta kai ta murd'a k'ofar tana me karanto Addu'o'i a bakinta.
Tana sanya k'afafuwanta cikin gidan, lokaci guda ta ga ya rikid'e zuwa wani yalwataccen, k'ayataccen lambu mai matuk'ar kyau da girman gaske!.
Wani irin nishad'i ne ta ji ya ziyarci zuciyarta lokaci guda, domin Allah ya yi Maryam da tsananin k'aunar lambu a rayuwarta, shi ya sanya ma Mahaifinta ya samar mata da lambun shak'atawa cikin gidansu wanda ke tsakiyar Jeji, a wancan duniyar da ta baro.
Tsoron dake zuciyarta duka ta mata dashi, yayin da wasu kyawawan filawowi masu matuk'ar kyau da haske, suka d'aukai hankalinta.
![](https://img.wattpad.com/cover/120700986-288-k665469.jpg)
YOU ARE READING
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Mystery / ThrillerTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...