AL-HINI

421 40 7
                                    

FAIROOZ

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

    Hafeez sai da ya yi kwana hud'u a gadon Asibiti, saboda tsananin jimamin jarabawar da ta gitto masa, bai tab'a tunanin Zeenat na da ciki ba, bai tab'a mafarkin za su sami ciki a wannan lokacin ba, sai gashi kuma Allah'n da ya basu ya karb'i abinsa.

Illahirin gidan gaba d'aya sun yi bak'in ciki da faruwar wannan al'amarin, ba kamar Hafeez wanda kullum cikin kukan zuci yake, da farko kamar ba zai bar damuwa ba, ganin cewa abinda yake nema kenan ku san shekaru goma sha hud’u, sannan Allah ya bashi wannan arzikin ba tare da ya sani ba kuma ya karb’i abinsa.

Allah kenan bayan da baya hukunta al’amarinsa.

Daga k’arshe dai haka nan ya hak’ura ya fawwala ma Allah dukkan lamarinsa,  da taimakon nasihar da Mahaifinsu ke yi masa tare da d’an uwansa Abbas.

Sai ya duk’ufa rok’on Allah, akan yadda ya bashi wannan kyauta kuma ya karb’a, da ya sake bashi arzikin wani d’an ko ‘ya masu albarka.

Bayan sati uku lokacin an sallamo Daweeshat tare da Zeenat daga Asibiti, Daweeshat ta warke garau inka ganta ma ba za ka d’auka itace kwanakin baya take kwance ba ta san inda kanta yake ba.

B'angaren Zeenat ita ma ta warware kamar ba ita ce ta yi b'ari ba, domin har ta ci gaba da sauran harkokinta, amma an hanata yin ayyukan da ta ke yi masu yawa kamar da, don gudun kar ta sake samun wani cikin ba’a sani ba a k’ara asararshi.

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Where stories live. Discover now