FAIROOOZ
Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar
BABI NA ASHIRIN DA D'AYA
Dr. Sa'eed sun d'auki lokaci me tsawo kafin suka fito daga office d'insa, jikin Dr. Abbas ya yi sanyi sosai, kallo d'aya za ka yiwa fuskarsa ka fahimci tsantsar damuwar dake bayyane a jikinta.
Dr. Sa'eed ne ya nufi inda suke zaune, shiko Dr. Abbas tunda ya kalli fuskar d'an uwasa sau d'aya suka had'a idanu sai ya sunkuyar da kanshi, bai k'ara kallonshi ba kuma be k'arasa inda suke ba, yana tunanin ta yadda yayanshi zai ji, ko ya karb'i abinda ya faru.
Tun kafin Dr. Sa'eed ya isa wurin da suke, Hafeez ya mik'e tsaye yana tambayarsa.
"Ya ake ciki Dr, me ya sameta ne, tana dai lafiya ko?"
Domin daga alamar da ya gani a fuskar d'anuwansa ya san wani abu ya faru.
"Kwantar da hankalinka Hafeez Matarka tana nan lafiya." cewar Dr sa'eed.
"To amma Dr. Me ya sanyata zuban jini ne? Shin Jinin ya tsaya yanzu?"
"Karka damu ya tsaya, zan ba ka amsar tambayarka na abinda ya sameta, amma so nake sai ka kwantar da hankalinka tukun don Allah, kasa nutsuwa da tawakkali wajen fahimtar abinda zan fad'ama kaji."
Hafeez yace "In shaa Allah, amma duk menene ya kawo wannan maganar?"
"Na san ka yarda da cewa Allah shine me yin duk yadda yaso, a kuma kowane irin lokaci, shi ke bayar da kyauta ga duk wanda yaso, lokaci guda kuma idan yaso sai ya karb'i abinsa..."
"Dakata Malam." Hafeez ya fad'a lokaci guda tare da cakumar rigar Dr. Sa'eed.
VOUS LISEZ
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO
Mystère / ThrillerTana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce mu...