BABI NA SHA UKU

439 40 22
                                    

                   FAIROOOZ

  Daga Alk'alamin Ashnur pyar

           BABI NA SHA UKU

Ko da Maryam ta bud’e littafin, kamar dai wancan lokacin da ta fara bud'e sa ne……Yau ma shafin farko…fuskar kyakkyawan saurayi nan fari mai k’warjini da cikar zati ta gani, zaune akan doki.

Rik’e yake da takobi, fuskarsa tana fidda murmushi mai cike da annuri.

Maryam ta k’ara bud’e wani shafin na gaba…….. sai ta sake gani hoton saurayin a bakin wata k’orama ya d’aga hannunsa, yana wasa da wasu zanen tsuntsaye da ta gani a saman hotonsa.

Haka Maryam ta ci gaba da bud’e shafukan littafin nan, tana ganin wad’an nan hotunan da ta riga ta gansu tun a kwanankin baya, tun daga kan k’oramar nan…zuwa wasu kyawawan tsuntsaye guda uku…har zuwa shafin da hoton jarumin nan yake a duk’e jini na zuba daga goshinsa….ras! gaban Maryam ya sake fad’uwa kamar wancan lokacin.

A hankali ta kai hannunta wajen bud'e shafin dake gaba, wanda shine daidai shafin da ya zuk’eta a wancan lokacin.

Maryam na tsammani kamar wancan lokacin zata ji littafin ya sake zuk’eta, amma sai ta ji shiru hakan bai faru ba, shiru-shiru ta dakata wai kowani abu zai faru, amma bata ga komai ya faru ba.

Cikin fargaba da sanyin jiki ta yanke shawarar bud’e shafin dake gaba da wannan.

Runtse idanuwanta ta yi, ba tare da ta bud'esu ba, hannunta na kakkarwa, saboda tsoron abin da zai iya faruwa, ta bud’o shafin dake gaban wanda ya zuk'eta.

FAIROOZ LITTAFI NA FARKO Where stories live. Discover now